Total Pageviews

Tuesday, June 7, 2011

Sharhi Na 7. Talaucin Arewa, Dalilansa da Maganinsa

SHARHI NA 7
LALACEWAR AREWA (2)

TALAUCI, DALILINSA DA MAGANINSA

Dan Arewa yau ya zama abun tsana, wariya da tsangwama a Najeriya ba don komai ba sai don ya fi kowa talauci. In ka musa, lura da abu daya. Ka taba ganin mai kudin da ba a haba haba da shi? Da zarar ka yi kudi, a ko’ina a duniya, mutane ba za su damu da asalinka ko halinka ba. Nan da nan zaka zama abokin shawarar sarki, malamai za su rika jawo nassi suna gaskata maganarka ko karya ce ka shara. Sai kaji sun ce, “Aiko mun gani a hadisi,” in Dan Ibro a wakarsa ta Bayanin Naira. Jama’an gari kuwa kowa na matsowa kusa da kai don ya samu abun lasa. In ka nemi ‘ya za a baka. In ka bada shawara za a dauka. In ka yi fada za a ji. Kudi ke nan. Mai Maqamatul Hariri kam da ya gama yiwa kudi kirari, sai ya rufe da cewa “ba don tsoron Allah ba, da na ce kudi sun fi komai iko.”

To in ‘yan Arewa na son dawo da martabarsu, bayan baiwa ilmi muhimmanci da aiki da shi, abu mafi na biyu shi ne su bi ilmin nan ya nuna musu hanyar samun arzikin duniya. Da razar arzikinsu ya bunkasa, to sauran hakkokinsu na siyasa da zamantakewa za su biyo baya cikin ruwan sanyi. In ko suka ci gaba da gudun duniya, to wallahi, ba hakkin da za su samu sai bauta a Najeriya da duniya baki daya. Da talaucin za a yi amfani a hana musu komai kamar yadda muka gani a zaben da ya gabata. Mutane suka rika karbar naira hamsin ko indomi suna jefa kuri’arsu inda ba nan suka so ba.

Amma kafin a san hanyar korar talauci ya kamata a san ta ina ya lallabo ya shige mu don mu toshe wannan hanya komai wuyarta. Akwai dalilai da yawan gaske wanda masu ilmin tattalin arziki suka zana. Na sha tattaunasu a rubutu na na turanci. Amma zan ambace su a takaice a nan. Nan gaba zan zabi wasu daga cikinsu in yi cikakken bayani akan kowannensu.

1. Rashin Gaskiya.

Ba abun da ya jawo mana talauci irin rashin gaskiya. Dukiya ba ta habaka sai an rike ta da gaskiya kamar yadda za a yi kokarin rike kwai a kwando. In aka sa rashin gaskiya, walau ta hanyar sace ta, ko hadata da haramiya irin su algus, da tauye awo, da cin hanci, da sauransu, to dole dukiyar ta tawaya. Wadannan abubuwan kuwa sun zame mana ruwan dare a nan Arewa. Masu sai da nama, masu awo, masu sai da mai, kowa aikinsa ke nan, ya sai da jabu, ko ya rage awo.

In da gaskiya da himma, Allah shi zai sa albarka a kasuwancin. Duk maikudi na son kudinsa su habaka. In da da gaskiya, da masu kudi sun rika baiwa ‘yan Arewa jari. Su kuma su sarrafa shi akan gaskiya da amana, da ilmi da himma. Zasu yi kokarin habaka dukiyar don su ma su amfana. Kafin shekara, naira miliyan daya sai ya dawo miliyan biyu ko fiye. Da haka dukiyar Arewa za ta yi ta habaka. Kafin a ce karni guda, wannan sashe na Najeriya ya mallaki tattalin arzikinsa. Rayuwa ta inganta, talauci ya tattara komatsansa ya bar gari.


Mu duba daga Inyamurai da Yarbawa. In sun aje yaro a shago da wuya zai saci dukiyarsu. Daga nan shagunansu suke karuwa har shima yaron a sallame shi ya bude nasa kasuwancin. An ci Inyamurai da yaki, aka bar masu arzikinsu da naira ashirin kacal, amma yau ta hanyar himma da gaskiya tsakaninsu, sun fi kowa a Najeriya dukiyar kasuwanci. Ga yahudawa nan. Basa cutar junansu. Ta hanyar hada kai da gaskiya tsakaninsu, yau ba wanda ya fi su arziki da fada aji a duniya. Da mu inyamurai suke misali da mu wajen rike amana. Amma yau sai tofin Allah tsine. Ko shiga motar hayarmu ba su son yi.

In munki gaskiya, ko anyi shekara dubu ana karbo kudi daga Abuja, ko ‘yan kasuwanmu na zuba jari, ba abun da zai karemu da shi sai tsiya, kamar an shuka dusa. Abu na farko ke nan.

2. Lalaci

Malam bahaushe ya yi kaurin suna wajen lalaci na tunani da aiki. A karshe sai ya jinginawa Allah sakamakon lalacinsa ya ce, “Allah ne ya sa haka. Kaddara! Duniya dama ba wajen jin dadin mumini ba ne.” Gudun duniya a gunsa shi ne tsoron Allah. Yana da saurin aminta da kalilan. Don haka in ya samu kadan sai ya rage himma.

Irin wannan tunani da ya shigi musulmi a duniya duka dole a koreshi. Allah ya kawo mu duniya ne don mu rayu a cikinta. Rayuwa kuwa tushenta tattalin arziki ne, don inda baki ya karkata, nan yawu yake zuba. In bamu tashi muka baiwa duniya hakkinta ba, to muna da bauta a gabanmu. Dole burin kowannenmu ya zame kyautata halin rayuwarsa ta duniya ta hanyar da zai tsira da mutuncinsa da na addininsa, wanda haka ba zai samu ba sai ya fita daga kangin talauci.

Bayan haka, dole mu lura cewa muna zaune a duniya tare da sauran al’ummomi. In su suna da himma, mu bamu da ita, to arzikin kasa zai koma wajen masu himma ne. Mu kuwa a barmu da allazi wahidun, kamar yadda muke yi yau.

A yau abunda yake faruwa kenan a Najeriya. Gamu nan da yara facaca marasa aikin yi don kawai ba su so su sha wuya. Iyayensu sun kawo su duniya suna ta bauta musu. Sun ki sa su harkar noma, ko kira, ko dukanci da sauran sana’o’i. Ga ruwan sama Allah na saukarwa duk shekara, ga filaye bila adadin, amma sun taru a birni ba su da niyyar kaura zuwa inda za su amfani kansu, sai dai iyayensu su ciyar da su. Masu zuwa gonar ma in hantsi ya yi sai su dawo gida. Balle a ce kaka ta shigo. Kadan ne suke noman rani. An barwa ‘yan lambu. Sauran jama’ar gari kuwa sai zaman banza duk tsawon rani, alhali ga koguna da dam dam masu yawa da Allah ya albarkaci Arewa da su.

Hakanan manyan ma. Kowa ya tare a kwangila da cin kudin jama’a a cikin gwamnati. An ki a bi hanya mai wuya irin noma da kiwo tunda ga kudin banza nan na fetur. Kalilan ne suke kafa masana’antu su tsaya da kansu, su hakura da kadan din da ake samu, don sauran mutane su amfana da aikin yi, ko har abun ya bunkasa.

A karshe karatun boko ya zo ya kara lalata zuciyar yaranmu. A wurinsu, aikin ofis shi ne aiki, ko a kamfani ko a gwamnati. Shi suke jira. Shi ma sai mai maiko. In ya zo, su yi. In bai zo ba, suna nan zaune suna kirga kansu cikin marasa aikin yi, iyayensu na ci da su, suna musu aure da sauran shagwaba.

Ina ga lokaci ya yi da za a nunawa mutane ba hakkin gwamnati ba ne samar wa kowa aikin yi. Aikinta ta wanzar da yanayin neman arziki. Daga nan kowa sai ya tashi tsaye, tashi ta fissheshi. Dalilin da ya sa ke nan in ‘yan siyasa sun yi alkawarin samarwa dukkan yara aikin yi suke gagara. Ba za su iya ba, don ba huruminsu ba ne.

Don haka iyaye su daina sagarta ‘ya’yansu. Yara kuwa su san cewa duniya ba ta rago ba ce. Duk wanda ya zota, dole ya tashi tsaye. Malamai kuwa su daina kashe zuciyar mutane da wani tauhidi da bashi da amfani komai asalinsa. Nan duniya muke. Ita muka sani. Ita ke da tasiri a rayuwarmu. Ta hanyarta za mu iya yin addinin cikin martaba da kamala. Wanda ke son lahira kawai, to ya jira ya mutu, ya daina kukan talauci. Gwamnati kuwa ta rika gayawa mutane gaskiya. In za ta taimaka, ta taimakawa wadanda suka tashi tsaye, ba zauna gari banza ba.

Arewa mu kori lalaci. In ba haka ba bauta yanzu muka farata a Najeriya.


3. Danniyar Gwamnatin

Akwai alamu masu yawa da ke nuna cewa gwamnatin tarayya, wacce ita ke da hakkin tsara tattalin arzikin kasa da manufofinsa, bata baiwa abubuwan da tattalin arzikin Arewa ya kafu a kansu muhimmanci ba. In ka duba kasafin kudin kowane shekara, za ka iske harkar noma ba a kulata ba ko kadan. Noman nan kuwa da shi akasarin gidaje a Arewa suka dogara kuma ta hanyarsa ake ciyar da Najeriya. Alal misali, akwai shekarar da Obasanjo ya warewa harkar noma naira biliyan goma rak, a lokacin da ya kashe sama da naira biliyan saba’in wajen gina dandalin wasanni na kasa a Abuja. Wannan zalunci ne da ‘yan Arewa yakamata su yaka, kwansu da kwarkwarsu. To amma anbarmu masu sharhi kawai da korafi a jarida.

In an ware isassun kudi don aikin noma, ta nan za a samu a yi wa manoma rangwamen kanyan aiki (subsidy) irin su tarakta, da iri, da taki, da sauransu. Manoma za su samu wadannan abubuwa cikin sauki ta yadda nomansu zai zo da riba mai yawa don su kuma yinsa badi. Rashin yin haka, da rashin tsari na adalci wajen rabon duk wani abu da gwamnati za ta bayar, shi ya sa manyan manoma da kamfanoni suka yi watsi da noman, ganin asarar da suke tafkawa duk shekara. A karshe, an bar noman hannun masu karamin karfi wadanda bai wuce su noma bukatunsu na gida ba kawai.

Bayan rashin isasshen rangwame, gwamnatin tarayya ta zalunci Arewa sossai wajen sa dokokin da ke dakushe noman kansa. Ga mari ga tsinka jaka! Alal misali, ba abunda ya fi kasuwa habaka noma. In manomi zai sai da kayan gonarsa da daraja, shi ke nan, badi ma zai noma fiye da haka. To amma kasuwan hatsi, wanda shi ne akasarin abun da muke nomawa, sai gwamnati ta sa masa takunkumi, ta haramta fitar da shi kasashen waje. Don haka, masara da gero da shinkafa kullum sai an sai da su a farashin da bai kai abunda aka kashe wajen nomasu ba. In kaga an fitar da su sai ta hanyar sumogal. Kullum sai sun yi kwantai a Najeriya. Alhali kuwa kudu am basu dama su fitar da kayan masana’antunsu yadda suke so, su sayar a farashin da suke so. Wannan magudi ne. Da sakel!

A gaskiya wannan zalunci ne wanda aka assasa shi bisa tsohon karatu dake tsammanin in an bada dama a fitar da abinci, wai za a yi yunwa. Ba yunwar da za a yi tunda dai haka zai jawo noman ya bunkasa sossai. Wannan shi ne matakin da Afrika ta kudu ta dauka. Ban ga dalilin da za a maida ‘yan Arewa bayi ba suyi ta noma ba riba don kawai wadanda ba sa noma su wadata da abinci. Sannan kuma, sai a dawo ana zagin Arewar cewa ta cika talauci, da mabarata, da almajirai, da sauran bakaken maganganu.

To ba za ta sabu ba. Dole ‘yan Arewa su tashi su tabbatar da an canza wannan dokar. Da zarar an bamu dama mu fitar da abinci, to zamu noma da yawa yadda zai wadaci gida kuma mu sayarwa makwabta. Wannan zai kawo mana aikin yi mai yawa ya kuma habaka arzikinmu. Talakawa ba za su tawaya ba sai dai su kara arziki. Tunda manoma ne, za su noma abunda zai ishe su ci su sai da sauran a farashi mai tsoka. Su kuwa wadanda ba sa noma – mai’aikata, ‘yan kasuwa da ‘yan kudu, sai su tanadi kudin saye. Kan mage yaw aye. Ba zai yiwu abar fiye da kashi saba’in bisa dari na al’umma cikin bauta ba, saura kuwa suna holewa.

Abunda kawai za a yi sai a bada sanarwar shekarar da dokar zata fara aiki. Kowa sai ya shirya wannan daminar. Wanda ya yi lalaci, to yunwar da ta sameshi shi ya so.

Dokar hana fitar da hatsi a Najeriya dole a soke ta. In ba haka ba, za mu ci gaba da bautawa wasu ne kawai a Najeriya, muna sauwake musu rayuwa, su kuma suna mana kallon matalauta.

Yan majalisunmu na Arewa da duk mai son ci gaban tattalin arzikin ‘yan Najeriya, kalubalenku. Za mu nemi ku yi amfani da yawanku a majalisa wajen tabbatar da wannan burin.Jama’a za mu dakata a nan. Za mu ci gaba da sharhi kan harkar noma da sauran abubuwan da gwamnati ke yi wajen haddasa talauci a Arewa. Allah ya taimaka.

7 June 2011

8 comments:

habiba said...

MashaAllah gaskiya ne duka. . . .ka kawo dalilai uku na talauci a arewa,ina fata har za ka iso kan rashin ilimi wanda a gani na ya fi komai sanadin tsiya.
A gani na,hatta ilmin addini dan arewa bai fahinta ba,shi ya sa ya ke zaton ba dole ba ne ya iya rubutu da karatu,bayan farkon wahayi ma shi ne 'kayi karatu'.Shi ya sa za a zage shi,a cuce shi,a kaskantar da shi a Nijiriya bai ma sani ba.Bayan haka,bai gane cewa ilimi a wannan zamani shi ma makami ne ba.
Ga kuma mugayen manya,wanda kansu kawai su ka sani. . . .ya kamata ma mu canza manya,na yanzu ba su yi ba!

Alkasim said...

allah Ya saka da alkhairi Ya kuma kara mana irinku a arewachin nigeria.

Anonymous said...

allah Ya saka da alkhairi Ya kuma kara mana irinku a arewachin nigeria.

Habib said...

Mu tashi mu farka yan AREWA ...

Isa Yunusa Chedi said...

Dr. Tilde, da kai da Malam Sanusi lamido Sanusi, da Sam Nda Izaya, da Rev. Mathew Hassan Kuka da wasu wadanda ban ambataba hakika kyautar ubangijice ga Arewa. Allah yaci gaba da baku hattara da hikima wajen taimakonmu yan Arewa, malalata.
Hakika abubuwan da ka ambata su ne dalilin samun kanmu cikin wannan hali mawuyaci, wadanda da yawa sun dauka Allah ne ya kaddara mana haka.
Sau dayawa nakanyi muhawara da abokai akan wadannan matsaloli wanda har wasu su kan kalleni da wata manufa ta kafirta. To a gaskiya Dr. a fahimtata, samun damar kawar da talauci daga arewa ya ta'allakane musanman ta waje daya. Da zarar kaci nasara a wannan matsala to sauran matsalolin za ka nemesu karasa da yardar ubangiji. Wannan matsala kuwa itace kyakkyawar fahimtar manar KADDARA.
Kamar yadda muka sani akwai kaddara a musulunci. Hasalima idan baka yarda da itaba nassi yanuna cewa ka kafirta domin kuwa tana cikin shikashikan musulunci. To amma rashin fahimtar ma'anarta shi yasa muke da yawan Yan maula da kuma yawan karayar arzuki. Hasalima dai bincike ya nuna cewa Bahaushe shi yafi kowa yawan karayar arzuki a Nigeria. Hakika ban yi mamaki akan hakaba domin kuwa annunawa Malam bahaushe cewa komai ya sameshi haka Allah ya so. Kuma zafin nema baya kawo samu. Kuma wai 'ALLAH YA FI SON TALAKA'


Malamai da dama sun taimaka wajen mummunar fahimtar abin da ake nufi da kaddara a rayuwa ta hanyar baudaddiyar fassarar kalmar. Kuma sun dakwafar da kwa-kwalwarmu wajen fadada nazari akanta.
Koda yake matsalar fahimtar maanar kaddara ta dade tare da alummar musulmai da karni masu yawa. Kuma malamai da dama sunyi mahawara akanta kamarsu marigayi ustaz jaafar Adam, Sanusi L. Sanusi, da sauransu. Kuma mafi yawansu sun nuna kwarai akwai matsala tare da fahimtar kalmar.

Saboda haka naso Dr. kayi cikakken bayani tara da kawo ayoyin AlQur'an da hadisai, da kuma kafa hujja da tarihi akan duk wani abu da ya shafi wannan matsala, kamar yadda ka saba. Domin kamar yadda na fada a farko wannan itace tushen wahalar da muka sami kanmu aciki a yau. Sannan kuma kubuta daga ita ya ta'allakane a kan yarda mu ka fahimceta. ALLAH ya taimaka mana mu fita daga wannan hali.

Mohammed said...

Assalamu Alaikum, wato duk ababen da na karanta cikin kasidar taka na samu gamsuwa kwarai da gaske. Mutanen mu gaskiya ana bukata a koyi hankali, juriya daga irin halin da mutum ya ke ciki, a nemi ilmi na addini ko na boko. Rashin sannin yakamata, mutun ya rika fadanci kafin ya sami biyan bukata wurin dan'uwansa namiji ko ma dai ince musulmi,ai bai dace ba. In har za a taimaka ma mutun bai kamata ace an wahalar dashi ba, ko kuma a sa ya bi wata hanya ta sabawa wa Allah (SWT), saboda rashin mutunci, Allah ya kawo mana sauki, ameen.

Sani Mudi said...

Dr naji dadin wannan sharhi mai ma'ana. abu daya da naga baka tabo ba shi ba shine irin mummunar rawar da shugabannin arewa na siyasa, wato gwamnoni da yan majalisu da ire irensu suke takawa wajen tauye yankin. Hakika abin daka fadi akan manufofin gwamnatin tarayya daidai ne amma suma gwamnatocin arewa, a ganina sun fi laifi don suke da hakki mafi nauyi don raya arewa. Abin takaici shine yadda su wayannan gwamnatoci, duk da koma bayan yankin arewa din sai gashi wajen rashawa, cin hanci da sata ai sai su dauki lambar zinari da azurfa da tagulla duk su bar yan kudu. Ina fata zzamu dubi wannan anan gaba. Jazakallah.

Anonymous said...

Dr ka yi kokari wajen kasidarka amma ni ina da raayi mababbanci da kai a bisa dogaro da noma a matsayin abin da zai kaimu gaci ba tare da kawo wasu alkaluma ba. Hasali ya kamat ka fahimci cewa yawancin manomanmu na neman abinci ne kawai domin gonakan ba masu girma bane da za su samarda wadataccen abinci har a sami rarar da za'a sayar a yi maganin talauci. Ga canjin yanayi ga dogaro da noman damina wanda ba kasafai ya kan samar da kudi ba.
Zargin Shugabaninmu da rashin kokari ina ganin zafafa rashin adalci ne garesu domin suna bakin kokarinsu. Kin daraja manya da tsageranci da wulakantasu ba zai zawo mana wani cigaba sai koma baya. Lallai masu ilmi da jamioinmu da kwalejojin fusaha su tashi tsaye wajen samar da ilmi da nazari da bincike wanda za su ciyar da mu gaba. kada fa farfagandar turawa da abokanan zamanmu su ingiza mu zuwa asara mabuwayiya. Ku da Allah Ya ba ku fahimta ku yi amfani da basirarku wajen karfafa hadin kanmu domin gujewa hasara. Idan ana yaki da wasu ba a kuma kaddamar da yakin basasa domin abokin gabarka ma waje zai hada ku ne ya taushe. Allah Ya sa mu gane!

Isa A