Abut Tayyib Al-Mutanabbi ne ya taba cewa, "Duk tsayayye yakamata lokaci-lokaci ya rika tsanantawa wanda ya ke jinkansa."
Haka. Wannan post din nawa kila aga na tsananta a kanmu, mu Hausawa a jumlance, watau mutanen Arewacin-Arewacin Nijeriya da suke Musulmi galiban. To ba tsanani ba ne siddan. Soyayya ce matuka. Yau ka samu wanda zai maka fada bisa gaskiya ma gata ne.
A gaskiya muna da sauran aiki. Me ya sa akasarinmu mun gagara daukar rayuwa da muhimmanci ne, yaranmu da manyanmu? Kome a wulakance muke ganinsa ba ma iya hangen nesa bisa al'amurra har sai mun ga uwar bari? Me ya sa arziki zai zo mana har gida amma mu yi ta kokarin sai mun kore shi mun maye shi da tsiya? Me ya sa mu kadai muke da wannan halin, sauran abokan zamanmu ba su da shi? Ga misalai biyu.
Yaro ne za ka takura kanka ka yi mar duk kokarin duniyan nan saboda ya yi karatu rayuwarsa ta amfane shi amma galiban sai ka samu in Bahaushe ne sam ko a jikinsa. Muddin yana ganin a gidansu akwai wadata, shi ke nan, yana da wuya ya saurari duk bayanin ko fadan da za ka masa. Haka zai yi ta shiririta abin har sai haza ta kam masa. Zan ba da misali daya a nan.
A Khartoum watarana ina tsaye a gaban Nigeria House, sai na ji wani yaro yana waya da dan ajinsu yana tambayarsa wai ko an fara koyarwa a wannan simesta din don shi bai fara zuwa makaranta ba tukun, yana gararinsa ne a cikin gari. Sai abokin nasa ya ce masa ai yanzu ma za a fara test din farko... Ya ce test? Ai kafin ka ce kwabo ya kashe waya ya yi gabas a guje ya doshi makaranta.
Jama'a, menene wannan. Yanzu haka ya zo karatun ne da kudin al'umma ko na mahaifinsa duk a kokarin da ake ya zama mutum amma a banza... Shi kam ya gagara hango bala'in da ke jiransa in ya ki karatu. Dan Arewa. Ga yaranmu da kwakwalwa amma ba hangen nesa.
To ba shi kadai ba ne. Rabin yaranmu haka suke, musulminmu da kiristanmu amma halin ya fi muni cikin musulmi. Amma dan kudu, Inyamuri ko Bayarbe, musulmi ko kirista, sau da yawa za su ce maka in suka yi tunanin wahalar da iyayensu ke shiga don su sama musu kudin da za su yi karatu, sai su k'ara azama su ce ba za su iya dawowa gida su ce musu sun fadi jarrabawa ba. A gaskiya suna baaaaaani sha'awa.
Haka abin yake wajen manya a fannin sana'a. In ka samu Bahaushe bakanike ka fara hulda da shi, sau da yawa da kyar huldarku za ta jima. Akwai wanda a kan gyaran awa daya sai ya ajiye mota na kwanaki. Kuma duk da haka in aka dawo da motar sai ka iske gyaran a wulakance aka yi shi. Yana da wuya ka samu irin wannan halin a cikin kanikawa Yarbawa ko Inyamurai. Musamman Bayarbe, kana iya shekara 30 da shi yana maka gyara kuma cikin ladabi da sauki. Ina da Lati, laririnshan dina a Kwangila, Zaria. Yau shekaranmu 30 cif. Har ya tsufa. Musamman na ke ratsewa in masa kyauta. Malam Bahaushe kuwa sai lalaci, ba zai fito aiki ba sai karefe 11. Ga girman kai, ga zamba, ga wulakanci, ga tsada. Ba duka ba, amma da yawa.
Haka abin yake a sauran sana'o'in hannu, kama daga gini da walda, da sauransu.
Wannan zuunannar matsala ce tun fil azal. Ga abinda Saadu Zungur ya ce tun shekaru 60 da suka wuce:
"Kai Bahaushe ba ka da zuciya
Za ka sha kunya nan duniya."
Za ka sha kunya nan duniya."
Abin kamar a al'adarmu ya bijiro tunda ya zama gadadde. Ko menene, Allahu aalamu.
A karshe ina addu'a Allah ya karawa masu himma a sana'arsu arziki da taimako. Yaranmu masu himma Allah ka kara musu albarka. Wadanda kuma suke da wannan gazawa cikin dalibanmu Allah ka sa su fahimta, su gyara halinsu, su daina ganawa iyayensu azabar bakin ciki, su fuskanci rayuwa da duk muhimmancin da ya kamata. Hakaza, masu sana'a da ke wasa da ita, Allah ka sa su gane cewa arziki ya fi tsiya, kuma da himma da kwarewa da gaskiya da tattali da ladabi kawai arzikin yake zuwa ba da lalaci da zamba da girman kai ba.
Amma har yanzu tambaya ita ce: me ya sa halin ko oho ya fi yawa a tsakaninmu Hausawa?
Dr. Aliyu U. Tilde
3/10/2015
3/10/2015
No comments:
Post a Comment