Ban Hakuri, Nadama da Shawara Ga Yayana Prof. Bogoro. Dara Ta Ci Gida.
Na dawo daga Kano sai na iske takarda da ke nuna yayana kuma Shugaban Asusun Raya Manyan Makarantu (TETFUND) ya damu kwarai kan rubutun da na yi a kansa satin da ya wuce lokacin bayyanarsa gaban Majalisar tarayya don bayanin wasu kudade masu yawa da ake zargin an salwantar a karkashin hukumar ta TETFUND. Ya yi kukan na zubar masa da mutunci a idon duniya.
In za a tuna da farko na ce EFCC ne suka cafke shi amma nan da nan na janye rubutun da na kara bincike sai na gane ba haka ba ne, maganar ba ta kai can ba. Amma a yanzu gayyata kawai majalisa ta masa kuma maganar ta shafi tsawon 2011 ne zuwa 2015, ba zamaninsa kadai ba a wurin.
In za a tuna da na samu tabbacin EFCC ba su kama shi ba, nan da nan na shafe wannan post din a Facebook na maye shi da bayanin cewa EFCC ba su kama shi ba, ya bayyana ne kawai gaban Majalisar Kasa kamar yadda sabon post din ya nuna a kasa.
Allah ya san ban yi da niyyar cin mutuncinsa ba. Hasali ma, in an tuna, a post din farko na nuna damuwata ne kan yadda ake takurawa manyan jami'an gwamnati sai sun ba da kudi don harkar zabe a zamanin da ya shude. Kuma a ciki na ba da kyakkaywar shaida ga shi yayan nawa kan halinsa na kwarai da taimakawa al'umma. Wannan shi ne ake cewa "fair comment" da Turanci wanda kowane dan kasa na da dama ya yi.
Maganar kudi kuwa, wata majiya a TETFUND din cewa ta yi akwai wasu biliyoyi kudaden TETFUND da tsohon shugaba Jonathan ya yi kwana da su kafin su iso hanun hukumar. Hukumar ta rubuta masa a zamaninsa cewa tana bukatar wannan kudaden amma bai ba da izinin a biya ba sai kwana daya kafin ya bar mulki.
Ni, Aliyu, ban ji dadin yadda ta kasance haka ba. Ina fata zai gane cewa shi shugaba ne wanda irin wannan zai ci gaba da faruwa da shi. Rayuwar Shugabanci dabam ne da rayuwar Jami'a. Sai ya dau hakuri in ba haka ba, a inda aka dosa din nan, mutane za su haukata shi.
Dalilin fadin haka kuwa shi ne sabon Ministan Ilmi, Malam Adamu Adamu, ya nuna gwamnati ta yi haramar binciken wasu manya manyan kwangiloli a manyan makarantun kasar nan. Fatarmu kawai kar abin ya shafi TETFUND. Haka kuma, ba mu san abinda majalisa za ta gano ba a cikin bincikenta. Shin za ta gano akwai badakalar ne, daga nan ta mika wa EFCC maganar, ko kuwa za ta wanke TETFUND gaba daya. A tsakanin nan maganganu za su yi ta yawo.
Zan ba da misali da kai na. Lokacin da muke Transition Committee na Jahar Bauchi, an yi zargin cewa an ba ni N560 million wanda wai na tura account din Gwamna M.A. Abubakar. Na san wanda ya buga labarin, ina ma da wayarsa. Amma ko kadan ban yi zaton in damu ba tunda na san ba daidai ba ne. Sai kawai na yi rubutu a shafina na Facebook cewa maganar ba daidai ta ke ba kuma kudin da aka ba mu don gudanar da ayyukan kwamiti din bai kai kashi daya bisa goma na abinda ake zargi a kai ba. Na kuma yi alkawarin zan lissafa kowane kwabo da muka kashe in mika wa gwamnati lissafin a karshe don wanda ke sin gani ta je ta gani. Haka kuma aka yi. Ba na jin akwai wani mahaluki yau da ya yarda an ba ni N560 million.
Professor Jega har waka aka yi ana zagin uwarsa an yi amma shi m bai nuna irin wannan damuwa ba. A karshe, gaskiyarsa ta bayyana. In kana da gaskiya, zargi ba zai dame ka ba kuma a karshe Allah zai tabbatar da gaskiyarka.
Don haka in shugaba bai sa hakuri ba ya biye wa yan koren da ke gabansa wadanda burinsu su tatse shi ne, to a gaskiya zai shiga fitina da yawa hannun yan jarida da jama'ar gari. Shawarata ke nan.
Karshe, kowa ajizi ne, tun ba marubuta ba. Sau da yawa na ga manyan marubuta, kamar su Muhammed Haruna, suna kuskure. Asalan abin yana biyo kuskure ne wajen.rahoton da.ya zo maka. Sai dai doka ta ba da dama na janyewa, watau retraction. Allah ka raba mu da girman kan jin mu mun fi karfin kuskure. La sa mu cikin masu karbar kurensu kuma su gyara!
Allah huci zuciyar yayana, Professor Bogoro, ya sa ya gama da fitinar TETFUND lafiya, ya baiwa mahassada kunya. A nan dai Dr. Tilde ya kobsa, don kuwa dara ta ci gida.
Dr. Aliyu U. Tilde
Please share.
No comments:
Post a Comment