SHARHI NA 5.
MATSALAR TALAKA
Na Dr. Aliyu U. Tilde
Jiya aka tafka wata muhawara a Arewa INEC Registration Group, daya daga cikin zaurukan Intanet na Arewa. Uwata mai suna Nana Asma'u Gwadabe ce ta ce ita takaici ya dameta don 'yankudu suna zagin manyanmu mu kuma muna tayasu. A karshe, inji Nana, mu ke cutuwa don komai munin 'yar yatsa, mutum ba ya guntuleta ya yar. Naka ai nake ne, ta ce.
Maganarta kuwa ya biyo bayan yadda wasu 'yankudu suka yi ca akan Mai Martaba, Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ne don ya tsawatawa Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Namadi Sambo, akan rashin tsaida lokaci. Namadi ya ce zai zo fadar Sarki karfe 10, amma shi ne bai bayyana ba sai karfe daya. Sarki da jama'arsa suka sha jira na tsawon awa uku. Wannan shi ya sa Sarki ya nuna bacin ransa, yace wa Namadi haka bai kamata ba, kuma ya ce su tarbiyyar su Tafawa Balewa da Sardauna ne, suna girmama lokaci. Sarki kuma sai ya koma gun Gwamnan Kano Shekarau ya tuhumeshi akan rashin sanar da Namadi al'adar fadar Kano wajen kiyaye lokaci. Wannan maganar ita ta sa wasu 'yankudu zagin Sarki suna nuna wai waye shi da zai yi wa mataimakin shugaban kasa fada? Nana kuma wannan ya 'bata mata rai ta zo zauren intanet ta bayyana bacin ranta.
To, akasarin wadanda suka yi sharhi akan batun sun goyi bayan Nana, amma dai akwai kalilan wadanda suka nuna cewa ai sarakuna su suka zubar da mutuncinsu, kamar yadda ake cewa sun ci amanar talakawansu lokacin zaben shugaban kasa da ya wuce. Wata ma har tambaya ta yi wai a gaya mata meye Sarkin Kano ya yi wa Kano a shekaru takwas din da suka wuce. Kamar yadda nace akasarin masu sharhi sun ce sarki ya yi daidai, tunda ya yi kira zuwa gyara ne. Gyara kayanka kuwa ba sauke mu raba ba ne.
Amma wannan batun ya sa na yi tsokaci kan wani abu da tuntuni nake son inyi rubutu a kai. Shin wai talakawa na da ikon nunawa sarakuna yatsa a Najeriyar mu ta yau kan rashin cigaba ko koma-bayan da Arewa ke fama da shi? A fahimtata dai talaka bashi da wani kwakkwaran dalili; komai ya faru gazawarsa ne tunda ya gagara amfani da ilmi da 'yancin da tsarin mulki ya bashi ta fuskoki dabam dabam don ya kyautata rayuwarsa.
Na farko dai in a lokacin N.A. za a zargi sarakuna da handama da danne talaka, to yau Allah ya kawomu lokacin da an gama kwace mulkin daga hannunsu an mikawa talakawa kacaukau dinsa. Ikon sarakuna ya rika ja da baya tunda Sardauna ya fito da tsarin kananan hukumomi wanda aka yi ta karfafa ikonsu a shekarun da suka biyo baya har an kai inda a yau ba su da mallakar komai na madafar iko. Talaka yau shi ne wuka shi ne nama. Ina mamakin yadda za a bar dukan jaki a yi ta bugun taiki.
Ni dai talaka ne. Ba inda zurriyarmu take da nasaba da sarauta. To amma irina muna da yawa da Arewa ta ilmantar damu don mu zame mata garkuwa in mun kawo karfi. Su Sardauna, Balewa, Malam Aminu Kano da sauran magabata, kamar yadda Magaji Danbatta ya gaya mun, sun zata idan aka ilmantar da talaka to Arewa za ta cigaba, matsalolinmu za su kau.
Banda ilmantar damu, Sardauna musamman ya fara canje-canjen da zai maida Arewa kasa ta zamani a bisa turbar demokradiyya tunda ya fahimci kwanakin mulukiyya sun tasamma 'karewa. Akan wannan sun samu sabani da sarakuna da yawa har abun ya kai ga tube wasu daga cikinsu.
Hakika, a kokarinsu na tabbatar da mun amfana, magabatanmu sun sadaukar da rayuwar duniyarsu da rayukansu. Sun rike amana matukar riko. Ba wanda ya bar wani abun azo a gani bayan ransa, har Balewa da ya yi Shugaban Kasa da shi Sardaunan da ya yi Premier na Arewa. Sun tsaya tsayin daka wajen kare hakkinmu ta hanyar tabbatar da abokan zamanmu daga kudu basu dannemu ba kamar kuma yadda suka wahala kwarai wajen tabbatar da hadin kanmu duk da bambamcin harsuna da addinanmu. A karshe, wasu 'yankudu suka kashe su, suka yi shahada saboda sun hana wasu damar su mallakemu. Ko a kabarinsu har yau zaginsu 'yan kudu suke yi…da wasu lalatattun 'yan Arewa da ke taimaka musu.
To amma me muka sakawa wadannan magabatan namu da shi? Shin mu 'ya'yan talakawa mun rike amana kamar yadda suka zata? Shin mun yi amafani da ilminmu da arzikin kasa da aka danga a hannunmu wajen cimma burin cigaba? Shin mun iya mun kare Arewa daga 'yankudu kamar yadda su Sardauna da Sarakuna a lokacin suka yi? Wannan abubuwan su na yi ta tunani akai cikin shekaru goma sha biyu da suka wuce tun da na fara rubutu a jarida.
Fahimtata itace mu talakawa muke dauke da babban laifi in ba dukkansa ba.
Matsalar farko ta rashin hada kan arewa dai mu talakawa muka jawota. Gowon ya rarraba arewan nan jaha jaha don tsirarun al'ummomi su samu yanci. Muka goya masa baya. Muka karawa kananan hukumomi iko. To gashi yau muna kuka da rashin hadin kai. Ya zaka hada abun da kake son ya dauwama a rababbe? Ta nan raunin Arewa ya faro, har aka shigemu aka mana zarra.
In kuwa zancen lalacewar mulki ne nan ma mu talakawa sai mu kuka da kanmu. Mu fara da mu'kamin shugaban kasa. Ai ba wani dan sarauta da ya taba zama shugaban kasa: Gowon, Buhari, Shagari, Babangida, Abacha, Abdulsalami, Obasanjo, Yar'adua, da Goodluck, duk 'ya'yan talakawa ne in ka debe cewa Shagari dan hakimi ne, kuma uban 'Yaradua yana da sarautar jeka-na-yi-ka ta mutawallen Katsina.
Hakaza duk wadanda suka yi mulkin jihohinmu tun da aka kirkirosu, banga wani sarki da aka nada ko dansa da ya tsaya zabe don ya zama gwamnan jahar sa ba. A cikin soja ne ma kad'ai aka samu mutum daya ko biyu irinsu Sani Sami ko Muhammadu Jega wadanda suka yi gwamna da suka fito daga gidajen sarauta. Amma saura karib dinsu, sojansu da farar hularsu, 'ya'yan talakawa ne. In mai karatu ya musa, ya zana gwamnonin jaharsa, ya ga ko akwai wani dan sarki a cikinsu.
In mun dawo kasa, wajen ministoci da manyan ma'aikata a tarayya da gwamnatocin jihohi, da chairmomin local government, maganar daya ce. In ka cire irin su Hasan Usman Katsina da Shehu Yar'adua da suka yi mulkin soja, yana da wuya ka ce ga 'ya'yan sarakuna a cikin wadanda suka rike mukaman da muka ambata.
Banda mu'kaman mulki, in mun duba fannin ayyuka irin likitoci da malaman makarantu, kashi nawa ne daga cikinsu suke 'ya'yan saraki?
Mu talakawa mu kuka da kanmu. Mu muka ci amanar ilmi muka ci amanar dukiyar kasa da siyasarta. Mu muka kashe jihohinmu, da asibitocinmu, da makarantunmu, da tsare tsaren bin doka da 'da'a, da sauransu. Daga samun mulki ya dawo hannunmu sai muka shiga sata, sata, sata, sata, ba kunya ba tsoron Allah. Akasarinmu muna haka ne saboda talaucin gidajenmu wanda muke tsoron komawa cikinsa, da rashin sanin menene mulkin kansa, da rashin kishin zuci, da rashin tsoron Allah. Wallahi mun ji kunya, mun nuna talaucinmu a fili. Ta wannan hanyar kome ya lalace har talaucin zuci da na aljihu ya samu ya yi 'ka'ka-gida a Arewa.
Bugu da kari, sai muka nuna bamu damu da kowa ba, ba da talakawa 'yanuwanmu ba, ba kuma da manyanmu ba cikin sarakuna, da malamai da attajirai. Kanmu kawai muka sani. In likitoci ne mu, sai mu sace magunguna da na'urorin aikin da aka saya don amfanin jama'a. Ga asibitocin nan, fayau. In malaman makaranta ne, sai mu sace takardun karatu; kai, har naga makarantar da shugabanta, talaka, ya shiga warware jinkar makarantar yana sayarwa bayan ya gama saida na'urorin fasaha da sauransu. Kuma 'ya'yan talakawa a ma'aikatar ilmi suka daure masa gindi har yau yana aiki. Akasarin malamai kuwa sai sun ga dama suke koyarwa. Ga makarantun nan, sha-'kura, ba a koyar da komai a ciki banda yara su yi ta safa da marwa na banza. Don Allah, meye hannun sarakuna a cikin irin wannan ta'asar da muke tafkawa babu 'ka'kkautawa?
In don mun sha kaye a siyasa ne muke korafi yakamata mu fadawa kanmu gaskiya. Tun yaushe talaka ya amshi hudubar maguzancin gurguzu ya dau gaba da sarauta? Yau shekara sama da hamsin kenan. In ka debe gurare kadan a Arewa-maso-yamma, talaka ya jima da samun 'yancinsa. Ba ya sauraren sarki in ba yana da bukatar a sa masa hannu a filin da ya saya, ko takardar indijin, ko in fitina ta taso, ko in an ga wata, ko wani abu mai kama da wannan wanda ba yi da tasiri a mulki. Zaben da ya ke yi ba sarki zai zaba ba, dan'uwansa talaka zai zaba wanda zai ci amanarsa.
In magudi aka yi, su waye suke magudin? 'Ya'yan talakawa ne da ke kan mulki suke zuwa su sato kudi a baital mali da bankuna, mangala mangala, su baiwa talakawa 'yanuwansu a cikin ma'aikatan zabe da na gwamnati, da 'yan kwaya da 'yan sara suka, da 'yan siyasa. Wadannan su ne suke murde abunda 'yan uwansu talakawa suka zaba, su dora son rai. In an kai 'kara ma a kotu duk tsiyar daya ce. Talakawa ne suka cika kotun. Shi ne mai shari'a, shi ne dan sanda, shi ne lauya. Sai su amshi kudi su danne gaskiya miraran.
Hakika a zaben da ya wuce ran talaka ya baci don ya sha kaye, mummuna kuwa. Amma laifin faduwan nan ya koma kansa ne. A sharhin da na yi makon jiya, na ce talaka kamar ruwa ya ke. Kome yawansa ba zai tsinanawa kansa komai ba in ba da sa hannun shugabanni ba. Duk yadda ruwa ya kai da yawa, sai an tareshi yake amfani, in ba haka ba, zai malala ne kawai ya koma teku. Tsirrai ma ba don Allah ya sa kasa na rike ruwan na dan lokaci ba, da suma ba za su amfana da shi ba. Amma in aka tare shi a masaki, ko a randa, ko a dam, to sai a sha, a yi ibada, har a yi noman rani da shi.
Hakaza talaka. Yana da amfani ne kawai in yana da shugabancin mutum uku: sarki, malami da attajiri. Ukun nan suna da muhimmanci wajen siyasa musamman irin ta wannan zamani. Shugabanni su za su tattara talaka, in da hali, su nuna masa ga inda zai dosa da kuri'arsa har kuri'ar ta yi masa amfani. Mutanen kudu haka suke yi. Shi ya sa koyaushe kuri'un kowane yanki a cikinsu ke tahowa dunkule ta yadda zai amfanesu a tsarin zamantakewar Najeriya. Amma banda 'dan Arewa! Shi ya san komai, bai jin kowa, bai girmama kowa. Don haka wannan karon da ya yi hobbasa wai don ya yi abu shi kadai, dole gazawa ta sameshi.
Da farko dai talaka a zaben da ya wuce ya nufi wani gu inda ba wanda ya isa ya ce masa dawo. Baya jin kira. In ba Buhari ka ce masa ba, to sai ma ya auna maka kaulasen. Ba wani mai fada a ji, walau sarki, ko malami ko attajiri da ya isa yace tak. Shi, talaka, a dole sai ya karya ka'idar rayuwa. Shi za a bi, ba shi zai bi ba. Muma da muka yi kokarin nuna masa kuskurensa ba irin sunan da bai kira mu ba. To sai yanzu da ya fadi, sai ya dawo yana zargin shugabanni. Ban ce ba sarakunan da basu taimakawa Goodluck ba ko sun fi karfin kuskure ko laifi. Amma in da talaka mai amfanar kansa ne ai da ya san basu da iko kan k'uri'arsa. Wai shin me ya sa tuntuni talakan nan ya ki zaban Aminu Kano ne wai?
Kuma a duba alkalumman zaben mana. In da talakawa sun yarda da 'yanci da cigaba, ai da ba'a samu tazara mai yawa tsakanin Goodluck da Buhari ba. Mutum nawa suka ki fitowa zaben shugaban kasa a arewa-maso-yamma inda Buhari ya fito kuma yake da mafi yawan magoya baya? Miliyan goma cus! Dauki wannan adadin ka kara akan miliyoyin da basu fito zaben ba a sauran sassan Arewa, ko wadanda suka fito amma suka zabi Goodluck a matsayin dan takarar jam'iyyarsu ta PDP ko suka karbi kudi da sauran 'kayan aiki' suka zabe shi, suka bar Buhari. Kanda talakawa basu nuna kwadayi ba ko gajiyawa wajen amfani da 'yancinsa ba, ta yaya kake tsammanin Goodluck zai yi wa Buhari wannan kayen? In ko kace ai talaucin da talaka ke ciki ne ya sa shi haka, sai ka yarda cewa 'yanuwansa talakawa da suka lalata kasannan ta hanyar sata da mummunan mulki suka jawo masa.
A takaice, har yau in talakan zai hada kai da rukunnan al'umma uku da muka ambata a sama, to wannan sashi na Najeriya yana da yawan k'uri'un da zai iya cin zabe dasu ko sau dari za a maimaita. Dole talaka ya yarda mai ilmi ya hango masa nesa; dole ya yarda mai kudi ya kawo kudinsa don kare masa kuri'a; dole kuma ya yarda manyansa su bashi kwarin gwiwar fita ya yi zaben da kareshi daga barazana. Cin zabe a ko'inan ne a duniya zai yi wuya da talauci, da jahilci, da sharri, da tsageranci.
A tawa wautar irin abubuwan da yakamata mu fara karkata zuwa garesu kenan bayan shan wannan kayen. Mu koma baya mu ga inda muka yi kuskure. Dorawa shugabanni karar tsana ba zai kaimu ko'ina ba. In muna son dunkulewa wuri guda, dole mu fahimci cewa a duniyar nan kowane dan Adam wal bani wal baka ne, wal hanani wal kememe…haka saura su ke yi. In bamu waiwayesu lokacin tsaida shawara ba, kuma ba abunda muke banda zaginsu rani da damina, to zalunci ne muce za mu dora laifin gazawarmu akansu.
A yanzu kam, mu talakawa mune babbar matsalar kanmu.
Haza wasalam.
Tilde
25 May 2011
14 comments:
Lallai wannan zance naka ta wani bangare gaskiyace, ta wani kuma akwai gyara. Babu shakka a nahawu kalmar talaka tana nufin duk wanda ba sarki ko dan sarki ba. Amma a zahiri kalma ce ayau da bata kunshi wannancan jama'a da ka lissafa ba, kamar kai kanka da ka ba da misali. Ayau talaka shine wannan da dansa ke halartar makaranta gwamnati, asibitin gwannati, ke noma (kadan)ko kasuwanci (kadan, ko bashi da abinyi sai maula, wanda musulunci ya kira mabukaci. In ko gaskiya zaka fadi, to ai kuwa wadannan mutane uku da ka lissafa, watau sarki, mai kudi da masu ilimi ba zasu taba jagorantar talaka da dadi ba, sai dai in talakawan sunyi wa kansu kiyamun laili nan gaba kamar yadda suke yi ayau a kasashen larabawa. In kuwa a tunaninka wadannan ukun sune masu ceton talaka, to lallai talakan Nejiriya zai mutu ba'a ceceshi ba. Ni a gani abinda talaka yayi bayan zaben shugaban kasa daidai ne, kuma muddin wadancan ukun da kakeso a taru a goya wa baya su ida kahe talaka basu chanza ba, to lokacin na zuwa da talakawa zasu masu boren kowa ya mutu a rasa.
Hahahahah....haba dan uwana talaka, lallai kayi gaskiya; saboda anche abunda Babba ya hangomaka to ko ka hau rimi baza kaganshiba. A yanzudai shawara ya rage ga mai shiga rigiya. Allah yaimuna jagora....ameen.
Da dai nayi hushi cewa ba zan kara yin jawabi a dandanlinka ba. To amma naga cewa akwai kura kurai waenda suke bukatar gyara a cikin tafiyar taka. Bana jayayya cewa ka iya rubutu a cikin basira ta yadda idan mai karatu baya da zurfin tunani sai dadin zancenka ya kwasheshi ku dinga tafka taasa tare. Abinda nake so ince anan kuwa shine; ya kamata ka faiyace wa mutane abinda gaskiyar kalmar 'talaka' take nufi akan bigeren da kake zance, sabo da kayi wa zance kwasan karar mahaukaciya ne kurum. Kana zaton ni zan iya saka ka cikin nauin talakawan da kake nufin suna zargin shuwagabanni da yan boko masu rike da mukamai (daya nauin na talakawan da kake zance) suke dannewa? Aa, ai kuskure ne. Ya kamata yadda ka fahimci gaskiya to karinka bayyana ta ba tare da karkata ba don kar zama abun zargi. Kowa ya san gaskiya, cewa lalle talakkan na hakika an danne shi tare da taimakon sarakunansa, attajiransa da kuma masu ilminsa, irinka. Kamar yadda kake kokarin ka nuna mana yanzu. An dake shi kuma kai kana cikin waenda ke son su hana shi kuka.
Zan barka anan, amma dai kar tayi ma zafi ka ki wallafa bayani fa.
Sai mun sake gamuwa.
To fa! "Talaka'" ya koro Talakawa!!! Ina ma talaka zai daure na dan kalilan ya saurari masu hangen nesa. Kash!!! Talauci yayi katutu a zukatun mafi yawa kamar bazai kareba! Gaskiya dokin karfe! Inaga ka saukar da nauyi a wannan dandali, saura ya rage garemu. Doc, how do we enhance the enlightenment on this forum (Discourse)? The targeted audience is fairly, off dis particular electronic networks. Won't flyers help (including having u to painstakingly, do same in 'ajami')? Well done sir! Salam. NUHU GIDADO.
Malam Aliyu,
Allah ya kara basira. Baka ban kunya ba. Fadar gaskiya wa al'umma irin tamu na bukatar jarunta. Ina fatar jama'armu ba zatayi girman kai ko jahilci ba wajen yin kunnen uwar shegu da wadannan shawarwari da ka bayar ba.
Malam Aliyu, wannan fahimtar taka nada matukar muhimmanci. Jama'ar Arewa tafi sauraron rediyo fiye da karance karance, balle ma ace rubutu a yanar gizo. Inama ace za'a karanta wannan rubutun naka ta gidajen rediyo. Ina ganin da mafi yawan jama'a sun amfana.
Allah bamu sa'a, amin.
Abdulkadir Jibril
YA KAMATA A YI WA TALAKA ADALCI DAI:
Na karanta wannan bayani naka a tsanake, sai dai ni ban yarda da cewa talaka ne matsalar kansa ba, domin kuwa babu yadda za a yi jela ta zama shugabar kai. Shi talaka mabiyi ne, na abin da shugaba ya shiryar da shi.
Mai ilimi, sai ya yi amfani da iliminsa wajen wayar da kan talaka da fadakar da shi, sannan talakan zai gane inda ke yi masa ciwo. Amma idan mai ilimi ya zabi ya lalata tasirin abin da ya koya, ya zama barawo, maketaci, ya sace kayan koyarwa, ya handame, ya rika tura 'ya'yansa Ingila suna karatu, alhali na talakawa suna gida ko suna gararamba a titi, ban ga dalilin da zai sa a kara dora wa talaka laifi ba.
Shi kuwa mai mulki, idan dai ya dafe mulkin, to fa ya tashi daga talaka, koda kuwa babansa ya fi beran masallaci talauci. Don haka, a lokacin da yake kan mulki, ya zama dole ya kasance adali, ya raba arzikin kasa daidai-wa-daida, ta yadda talakan zai samu ilimi, zai samu muhalli, zai kuma samu inda zai rika yin kwadago, yana samun abin sa wa bakin salati. Amma kash, sai masu mulki suka kasance azzalumai, barayi... Kuma don rashin adalci sai a sake zargar talaka da jawo wa kansa bala'i? Haba Malam Tilde, a sake nazari dai!
Shi kuma malamin addini da ka sanya sabulu ka wanke shi, ta ina zai wanku? Ilimin addini da Allah Ya ba shi, maimakon ya yi amfani da shi wajen jawo talaka a jika, maimakon ya yi amfani da shi wajen hada kan talaka da fadakar da shi bisa gaskiya, sai ya bige wajen yi wa masu mulki tumasance, ya bige wajen yi masa tsafe-tsafe da tsubbace-tsubbace. Kuma shi ke nan idan abu ya kwabe, sai a ce za a zargi talaka. Haba! Ai dukan zai yi masa yawa. Rai dai, wai an cire wa kuda kai!
Mu dai fatarmu, Allah Ya ba talaka jagora ta kwarai. Jagorar da za ta fitar da shi daga kangin jahilci, daga duhun talauci!Wannan kuma zai samu idan aka samu sahihan shugabanni, sahihan malamai da sahihan attajirai. Allah Ya ba mu su. Amin.
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
byahuza03@yahoo.com
08065576011
haba mal Bashir ka ce ka karanta bayanin Dr a tsanake, amma ni sai na ga kamar baka fahimce shi ba. Domin ba yadda za a ce don an zabi dan talaka a wani matsayi ko ya je makaranta ya sami ilmi shi ya mai da shi basarake. Abin nufi anan shine, shifa dan talakane wanda yanzu ya samu yanci kuma yasamu damar gogayya kafada da kafada da kowa sabanin halin da ya sami kansa a da na rashin yanci da talauci, bai kamata ya mance halin da dan uwansa talaka yake cikiba.
A gaskiya a Arewa matsalolinmu ba za su kau ba sai mun yarda mu hadiyi gaskiya komai dacinta. Kan da dan talaka da aka ilmantar bai mance da asalinsa ba ai da yanzu Arewa an yi nisa. Wannan gaskiyar, gata a bayyane kamar rana, itace wasu ke kokarin karyatawa don su ci gab a da yaudarar talaka cewa sarakuna ne awoken gabanshi. Ina ga wancan zamanin ya wuce. Akidar gurguzu ta kau. Ko dan talaka ya koyi hali nagari ko iyayensa da zurriyarsa su ci gaba da shan wuya cikin jahilci, lalaci da talauci. An bashi yanci amma son kai da karamin hali ya hana ya rike amanar danginsa mutanensa.
DR, ni aganina talaka bashine matsalar ba ,sabada shi talaka, ya sa mu kansa ne achikin halin kakanikayi,achikin tarkon talauci da jahilci dakuma rashi shgabanci nagari.Amma babban mailaifi anan sune masu ilmin cikinmu wadanda bature yake cewa (elites).Tabbas mafin yawansu sun fitone dagacikinmu talakawa,to amma sun rikide sun zama munafukai,su ke hada bakin da makiyen domin su tabbata talakawa kansu bai haduba ta yadda za su gane waye makiyinsu.Kuma duk lokacin da suka so biyan bukatarsu,a tsakaninsu ba sa banbancewa waye dan talaka waye dan sarauta.Zaunawa suke kan teburi guda su tsarawa kansu yadda bukatarsu zata biya koda talaka zai mutu basu damuba.Inaga dalili kenan,bayan da talaka ya sha kaye azaben daya wuce,ya far musu batare da banbancewa wanene dan talaka wanene sarakiba.Saboda haka manya masu laifi, ba wasu bane illa MUNAFUKAI,kuma ana samunsu achikin masu ilmin da attajiran dama sarakunan.
Allah sarki talaka! yau an wayi gari kai ke cutar kanka da kanka.Me ya rage, baya ka sauya tunaninka, ka kuma dage ka ceto kanka daga matsalar daka shiga.Allah shi kyauta, ya sakawa masana irin su Dr tilde da alkhairi.
Jamilu y .jega
Mallam, ka yi susa inda take man 'kai'kayi. Allah Ya saka maka da alheriSa. Ya kuma kara maka basira. Allah Ya sa mu talakawa mu gane mu gyara kurenmu. Mu hada kawukanmu don mu cida arewa gaba. Tsinke daya dai bata shara, kai ko sun tattaru da yawa sai da madauri suke iya shara.
Almajirinka
Dr Abdullahi Ahmed Yusuf
Doktan Maza sarkin yakin mayaka! Allah ya saka da alheri. Ai da ba don ire irenka ba da tuni mun fi haka....lalecewa?
Irin haka dai. Ina ganin matsayinka ya kai na ka dinga daure wa martani marar dadi ta fuskar zuzzurfan tunani da kyakkyauwan nazari bisa ga abinda masharhanci ya ributa, ba kawai ka doge dole sai an karbi abinda kazo dashi ba dari bisa dari. Wannan tabiar sai tasa kaima mu saka ka cikin 'yan inna rididi.
Ina fatan zaka buga wannan don inga lalle ansamu chanji. Tunda nima na danyi bambadanci a farko da karshe.
Well done Sir!
SB Muazu
Ni, a fahimtata, halayenmu shine yake jawo mummunan halin da muke shiga. Allah yana baiwa al'umma shuwagabanni daidai dasune. Malamai masana ilmi,sai sun fadakar da al'umma, kuma su zamo abin koyi akan shugabanchi, sannan talaka zai gane amfanin ilmi da kuma shugabanchi nagari.
Assalamu Alaikum Dakta maganar ka dutsi, na ga Mallam Bashir bai fahimci in da aka nufa ba, amma zan bashi shawara ya koma ya kara karantawa. Allah yayi mana jagora
Post a Comment