Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

ALLAH KA BA MU ZAMAN LAFIYA

1. Ta’ala kadiri kaban lafiya
In rera waken zaman lafiya.
2. Ka ba ni hazaka har da fasaha
Gurin rera wakar zaman lafiya.
3. Tsira aminci su tabbata gun
Muhammadu manzon zaman lafiya.
4. Ba shi kadai ba har da sahabbai
Da aluh da matansa baki daya.
5. Ya bar wasiyya ga umma tasa
Su zanka shiri don zaman lafiya.
6. Ya zo da sako na jalla garemu
Islam nufinsa zaman lafiya.
7. Jigo biyar ne inji Muhamman
Biyo ni ka ji su ga baki daya.
8. Farkonsu Kalmar Shahada ka gane
Biyayya ga Allah zaman lafiya.
9. Yarda da sakon Muhammadu shi ma
Ya na kai ga turbar zaman lafiya.
10. Na biyyunsu sallah na khamsu biyar ne
Da ba su yuwa sai akwai lafiya.
11. Ga Ramalana mu zan azuminsa
Kaza ba da zakka zaman lafiya.
12. Cikonnasu Hajji ka je in da hali
Guzuri da hanyarka mai lafiya.
13. Sahabi ya ce ya Rasulu gaya mun
Zan sam sawaba zaman lafiya?
14. In na rike su biyar babu kari?
Manzo ya ce har ka zam lafiya.
15. A gobe kiyama a saka a Jannah
Nan ne tikewar zaman lafiya.
16. Tayaya musulmi a yau sunka baude
Wa horo na manzon zaman lafiya?
17. Su kafirta bayi da Kalmar shahada
Suna rushe sakon zaman lafiya.
18. Wasunsu gama har makamai garesu
Gilla suke ba zaman lafiya.
19. A Yerwa da Bama da Baga da Gwoza
Banki, Chibok ba zaman lafiya.
20. Su kan harbe mata da yara da tsofi
Samari su sace su baki daya.
21. Su kan sace mata da ba su da aure
Su auresu karhan suna fariya.
22. Su je makaranta su kona ta kurmus
Da yara cikinta ga baki daya.
23. Su ce musu arna da Kalmar Shahada
A baki, su fille su ba yafiya.
24. Boko Haramunga sun mana illa
Sun ci amanar zaman lafiya.
25. Sun watse birni kaza har da kauye
Kowa ta kai nai yake tafiya.
26. Iyali su watse da dangi hakan nan
Kowa a firgice sai tafiya.
27. Da muggan d’iya cikin namu soja
Ba su da niyyar zaman lafiya.
28. A kauye birane misalin su Baga
Sun yi ta gilla gabaki daya.
29. Sun kashe yara, sun kona mata
Sun kauda dadin zaman lafiya.
30. Ta’ala mashiryi ga ni gareka
Ina zanka rokon zaman lafiya.
31. Gare ni da ‘ya’ya da mata dukkanmu
Da dangi abokai ga baki daya.
32. Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu
Hada mu zumuncin zaman lafiya.
33. Dademu fahimta ta juna mu gane
Cikin arziki ba kamar lafiya.
34. Fitinnu na baya kaza na zamanu
Ka kare mu Jalla mu zam lafiya.
35. Mu rungumi ilmu na Dini da dunya
Cigaba rizku don zaman lafiya.
36. Dademu da tsoronka ya Jalla Sarki
Domin Muhamman mijin Mariya.
37. Ba mu kadai ba har da Boko Haramun
Yaranmu shirye su baki daya.
38. Kanne da yayu cikinsu gaba dai
Maido su hanyar zaman lafiya.
39. Ka yafe su laifinsu komai yawansa
Bayinka ne Rabbu mai lafiya.
40. Idan ka tsanesu Allah Gafuru
Waye garesu ko a nan duniya?
41. Ka nunan da raina ina sintiri
Da nono a Yerwa zaman lafiya.
42. In je ni Bama in mika caffa
Gidan Mbusube Baba mai gaskiya.
43. Rabbi ka kaini Gwoza in gansu
Mutane na kirkin zaman lafiya.
44. Askira, Uba, Michika in je
Kasashe na Margi mutan lafiya.
45. In shiga Maiha da Mubi in gansu
In ba su Wakar Zaman Lafiya.
46. In zo ni Gombi in shiga Hong
Har ma da Song don zaman lafiya.
47. Ku bar ni in zarce wajen Yola dangi
Filani na Lamido mai gaskiya.
48. In kwan salati in je ga Inna
Da "Intel" da dukkan maso lafiya.
49. Nuhu Ribadu aboki amini
Ina mika caffa ga mai gaskiya.
50. Da safe in je ni school in ganesu
Teachers na ilmu cikin lafiya.
51. Ga yara da manya musamman ga mata
Ci gaba za mui ga baki daya.
52. In shiga mota in kama hanya
Zuwa Ganye gun su mutan lafiya.
53. In je ni in gana da danginmu Chamba
Da sarkinsu Gamwari Mai gaskiya.
54. In zo ni Numan, na sheke ayata
Baki na Benue zaman lafiya.
55. Timawus Mathias in ganai har ya kaini
Gurin nasa gwarzon zaman lafiya.
56. Sarkin ‘Bata in yi chaffa gareshi
In fadi gu nasa mai gaskiya.
57. Lamurde zan sayi kifi gasasshe
Na cinye a mota zaman lafiya.
58. Ga Tula sun zo da tarba gareni
Suna so in rera Zaman Lafiya.
59. Kaltungo, Billiri har ma da Kumo
Ku tashi ku mike zaman lafiya.
60. Ku wo dandazon sallama don in ganku
Ku ba ni aron kunnuwan lafiya.
61. Ku kore su Sheidan ku zan yin zumunci
Ku zauna ku mike cikin lafiya.
62. Zan shiga Kumo domin in gan shi
Muhammadu Kumo ka na lafiya?
63. In ba su loto da baya tsawaita
Domin in zarce garin gaskiya.
64. Gombe ta Buba in sadu da dangi
Hausa da Fulbe gaba ki daya.
65. In shiga Makay in yi sayayya
In mika katina don in biya.
66. SanHusein da Samaha sai na shige su
In kara sayayya, zaman lafiya.
67. Idan sun ka ce Ya Aliyu ka kwana
In ce musu a’a cikin dariya
68. Zan Kwana Bauchi da ikonsa Allah
Ta Yakubu garun zaman lafiya.
69. In isa gu nasa Sarkin garinmu
In fadi domin zaman lafiya.
70. In fita fadar ina takama
Na zo gida kana ga lafiya.
71. In je gari in ga Tahir aboki
Muhamman Madaminmu mai gaskiya.
72. In nemi Habuna, sadiqi na Mamman
Muhimmi gareni wajen tafiya.
73. Ahmad Nadani ina zan ganeka
Ka ba ni shauki cikin zuciya.
74. Yan kasuwan Bauchi caffa gareku
Ku zauna da himmar zaman lafiya.
75. Ku sai mun da nono idan na taho
Ku zan yin raha don zaman lafiya.
76. In na ga dama in je buga kwallo
Wasanmu Golf ba ya shi ka jiya?
77. Safiya ta bani abinci dafaffe
Da ‘ya’yan itace tana dariya.
78. In kwana a gunta cikin so da kauna
Ta’ala ka barmu gabaki daya.
79. Da sassafe in tashi in nufi Tilde
Ba ni da haufi cikin tafiya.
80. In isa Toro ga Katuka Sarki
Na samai da dangi cikin lafiya.
81. Ina yanuwana na Tilde ku zo
Kuna nan da shauki ku na tambaya.
82. Wata ukku daidai babu Aliyu
Cuso na Nana maso lafiya.
83. Yaro na Fatima har ma da Umma
Ga Luba can sun zaman lafiya.
84. Na je can gidanmu in gaida Iro
Barhama Ghandinmu mai gaskiya.
85. In je kufayi in yi salati
Ziyara ga manya gidan gaskiya.
86. In zo ni Zango in tadda ‘ya’ya
Da mata da dangi suna lafiya.
87. In yi sujuda in gode Allah
Ta’ala ka zaunar da mu lafiya.
88. Najeriyarmu gaba d'ai Africa
Ka bamu rabo da zaman lafiya.
89. Arewarmu Allah ka k'areta ilmu
Sana’a amana da son gaskiya.
90. Yaranmu Allah ka shiryesu Hadi
A hanya tsayayya su so gaskiya.
91. Manyanmu kau rabbi k’aresu tausai
Na yara, talakka da son mabiya.
92. Ka kore mugunta cikin zuciyarsu
Mayeta da hubbi ga baki daya.
93. Tammat fa waka a nan zan aje ta
Ta cika baiti dari ba daya.
94. Mai tambaya za ya ce wa ya yi ta
Zan baka amsa xikin gaskiya.
95. Cene Aliyu na Tilde ya yi ta
Dan Usmanu mazajen jiya.
96. A karshe kirana ga Allah fiyayye
Ta’ala ka tsarshe ni aikin riya.
97. Ka karbi ibadunmu Rabbi Shakuru
Ka karemu Sarkin zaman lafiya.
98. Iyaye jik'an su ka sa su a Janna
Da alkausara gun zaman lafiya.
99. Ka kara salati bisa Annabinmu
Muhammadu manzon zaman lafiya.
Tammat.
25 Nuwamba 2014

No comments: