Total Pageviews

Thursday, April 28, 2011

SAKO 1. KWANKWASO YA KAFA TARIHI A KANO

Aliyu U. Tilde 12:52am Apr 28
Kwankwaso Ya Kafa Tarihi a Kano.

Bana jin a Kano an taba sarkin da ya je ya dawo. In Shekarau ya karya al'adar single tenure, to Kwankwaso, wanda ban sani ba, ban taba gani ba, ya karya al'adar rashin dawowar sarakuna a kasar Hausa.

Ina tuna abinda kakanmu Sarkin Kano Sanusi (Rahimahullah) ya gayawa Abubakar Rimi (Rahimahullah) lokacin da tsohon gwamnan ya sauka a 1983 zai sake takara a wata jam'iyya. Da ya samu tsohon sarkin a Wudil, ya ce mar ga niyyarsa, sai Sanusi ya ce mar, "Kash, dana, ka yi kuskure. Ai ba a barin mulki a dawo." Sadaqata. Dawowar da Rimi bai yi ba ke nan.

Dawowar Kwankwaso ya fito da amfanin hazaka, da rashin karaya da naci a fili. Nasarar da ya samu ya bauta mata, in za a fadi gaskiya. A 2002/2003 in na tuna jifansa ake, har a lokacin ina kiran haka "Kano intifada" a column dina. Amma abubuwa da yawa sun taimaka masa musamman mukaminsa na minista, da kusancinsa da mutanen jamiyyarsa da daukan nauyinsu, da rashin barinta ya koma wata.

Nasararsa abar yabawa ce, kamar ta Shekarau ce a 2007. Haka kuma darasi ne ga 'yan siyasa musamman 'yan jam'iyyar CPC da suke tsammani za su fake a bayan Buhari su ci nasara. Hakan na iya yiyuwa a jihohin kauye, amma ba a Dala Babbar Hausa ba. Yaro ko da me ka zo an fi ka!

Ina taya Kanawa murnar samun sabon gwamna. Allah ya taya mar da basira, da tausayin talakawansa, da aiki tukuru, ya raba shi da halin tsiya na bita da kulli da zalunci da ramuwar gayya. Allah ja zamaninsa in yai haka. Ku ko talakawansa, Allah ya baku ikon hakuri da shi, da taimaka masa, da kyautata masa zato.

Samun mulki don ai mulki
Manufa jan mulkin bis sidki
Ji amarya kan bata hau doki
Ba, Ba Za a aza mata kaya ba.
....
Ai samu yafi iyawa, shi
Kwado bai mallaki ko dukushi
A ruwa aka san shi makomarshi
Nan ne zai sami abincinshi
Ya yi wasanni da nishadinshi
(Abubakar Ladan)

Don Allah a mika nasiharmu zuwa gareshi.

Shi ko Shekarau, Allah ba shi ladan aikinsa nagari, ya yafemar kurakuransa, ya sauwake masa hisabi gobe kiyama. Kuma talakawansa, yana da kyau ku yafe mar, ku san cewa mulki a kasa cike da talauci da mutane masu son zuciya ba sauki ba ne. Sai mutum yana gwamnati zai san haka. A waje muna waliyi, a ciki muna gafiya, sai wanda Allah ya so.

Haza wasalam

Aliyu

20 comments:

Salisu said...

Allah shi saka ma da alkhairi for your matured insight. Indeed, your choice of Hausa as the language for this article is far from been out of place. Infact, it is execellently done.

Salisu said...

Allah ubangiji ya saka da alkhairi. Indeed, your choice of Hausa as a language for this important article is far from been out of place, infact, it timely.

GIM said...

MashaAllah, Dr. Tilde. Allah Ya saka da alkhairi, Ya kara maka basirah. Allah Ya anfane mu da wannan aiki naka, Amin. Maassalam.

Dr. Garba Malumfashi

Alfa Ibrahim said...

Kar Allah SWT Ya jarabce mu kuma da irin fitinar da ta addabi mutanen kano a lokacin mulkin sa na baya. Allah Ya kare wannan al'umma tamu daga sharrin rayukan ta da kuma munanan aiyukan ta.

Nasiru Yusuf Ibrahim said...

AlhamduliLah! Sabon Gwamna Sabon S......

Nasiru Yusuf Ibrahim said...

AlhamduliLah! Sabon Gwamna Sabon S.....

photo said...

Na yi murna da ganin rubutun nan a harshen mu

Yusuf M. Adamu said...

Malam wannan rubutu na ka ya yi. Na ji dadin ganin yadda ka bayyana cewa Kwankwaso ya yi aiki don samun nasararsa da kuma dalilan nasarar. Muna fatan kuma Allah ya yi masa jagora. Ya kamata Kanawa su karbi wannan hukunci na Allah su kuma yi ta addu'a kada Allah ya bar Kwankwaso da wayonsa amma ya yi masa jagora don yi musu jagaba.
Dr Yusuf M Adamu

muhalisu said...

Hakikanin gaskiya wannan sabon alamari ne a jihar mu ta Kano; Jalla Babbar Hausa, yaro ko damai kazo anfika! Saidai fatan alhairi a gareshi, da kuma daukan darasi gamai da abun da yafaru shekaru da dama sanda yake gwamna wancan karin; idan yayi da kyau(muna mai fatan haka) tau, zai ga da kyau a rayuwar sa ta duniya da lahira; sabi da jamaar Kano, jamaar arewacin Nigeria, dama kasar gabaki daya na fama da talauci matuka, an kuma kasa samun zakaru a duk shuwagabanin mu tun bayan rashin magabata su Sardauna, Tafawa Balewa, Muhammad Ribadu, Abubakar imam, Mallam Aminu Kano da dai suranan su (Allah ubangiji yayi musu rahama).

muhalisu said...

Hakikanin gaskiya wannan sabon alamari ne a jihar mu ta Kano; Jalla Babbar Hausa, yaro ko damai kazo anfika! Saidai fatan alhairi a gareshi, da kuma daukan darasi gamai da abun da yafaru shekaru da dama sanda yake gwamna wancan karin; idan yayi da kyau(muna mai fatan haka) tau, zai ga da kyau a rayuwar sa ta duniya da lahira; sabi da jamaar Kano, jamaar arewacin Nigeria, dama kasar gabaki daya na fama da talauci matuka, an kuma kasa samun zakaru a duk shuwagabanin mu tun bayan rashin magabata su Sardauna, Tafawa Balewa, Muhammad Ribadu, Abubakar imam, Mallam Aminu Kano da dai suranan su (Allah ubangiji yayi musu rahama).

Dr. Aliyu said...

Dr. Allah ya biya ka. Wannan babbar aya ce gare mu. Ba zaben kano ba kadai har zaben Nigeria gaba daya, kadai dai masu hankali ke ganin ayar.
Game da na kano wata kila ayar tafi fitowa fili domin kowa yasan kwankwaso ba shiri yabar gidan gwamnati, M. kuma yazo har akace bazai shiga gidan gwamnati ba saboda tsoron Allah. To yanzu ya girma har yana ganin abinda yace shi za`a yi. Ba farkon ba karshen shine magana. Allah yai mana afuwa. Dr. Rabiu Musa congratulations, kaninka kaunarka da kanawa, kayafewa duk wani dan kano, shugaba ne kai da ke da experience a jagoranci, kuma ina zaton bugawa da irinsu Jonathan dan kwato hakki bana rago ba ne, sai dai shugabanni irinka. Allah yai maka Jagora. Aliyu Dahir (Phd Candidate, IIUM)

Aliyu Dahir said...

Dr. Allah yabiyaka,

Dr. Rabiu Musa congratulations. Ka yafewa kanawa, ka samawa yan tawagarka da ba naka ba aiki, ka yunkura dan kwato hakkin kanawa a kasa domin bugawa da Jonathan sai mazaje irinku dan ba na rago bane.
Aliyu Dahir (PhD Candidate, IIUM)

Aliyu Dahir said...

Dr. Allah yabiyaka,

Dr. Rabiu Musa congratulations. Ka yafewa kanawa, ka samawa yan tawagarka da ba naka ba aiki, ka yunkura dan kwato hakkin kanawa a kasa domin bugawa da Jonathan sai mazaje irinku dan ba na rago bane.
Aliyu Dahir (PhD Candidate, IIUM)

Dr. Aliyu said...

Dr. Allah yabiyaka,

Dr. Rabiu Musa congratulations. Ka yafewa kanawa, ka samawa yan tawagarka da ba naka ba aiki, ka yunkura dan kwato hakkin kanawa a kasa domin bugawa da Jonathan sai mazaje irinku dan ba na rago bane.
Aliyu Dahir (PhD Candidate, IIUM)

Dr. Ameenuddeen A. said...

Tafiyar Kwankwaso ikon Allah dawowarsa ma ikon Allah ga masu tunani. A yanzu a na bukatar aiki fiye da magana,musamman gwamnati ta sa gaba a noman rani da kiwo,da ilimi,da kasuwanci da masanaantu da bin doka da oda ,a maimakon a ce mutane sa gyara da hankular su.Dr. Ameenuddeen.

Haroun said...

Bada niyyar arziki yazo ba, adai bari ya zauna tukun.

Maliki K. Umar said...

Ameen!Ameen! Ameen! Allah Ya amsa adduar da ka yi.

Ina kyautata zaton Rabiu Musa Kwankwaso ya koyi babban darasin jagorar alumar Kano: ya yi mulki, ya rasa mulki ya kuma samun damar ya mulki jama'ar Kano da izinin Allah Madaukakin Sarki.

Ina kuma kyautata zaton batun "bita-da-kulli" bai taso ba. Amma duk wata barna da ta bayyana, ta cin amanar dukiyar al-umma, lallai a bi sawun ta da nufin kwato wa al-umma hakkin su.

Duk abin kirkin da gwamnatin Shekarau ta yi, ya kamata a inganta shi. Wanda ta yi kuskure, ko sakachi a yi watsi dashi.

Allah Ya taimaki Kano da Nigeria, Ya inganta rayuwar mu.

U.M Tukur said...

Dr Tilde Allah Saka maka da alkhairi wannan ijtihadi da kakeyi.Ya karawa rayuwarka albarka Ya Aljannah ce makomarka.Shi kuma Kwankwaso Allah Sa wannan ya zama darasi gareshi cewar bamai bada ko karbe mulki sai Allah.

Dr Ahmadu Dahiru said...

Dr Aliyyu Tilde kace Shekarau yayi hazakar da ya kamata a yaba masa a 2007 saboda samun nasarar da yayi na sake zaben sa a matsayin gwamna karo na biyu. Ga haske: Ina rantsuwa da Allah Makadaici, Mabuwayi, Marinjayi cewar najejje garin mu Rogo a jihar Kano domin yin zabukan da akayi a wannan lokacin amma kawo ya zuwa yanzu ban ga akwatin wannan zaben da aka ce wai anyi a jihar Kano ba. Kuma ina fada ma cewar sakamakon da aka bayar na Rogo LGA shine wai Mallam Ibrahim Shekarau shine ya lashe zaben. Don haka fadar Shekarau yayi kokari a wannan zaben, a Rogo, soki burutsu ne. Sai dai ban san a bin da ya faru a wasu wuraren ba a jihar tamu a wannan lokacin. Bissalam.

Aminu s bakin zuwo said...

Check the date and today's political issiues to find another great victory, Ameen baba rabiu musa.