Total Pageviews

Friday, April 29, 2011

Sako 2. Murnar Cin Zaben Kwankwaso

Aliyu U. Tilde 9:11am Apr 29
Labaru sun zo mana kan irin murnar da wasu mutane ke yi a Kano ta cin zaben Kwankwaso ta hanyoyin da ya ke nuna suna maraba da shi don zai kau da Shari'a. Wannan zai sa in kura ta lafa mu yi dogon tattaunawa kan tarbiyyar al'umma a tsarin demokradiya na wannan zamanin.

Su wadanan da ke murna ta hanyar yin wadannan abubuwa, kar mu dauka da addini su ke ja. Hasali ma, sau da yawa in aka wa addininsu kalubale, ko da a gidan giya ne, to wallahi kaca-kaca ake da su. Sai su tashi su pasa kwalba, su yi ashar, su ce za su kara da duk wanda ya baci addininsu.

Wancan satin a kauyenmu, Tilde, akwai 'yan wiwi da ke busa sigarinsu a bayan gidana, da unguwata da nake shugabanta, da kuma makarantar firamare da ke kusa da ni. Mutane sun aza sun addabemu. Nakan ce mu rika hakuri da su. Suma akwai ranarsu. Don ina da sanin amfaninsu a fadan zangon kataf da sharia a Kaduna. Ile kuwa. Wancan satin, da aka ce ga kabilu can sun kawowa Tilde hari daga duwatsu, su wadannan yan wiwin su ne kan gaba wajen kare garin. Kowa sai sa musu albarka ya ke. Akwai yara da suka rika yawo suna barna suna kona gidajen kirista bayan an ce Buhari ya fadi zabe. Ko mutanen gari sun musu magana, ba sa saurarensu. Amma da zarar sun hango 'yan wiwin nan, sai su ruga, su bar wurin. To, shege ma da ranarsa!

Watau, dan Adam yana da wuyar sha'ani. In ya yi wani abu yakamata mu nazarce shi, mu gano dalilansa. Akasari sai ka ga ba abun da muke tsammani ba ne. Zai yiyu, mun tsananta wajen gudanar da sharia ta yadda ta saba da asalinta ko da zamaninmu. Zan ba da misalin shan giya.

In ka duba batun shan giya, ni a raayina an zafafa. Ko a Madinar Manzon Allah ana sai da barasa a wasu unguwanni har zamanin khalifofinsa. Haka kuma a manyan biranen musulunci irin su Damascus, da Bagadaza, da Kufa, da Seville, da Cordoba, da Alkahira. Ban taba jin inda aka yi dokar hana sai da ita ba tamaman tunda a ko yaushe, saboda sassaucin muslumci, akwai wadanda ba musulmi ba tattare da musulmi. Kai! Har a kasar Hausa, su Shehu Usumanu basu damu da su yi doka da zata hana samar da giya ba kwata-kwata. Shi ya sa kusan ake da bauda a daukacin kasar Hausa, birni da kauye. Amma tanadin sharia shi ne duk musulmin da aka kama ya sha, to a masa bulala 80. Shike nan. Akwai wanda Umar ya sa aka wa bulala don an same shi a bauda, duk da cewa an tabbatar ba giyar ya ke sha Ba. Umar ya ce to me ya kaishi zama a inda ake shanta? Wannan, a maimakon Umar ya yii dokar hana sai da giya ba.

Kuma burin sharia ba wai ta maida mutane mala'iku ba ne da za su zam ba sa laifi kwata-kwata. Sam. Allah ya fi son ya gansu a 'yan Adam dinsu, masu laifi lokaci-lokaci, amma kuma masu reman gafararsa a kullum. Ina jin akwai ingantaccen hadisi qudusi a kan wannan. Malamai suna iya binciko mana. In burinsa marasa laifi ne, ai yana da mala'iku da ba sa sabama umarninsa, suna masa tasbihi ba dare ba rana.

Don haka, yana da wuya a kauda dan Adam daga wannan dabi'ar da aka halicceshi a kanta, dabi'ar laifi da zunubi. Dama shi mai sabone asalan. Aikin addini shi ne ya kira shi ga alheri, in ya amsa sai ya ribanta da kyautata sabon nan da aikin alheri da hali nagari, kamar yadda za a hana shi mummunan aiki ta hanyar da ta dace da lokacinsa da abunda nassi ya kawo na wa'azi da ladabtarwa yadda ya fi dacewa.

Hakanan kan abubuwa da yawa wanda harkar film na cikinsu. Fasaha bata wanzuwa sai cikin 'yanci da walwala. Ai ido ba mudu ba ne amma ya san kima. Da yakamata a duba yanayin kasarmu, da matsayin tarbiyyarmu, a fara da sassauci hatta kan abubuwan da musulunci ya tsananta, kuma a yi sassauci har abada kan abunda bai tsananta ba...a bimu sannu sannu har mu fahimta, mu daidaita sahu.

Don haka, a takaice, wadannan 'yan'uwa namu ban yi tsammani wai yaki da addini suke yi ba. Hanyar da muka bi wajen d'abbaka shariar ce kila bai dace da zamaninsu ba ko d'abi'arsu. Kila mun gaggauta wasu abubuwan, mun tsananta a wasu. Don haka suka nuna bijirewarsu ga tsarin amma ba ga addinin ba.

In an tuna ai a zamanin Kwankwaso aka fara shariar, irinta wannan zamanin. Ina tuna lokacin da mataimakinsa, Ganduje, da Malamina, Aminuddeen Abubakar, suke yawo otel otel suna farautar kilakai a cikinsu. Don haka ba bakinta ba ne. Kwankwaso na da nasa malaman. Ba ni da haufin za su bari ya goyawa abunda zai maida musulunci baya.

Kamar yadda na fada jiya, sabon gwamnan sai ya gina kan abunda Malam Shekarau ya yi;ya yi gyara inda ake bukatar gyara; ya cigaba da duk abu mai kyau; ya kuma jingine, bisa shawara, abunda yake ganin kuskure ne. Amma kashedi kashedinsa, kar ya bibiye ma ashararai da za su kai shi su baro. Shekara hudu kamar gobe ne.

Haza wasalam.

Aliyu