A Facebook friend requested me to compose a poem recommending how he can live on Halal. This was my answer:
YAS’ALUNAKA
Ta Dr. Aliyu U. Tilde
1. Ina jama’a /ku zo ku mu/ gode Allah
Wa lau da akwai/ walau da rashi/ da yunwa.
Wa lau da akwai/ walau da rashi/ da yunwa.
2. Mu zam da yakin/ a zucci akwai/ Ta’ala
Ya na da sani/ ya na kuma ko/ ganewa.
Ya na da sani/ ya na kuma ko/ ganewa.
3. Abun da muke gaba daya ya gabata
Fa ba lamari da ba shi ga Mai Iyawa.
Fa ba lamari da ba shi ga Mai Iyawa.
4. Ya na da shirin abinci da rai na bayi
Ya na hidima cikin natsuwa ga kowa.
Ya na hidima cikin natsuwa ga kowa.
5. Cikin hikima ya ke tafiyar da kome
Da ba matsala da za ta fi warwarewa.
Da ba matsala da za ta fi warwarewa.
6. Da “kun fa ya kun” ya ke lamari a kullum
Cikin ilimi ya ke k’adari ga kowa.
Cikin ilimi ya ke k’adari ga kowa.
7. Akwai k’adara akwai sababi a gu nai
Biyun duka zo gare ni na bayyanawa.
Biyun duka zo gare ni na bayyanawa.
8. Ka san k’adara tana tafe ko da yaushe
Ka zam hakuri ga Mai Sama dogarawa.
Ka zam hakuri ga Mai Sama dogarawa.
9. Irin haka san fa nadiratan ka zowwa
Ka na iya mai da shi da’da jarrabawa..
Ka na iya mai da shi da’da jarrabawa..
10. Ka san lamari mafi adadi na bayi
A kan sababi yake tafe inda kowa.
A kan sababi yake tafe inda kowa.
11. Idan ya taho bak’in lamari da aya:
“Bi ma kasabat” a Fatiri bar musawa.
“Bi ma kasabat” a Fatiri bar musawa.
12. Ga mai cigiyar: ina-da-halal? Taho nan
Akwai lak’ani ya na tafe ba jimawa.
Akwai lak’ani ya na tafe ba jimawa.
13. Rike shi da kyau a kul ka bari ya kubce
Ka sam fatahi da ba wani tamtamawa.
Ka sam fatahi da ba wani tamtamawa.
14. Ina iya rantsuwa kuma ban da shakka
A kan lak’anin akwai jazaman ga kowa.
A kan lak’anin akwai jazaman ga kowa.
15. Cikin ladabi matso kusa zo ka zamna
A yanzu ka sam abin da ka ke bidowa.
A yanzu ka sam abin da ka ke bidowa.
16. Gaban likita ka zo da bidar dawa’i
Ka alkawari ka na da halin kulawa.
Ka alkawari ka na da halin kulawa.
17. Ya ce da Ali ba zan maka fariya ba
Bila fakhari ina da halin kulawa.
Bila fakhari ina da halin kulawa.
18. Ka san igiya guda haka: biu kacal ne
Suke tafiya su je su taho a baiwa.
Suke tafiya su je su taho a baiwa.
19. Ta fari ta na bido maka kulla hairi
Ta bin daga nan ta na ta bidar ragewa.
Ta bin daga nan ta na ta bidar ragewa.
20. Ka san wada za ka ja igiya ta hairi
Ya zan ka kware bila amadin iyawa.
Ya zan ka kware bila amadin iyawa.
21. Ka san kuma zaka sau igiya ta sharri
Ka bar duka bibiye mata ko kulawa.
Ka bar duka bibiye mata ko kulawa.
22. “K’adaf laha” can na bincika wanga sirri
Ya zam mafita gareni ina yabawa.
Ya zam mafita gareni ina yabawa.
23. Cikin darasi guda shida duk na khairi
Rike su da kyau shidan duka zan kidawa.
Rike su da kyau shidan duka zan kidawa.
24. Ka d’au adu’a ka d’au ilmin sana’a
A kan su biyu tsaya na daka kwarewa.
A kan su biyu tsaya na daka kwarewa.
25. To sai na ukun ka daukaka so ga himma
Idan ka nawa a take ka ke rasawa.
Idan ka nawa a take ka ke rasawa.
26. A kan na hudu ka zam marikin amana
Ta na da isa kamar mak’ata iyawa.
Ta na da isa kamar mak’ata iyawa.
27. Kudinka da tattali ka ke tanadinsu
Ka ce na biyar na ba ka ka zam kulawa.
Ka ce na biyar na ba ka ka zam kulawa.
28. To sai na shidansu zam rika ba da zakka
Idan ka biya ta na hab’aka rib’awa.
Idan ka biya ta na hab’aka rib’awa.
29. Idan ka musa ina maka d’an ishara
A Suratu Rum ka na iya fayyacewa.
A Suratu Rum ka na iya fayyacewa.
30. Ka ba da ita ta zam shukura ga Allah
Ta sam sanadin na “zid” haka tabbatarwa.
Ta sam sanadin na “zid” haka tabbatarwa.
31. Tsaya tukuna ina da kadan bayani
A kan su bakwai wadanda suke ragewa.
A kan su bakwai wadanda suke ragewa.
32. Ka san ko a kul ka aikata ko dayansu
Tsiya aguje tana tafe ba jimawa.
Tsiya aguje tana tafe ba jimawa.
33. Cikin taqawa ka bar dukanin kaba’ir
Da sakamako da za a biya gujewa.
Da sakamako da za a biya gujewa.
34. “Wa yarzuk’uhu” ta na a cikin Talak’i
Idan ka musa kana iya hallakewa.
Idan ka musa kana iya hallakewa.
35. Cikin su ka’ba’irai zina ta fi saurin
Taho da tsiya ta gatar mai iyawa.
Taho da tsiya ta gatar mai iyawa.
36. Gare ka gama musibatu za ta sabka
Saboda ka zan ka tuba da ba mayawa.
Saboda ka zan ka tuba da ba mayawa.
37. Idan kuwa shi ya so ka da hallakewa
Ka na bidiri ana ta dad’i tulawa.
Ka na bidiri ana ta dad’i tulawa.
38. Ka san halaka dare daya za ta zo ma
Ka na mutuwa ana maka azzabarwa.
Ka na mutuwa ana maka azzabarwa.
39. Akwai kuma cin gumin wasu masu hakki
Yana saka dukiya masakin zubewa.
Yana saka dukiya masakin zubewa.
40. Kiyayi hak’i cire shi walau bi zarrin
Wuta ka cire gabanin tallafewa.
Wuta ka cire gabanin tallafewa.
41. Ka bar rage kyau saboda ka samu riba
Tsiya takanas ga kha’inu ba jimawa.
Tsiya takanas ga kha’inu ba jimawa.
42. Da alfahari hakan na gano a Kahfi
Yana iya sa hanunka a tallafewa.
Yana iya sa hanunka a tallafewa.
43. Ka bar hasada saboda gudun a tsine
Ta na iya dakatar maka kyautatawa.
Ta na iya dakatar maka kyautatawa.
44. Guje duniya ka gane irin halinta
Tana rika bin wadanda suke gujewa.
Tana rika bin wadanda suke gujewa.
45. Idan ko kace da d’a’atu za ka bi ta
Ta ba ka tsana halinta halin budurwa.
Ta ba ka tsana halinta halin budurwa.
46. Ina adu’a ga masu bidar halal yau
Ka kai musu agajinka da ba gushewa.
Ka kai musu agajinka da ba gushewa.
47. Ka dubi Ali da duk ta’adin zunubbai
Ka ce masa je gaba daya ba tunawa.
Ka ce masa je gaba daya ba tunawa.
48. Jikan su uwa ka sa da uba a Janna
Ga Mustapha ko ka salli da sallamawa.
Ga Mustapha ko ka salli da sallamawa.
49. A nan na tike na ce ma ta “Yas’alunak”
Mafa’alatun mafa’alatun mayawa.
Mafa’alatun mafa’alatun mayawa.
Tammat bi hamdillah
18 March 2015
No comments:
Post a Comment