Total Pageviews

Saturday, May 14, 2011

Sako 3. Maraba da Dokar Hana Sadaka a Legas

SAKO 3
MARABA DA DOKAR HANA SADAKA A LEGAS
Dr. Aliyu U. Tilde
 
 
A farkon wannan satin, gwamnatin Jahar Legas ta zartar da dokar hana baiwa mabarata sadaka a titunan garin Legas. Wannan dori ne kan dokar hana barar kwatakwata wacce aka kafa shekarun baya da matakin kwaso masu barar a mota daga legas din ana jibge su a manyan garuruwan Arewa, musamman Kaduna.
 
Dokar hana sadakar ta tanadar da daurin shekara biyu ga duk wanda aka kama yana baiwa mabaraci sadaka a titunan Legas. Ba hana sadaka dokar ta yi ba, don ta yardarwa duk maniyyaci ya kai sadakarsa masallaci ko coci ko gidajen gajiyayyu wadanda gwamnatin jahar ta tanadar.
 
Wani ya ji dokar ta zo masa bambarakwai. Dokar hana sadaka? In ma ba a ci sa’a ba sai ya dorawa Gwamna Fashola kaulasen don a ganinsa ya zama manna’in lil khairi, watau “wanda yake hana alheri”.
 
Ni kuwa a ra’ayina wannan doka ce da aka jima ana jiranta, wacce kuma za ta taimakawa al’umma fiye ma da dokar hana bara ko matakin kwaso mabaratan a maido su Arewa. Hukumomi sun sha yin dokar hana bara amma mabarata sun yi biris da wadannan dokokin tunda barar ta zame musu sana’a. Amma in aka hana mai bayarwa, ka ga mai bara in ya gama shan ranarsa yau a titi, gobe ma ya sha, jibi ya sha, ba tare da  samun ko sisi ba, gata zai yi wa kansa kiyamul laili. Sai ya zauna a gida yayi ta rusawa Fashola ashar. Nan ma, in ya ga ba ci, sai ya daina ya doshi masallaci ko coci kamar yadda doka ta tanadar. Kaga ba duka ba zagi an kau da ganinsa akan titi inda yake sa kansa cikin hadari kuma yake zubar da mutuncin addininsa da na jinsinsa.
 
Na yarda cewa a gaskiya Fashola ya san kan tsiya. In ba mangala, me zai kai jaki gona? Farkon na ji irin wannan doka a kasar Nijer ne. Su mutanen Nijer in anyi obalod (watau cika mota da fasinja fiye da abun da doka ta tanada), ba direban jandarmai su ke kamawa ba. A’a. Ba ruwansu da shi in sun tsaiyar da mota. Fasinjan da aka yi obalod din da shi shi ne suke fitarwa suyi ta jibja sannan su hukunta shi. Ka ga gobe in ya zo tasha ya ga mota ta cika, ba zai ce a yi obalod da shi ba. Kan da Gwamna Sule Lamido na Jigawa ya gane ma, shi ma da haka ya yi.
 
Mu koma kan batun bara. Kamar yadda na ce, ina maraba da dokar hana bada sadaka a titi, ba ma na Legas ba, ko a titin Bauchi ne, in Gwmanonin namu suna da katabus din yin haka. Ra’ayina akan bara, sabanin almajirci, sanannne ne don na rubuta dogon sharhi a kai bariya waccar. Almajirci wani abu ne dabam. Shi ba bara ba ne, tsarin karatun muhammadiya ne da ake koyawa yara iya karatu da rubutu, da kuma karatun Kur’ani Maigirma, da haddace shi, da rubutashi. Bara kuwa it ace gararambar da manya da yara suke yi akan titi da guraren da jama’a ke taruwa, ana roko. Akwai almajirai da yawa da basa roko akan titi da matattarar mutane. Tsanani in suna yara sukan bi gidajen mutane suna ko dan kanzo. In ko sun kai shekara 14, to sai su fara sana’a kamar noma, dinkin hula, kasuwanci da sauransu kafin su karasa hada haddarsu. In sun cira gaba kadan sai aure, da iyali, da rayuwa kamar to kowa. Don haka nake da tsattsauran ra’ayi kan bambamta bara da almajirci.
 
To, ina ga katon da yake baje nakasarsa a fili yana nuna wai ga abun da Allah ya maida shi don kawai a tausaya masa a bashi kudin kashewa? Kuma inda Legas kachaukau dinta za ta taru yau ta bashi kudin Alhasan Dantata, ba godewa Allah zai yi ba ya hakura ya zauna a gida. A’a. komowa gobe zai yi yana nuna dungun hannusa ko tsiyayayyun idanunsa yana cewa a bashi don Annabi. A dole ga shi shi ne wanda Allah bai yiwa gata ba.  Subhanallahi. Can gida kuwa ya yi asusu sai tara kudi ya ke yi jiddin-wala-hairan har ya sayi motoci da gidaje, abunda akasarin yake roka ma basu da shi. In ko baka bashi ba, wani mabaracin ma har zambonka zai yi, ya ce wa ‘yan uwansa mabarata, “wannan maciji ne” (wai don ka daga hannu ka ce ya yi hakuri), ko ya kiraka “Shago” (watau mai hanu dunkule kamar dan dambe), da dai sauransu.
 
Inda za ka gane bara ba tilas ba ce shi ne Malam Bahaushe ne kawai yake yin ta a Najeriya. In an ce Malam Bahaushe, ana nufin musulmin da ke Arewacin Najeriya kama daga kasar Nupawa har zuwa Sakkwato da Barno. Ka taba ganin wani dan kabilar kudu ko tsakiyar Najeriya yana bara, ko da kuwa musulmi ne? Wannan aikin sai mu, da yake mu muka fi rena wa Ubangiji. Don haka aka renamu a kasan nan, ake ganin mun fi kowa ci baya da talauci.
 
Wasu sun dauka wai bara musulunci ne. Wanda ya ce haka ya yi wa Allah karya. Daga Bakara har Nasi ba inda aka ce wani ya mai da bara hanyar cin abincinsa ko tara arziki. Abunda nassi ya yarda da shi shi ne mabukaci ya baraici daidai da bukatarsa inda yake zaton samun biyan bukatar musamman ma a tsakanin danginsa ko abokan zamansa na kusa wadanda yake da hakki kan dukiyarsu kamar yadda ya zo a Kur’ani. Amma ya tashi takanas ta Kano ya tafi wani gari da sunan bara wannan al’adar Malam Bahaushe ce da take barar da mutuncin jinsinsa gaba daya. Dole ne sauran kabilu da ke bashi sadaka Allah ya daukaka su a kansa, don maganar Annabi ba za ta fadi kasa banza ba, da ya ce hannu mai bayarwa yana sama da hannu mai karba.
 
To in musulunci bai yarda da bara ba, me zai sa ba za mu marawa gwamnatocinmu baya ba wajen tumbuke wannan mugunyar itaciya da take zubar mana da mutunci? Na yi murna mutane sun fara fahimtar haka don ban ji wani mai mutunci da ya ce Fashola ya yi laifi ba. Ni kam yamun daidai. Fata nake sauran gwamnoni su goyi bayansa, musamman na kudu, kafin dokar ta hauro nan Arewa.
 
Sai dai kuma wani hanzarin da ba gudu ba. In a Legas akwai gwamnati mai karfi, a nan Arewa bamu da gwamnatoci da za su iya aiwatar da doka, kowace iri ce kuwa. Kai dai a bar gwamnoninmu wajen yin gululu a zabe da sayar da hakkin jama’arsu samanan kalilan wa ‘yan kudu. Nan kam ba wanda ya fisu. Amma da sannu za su taho da abunda suka yi gululunsa ranar Kiyama.
 
A karshe muna jinjinawa Gwamna Fashola don wannan gagarumin taimako da ya yi wa Arewa. Muna kuma yi masa fatan Allah ya kara masa basira da hazaka.
 
Ba karambanin da zai sa in sake baiwa wani musaki sadaka a titin Legas. Ina sauka filin jirgi a Ikeja, zan kama zip din lalitata in ja, zeeep. Ba sadaka, sai a masallaci, in na yi niyya.

Tilde,

15 May 2011

23 comments:

Muktar Bature said...

Assalamu Alaikum,

Ina rokon Allah suhnahu wata'ala ya sa mu fahimci sakon Dr. Tilde, gwamnatocin mu kuma su farka.

Abunda yake mafi muhimmanci a cikin wannan rubutu na Tilde shine bambanta Almajiranci da Bara.

Jazakumullah.

Abdulkadir said...

Assalamu alaikum Malam Aliyu,

Ni dai na goyi bayan wannan raayi naka dari bisa dari, musamman matsayin da ka dauka duk lokacin da ka shiga Legas. Nima ka koyar dani.

Allah sa jamaar kasar hausa ta farka ko zata dawo da mutucinta, amin.

Abdulkadir Jibril

Abdulrahman Abdulsamad Kankia said...

Wannan abin yabo ne gwamnan Legas yayi. Da gwamnonin arewa zababbu ne da sunyi koyi da Fashola a samu ci gaba.

Tilde kayi kokari wajen rarrabe bara da almajirci, Allah yasa hakan tasa a samu waraka.

Tilde wasu abubuwan bahaushe da aka maida addini kuma suke hana mu ci gaba sune MISALI MUTUM YAYI HADARI DA MOTA (KO DA BISA GANGANCI NE) AMMA SAI KAJI ANYI WUF ANCE "HAKA ALLAH YASO" KO KUMA "AI KADDARA CE". Saboda haka ba'a bincike bare a samu gyara.
Menene bambancin GANGANCI da KADDARA?

amadu sajoh said...

Well I don't speak Hausa, but Fulfulde, and I am happy to see intellectuals like Dr Tilde is writing in an African language, this will definitely give our languages more prestige.

For those who may like to read article in Fulfulde, please go to: www.peeral.com

Keep up the good job, Dr Tilde.

Mi yettii ma masin.

M. D. Magaji said...

Babu shakka Dr. Sheikh Aliyu Tilde ya sosa min inda ke yimin kaikai! Duk in da mutum yaje, Hausa/Fulani ne mabarata. Saboba haka, Gwamna Fashola yayi abinda yaddace. Kasashe da dama na musulmin duniya sun yi Allah waddai da bara tuni, domin yin hakan, babu shakka yana zubadda mutuncin Musulmi da Musulunci, kanar yadda yake faruwa garemu musulmin Nigeria. Da fatan gwamnonimmu zasu doki irin wannan mataki da Fashola ya dauka, amma su kara da baiwa talakawansu, musamman mabukatan gaske, da hakko- kin su. Allah (SWT) Shi tabbatadda khairinSa, ameen. M. D. Magaji.

Mainasara said...

Haka ne,Aliyu Sarkin yakin Sarkin Musulmi.Amma ba na soja ba.

Maliki K. Umar said...

Malam Tilde, Allah Ya saka da alheri. Ina ma shugabannin mu za su iya abin da Fashola yayi? A Kano, misali, akwai dokokin da suka hana bara da talla a titi. Amma, kash! Shugabannin baza su iya tabbatar da ganin an hukunta duk wanda ya saba wa dokokin ba. Allah Ya kawo mu zamanin da shugabanni suke tsoron gaya wa jama'ar su gaskiya. Kusan duk shugaban da ka zauna da shi, ka tattauna matsalolin bara, za ka same shi yana kin ta; amma bai isa ya fito fili ya kyamace ta ba. Na tuna wata hira da aka yi da marigayi Janar Hassan Usman Katsina a kafafen yada labaru; ya nuna bakin cikin sa akan yadda muke zubar da mutuncin mu sabo da bara. "Bahaushe" ne kawai ya ke yin ta, sai ka ce shi kadai ne ya ke talauchi a duniya. Watakila da shugabannin mu za su kamanta kyamar bara kamar yadda Janar Hassan ya yi, da watakila annobar ta ragu. An ce wani malami ma ya ce masu bara ne direbobin da zasu kai mu al-janna.

Allah Ya sawake.

Salih said...

Dokta aima da hadisan manzon tsira (S. A. W.) da suka hana lalaci, mutuwar zuciya, roko da sauran su. A yau kuwa barar ta za ma roko, mutuwar zuci da lalaci.

Danbauchi said...

Ni ma na ce Allah Ya sa Malam bahaushe ya farka daga barci, ya fahimci illar mayar da bara sana'a, domin ba a Lagos kawai ba, har Sa'udiyya da Sudan idan ka je za ka ga Bahaushe, abin kunya, yana yawon bara a kan titi, kamar tun da Allah Ya halicci duniya shi kadai ne maraya. Allah kuma Ya sa gwamnatocinmu a jihohin arewa su ma su farka su haramta yin bara a kan titi. Mai bukata ya je masallaci ko coci ko kuma a kafa gidajen marasa galihu su je su taru a can. Amma irin kaskantar da jinsin Bahaushe da bara ta ke yi, abin da ban haushi. Kai, Dr. Tilde ka burge ni da wannan bayani naka.

Anonymous said...

@aliyu, on yours "....Fasinjan da aka yi obalod din da shi shi ne suke fitarwa suyi ta jibja sannan su hukunta shi", this is quite barbaric for anyone and for whatever cause to do. while overload is bad, jibgar anyone for it is utterly inhuman.

jamilu y jega said...

Allah sarki na Tanko....( Bahaushe),yau takai a kaddamar da doka kanka a garin legas.To sai mun gani! yaya zakayi? zaka ci gaba da zamanne ana tsanarka,ko zakaci gaba da wulakantar da kanka kana gararanba a tsakanin masallaci da coci domin sadaka?...Allah ya karawa Danmasani( Dr tilde) basira, ya kuma karemu da wulakantar da kanmu amatsayin mabarata a kasannan.
wassalam,

Jamilu y. jega

Ahmad Arab Abubakar Azare said...

Yayi amma dai dokar tayi tsauri matuka. Kamat yayi a tunani kwarai.

Hajiya Lami said...

I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will be good for Nigeria if more people come out and speak and write the truth as they see it.

Hajiya Lami said...

I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will be good for Nigeria if more people come out and speak and write the truth as they see it.

halima said...

Yau da safe na yi fakin domin bawa masu bara kudi. Sai da diya ta ta fita da gudu domin mun wuce su kadan, kuma sai da muka hada canjin mu da nawa da nata, har ma a ka yi ta mana horn domin mun tare hanya (a abuja). Amma ina kyautata zaton ba taimako bane, sam. Saboda haka na yarda da nazarin da Dr. ya yi. Sadaka fisabilillahi ba lallai sai a titi ba, Allah ya ba mu ikon gane wa, amin.

Al-fazazi said...

Allah SWT Ya numa nama ranar da za'a ce bahaushe ya yi watsi da bara ta ko wace irin hanya. Watau Allah SWT Ya kau da akidar maula, tumasanci, raraka, banbadanci (roko),'Allah Ya baku mu samu','In an bamu a tsunkule hannu', 'samun ku shine namu' a cikin zukatan hausawa. Amin summa amin. Haza wassalam.

Nuhu Abba Ibrahim said...

Allah na kwana biyu bana bada sadaka a kan titi, akwai bukata a cikin 'yanuwa na da makota. Wannan doka na maraba da ita ya kamata Gwamnonin arewa su dauki irin wannan matakin. Amma maganar almajiranci da bara na yarda akwai banbanci, sai a zamaini yanzu almajiranci a manyan biraanan mu ya zama matsala, iyaye daga 'kauyuka na turo yara birane saboda su guji hakkin dake kansu na kula da su. Maganar tsangaya kamar yadda Gwamnati Mallam Shekarau suka fahinta a Kano na bukatar a duba, saboda tana tare da matsala. Tsangaya an san tun da a Kauye da daij take ba cikin birane ba. Allah ya sa mugane.

Kabiru said...

Malam daidai ne wannan Dokar Allah ya kawo ta KANO abin yayi yawa.

Kabiru Yakasai

Daily trust, kano

Bashir Yahuza Malumfashi said...

Wannan doka a kan hanya take, sai dai kamar kowace doka a Najeriya, ba za ta taba yin tasiri ba, muddin dai ba tashi tsaye aka yi ba, aka nuna cewa da gaske ake yi.
Maganar bara kuwa, yau sama da shekara 50 ke nan da marigayi Malam Sa'adu Zungur ya gargadi al'ummarmu, da cewa mu kiyayi wannan mummunar ta'ada. Ya yi wannan gargadi ne a wakensa da ya sanya wa suna "Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?" Ga shi mun yi biris da ita, muna ganin illar haka.
A shekarun baya, marigayi Janar Hassan Usman, shi da su Kanar Usman Jibrin sun taba turza hana bara, amma wasu rubabbun malaman Musulunci suka yi musu caa, suna dakile musu himma. Ni kuwa na ce idan mun ki ji, ba ma ki gani ba.
Allah Ya ganar da mu gaskiya kuma Ya ba mu ikon bin ta, amin.

Bashir Yahuza Malumfashi
byahuza03@yahoo.com
08065576011

A. Y. Safana said...

Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.

A. Y. Safana said...

Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.

A. Y. Safana said...

Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.

Rabia Husaini Adamu -Eshak said...

Wannan doka da Fashola yayi kalubale ne kan gwamnonin jihohin arewa ,da suke haduwa yau sama da shekaru talatin akan neman hanyar hana barace barace, amma hakan bai yiwu ba har yau. Yanzu ko dai shugabanin mu na arewa su tashi tsaye wajen shirin killata bakin da za mu samu nan da 'yan kwanaki domin kuwa Legas tayi musu zafi tunda babu na bati,ko kuma mu shirya kara tabarbarewar al amurran mu.Yakamata Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu mu fara tunanin karfafa tarawa da raba dukiyar zakkat ta hanyar da a zamanance ake kira "STRATEGIC PHILANTHROPHY"