Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

WAKAR ILMI

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Dawil: ( v - - v - - - v - - v - - -)
1. Da sunansa zan fara \mutane ku saurara
Ina gargadi dangi \mu himma a kan ilmu.
2. Mu san ba ya shi ilmi\ a dunya a tun farko
Mu dau Adamun farko\ misali a kan ilmu.
3. Gamawar halitta tai \a kai kos a ilmantar
Da shi kan abubba duk\ ya zanto a kan ilmu.
4. “Wa allama Adamal asma”\ batu ne da ba karya
Ya na nan cikin Baqra\ idan ka bido ilmu.
5. Fiyayya a kan sauran \halittu da sun kasa
Da tabbas a kan cewa \mu zanto bid’ar ilmu.
6. Ka d’au ci da sha dukka\ku san su muhimmai ne
Wurin d’an Adam amma \ba sui martabar ilmu.
7. Idan ka yi jayayya \da ni sai ka saurara
Da hujja a K’ur’ani \a kan martabar ilmu.
8. Bisa ci da sha har ma\ mazauni masakinu
“Wa ya Adamus kun an\ta” bayan batun ilmu.
9. Mu karo “Kula min haithu shiituma” umarni ne
Fa sun zo ga Adam bal \a bayan batun ilmu.
10. Ka za ma shari’a duk \da karfinta ba musu
“Wala taqraba” ta zo \a bayan batun ilmu.
11. Masoya shari’ah sai \ku zamto kuna lura
Ku wo ci da sha ku wo\ mazauni a kan ilmu.
12. Idan ba ukun farko \ku san za a ja baya
Bare ko a ce tun can\ mutanenmu ba ilmu.
13. Ga ma ko azaba ba\ a yi nai a kan laifi
Idan ba shirin farko \sanarwa a kan ilmu.
14. Idan za ka yin komai\ nasihar da zan bayar
Ka tai inda gogaggu \a fannin bido ilmu.
15. Ka zam mai ladab gun\ kowane don ka amfana
Ka san “Fas’alu” aya \musamman a kan ilmu.
16. Gama ko a waka ce\ ka zam mai bidar haske
Wajen malaman adabi\ ka komai a kan ilmu.
17. Ka tai inda Bello dan\ Sa’id ka ji gogagge
Ka je inda Dangambo\ da Birniwa don ilmu.
18. Aruli su nuna ma\ ka san yadda tsarinta
Ya ke gunsu sai sauk\i da albarkacin ilmu.
19. Ina mai musu zo nan\ da hujja ga Danmama
A Sabbih akwai “Iqra\ bismi” a kan ilmu.
20. Umarni na farko wan\da Jibril ya saukewa
Muhammad ya zam hujja \azal kan bidar ilmu.
21. Hadisi “walau bis Sin”\ kaza ya yi umarni
A ko da kasar Sin ne\ muje don bidar ilmu.
22. Mu ilmi na dini har \da dunya bila haddin
Ado ne abun kauna\ ga kowa ka dau ilmu.
23. Ga yara mu san gata\ dawaman a nan dunya
Idan munka duba duk\ ba ya gatar bidar ilmu.
24. Da kurdi da mota har\ da dangi su na baya
Gida har da mata duk\ ba sa yin kamar ilmu.
25. Biyar din suna kauwa \su bar ka awa fanko
Da d’ai ba a yin canji\ wurin sahibin ilmu.
26. Iyaye ina rokon\ ku zam masu gaggawa
Wuya duk ku kai yaran\ku zauren bidar ilmu.
27. Izan za ku kwan yunwa\ ta na ci cikin hanji
Ku zam kunfi kaunarta \a kan sui rashin ilmu.
28. Fa ya Rabbi na roke ka \Sarkinmu mai ilmu
Ka nunan Arewarmu\ da yara maso ilmu.
29. Da safe suna samko \su kimtsa cikin sauri
Da salla su wanka tsab \su karya su tai ilmu.
30. Du’a’in da zan ke nan\ ga yaranmu har kullum
Mujibu ka karba mun \da albarkacin ilmu.
31. Su kai inda girma har \su gemu suna nema
Su dau rayuwa kanta \su dora ta kan ilmu.
32. Amana cikin zucci \da kauli kaza aiki
Su zam sun rike ta da kyau \muhimma ga mai ilmu.
33. Ku san ilmu bai komai \idan ba hali mai kyau
Hali ak k’asa, kai nai \ruwa ke zuba: ilmu!
34. Kasa in da kyau tabbas\ ruwa za ya amfanar
Idan ko da muni ba\bu tsaba wurin ilmu.
35. Hali bai zuwa siddan\ idan ba da horo ba
Mu kara da tarbiyya \ta yara a kan ilmu.
36. Su zam tsoron Ta’ala \a zucci zuwa aiki
Su himma su amfanar \mutanensu don ilmu.
37. Na dina, sana’a bin \su tara wajen horo
Su d’au d’ai kadai tabbbas\ ya na warware ilmu.
38. Fa ilmin sana’a d’ai \fasadi ya ke kaiwa
Ga assha da sata har\ da gillar marar ilmu.
39. Idan ko akai ilmi \na dina kad’ai dinsa
Da roko a kan k’are bayan bidar ilmu.
40. Bala’in da yas same\ mu yau ne irin wannan
Da boko awa dala, \a dina ko ba ilmu.
41. A ofis cire shakka \sana’arsu sata ce
Ta ya za a taqwa in\ a dina ba ai ilmu?
42. Akwai wanda sun ilmi\ na dina da ba nema
Dabi’arsu maula ce \da sun dakushe ilmu.
43. Mi tuubi karambani \ku yafeni har kullum
Ina ma a ce da na \yi himma a kan ilmu?
44. Jahala garen wallah\ da kwalwa marar komai
Fa ya Rabbi yafe mun\ mi mauni wala ilmu.
45. Dawil yau na sak’a baituka arba’in sitta
Fa’uulun mafaa’iilun \na waka a kan ilmu.
46. Salati a kan manzo \da duk sahibul qiblah
Jik’an duk iyayena \da albarkacin ilmu.
Tammat bi hamdillah!
14 March 2015

No comments: