Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

Anya Mun Waye Kuwa?

Daga cikin dabi'ar dabbobi shi ne fada (aggression) da bako idan ya shigo garkensu. Bakuwar saniya kullum sai ta baka tausayi saboda wahalar da za ta sha kafin sauran shanu su karbe ta.
Masana ilmin rayuwar mutanen da sun tabbatar cewa mutanen farko na saurin kashe baki da wuyan yarda da su. Wannan hali har yanzu na cikin jinin wasu kabilu a kasashen duniya dabam dabam, ciki har da Nijeriya. Wannan shi ne tushen da'awar Donald Trump a Amurka.
Hakanan idan aka debi sabbin sojoji kurata ko sabbin dalibai a makarantun kwana, ana samun matsala sosai ta cin zalinsu kafin su samu karbuwa a hannun sauran dalibai.
A takaice rashin karbar bako da martaba shi hali ne na dabbobi da rashin wayewa. Don haka, yana daga cikin ma'aunin da ake amfani da shi a ilmin zamantakewa don gane ci gaban alumma da wayewar mutum. Sauran ma'aunan sun hada da yadda ake martaba masu rauni a al'umma kamar mata, yara, da tsirarun kabilu ko akidu.
A nan dole mutum ya sarawa musulunci da kuma manzonsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya yi bayanai da yawa a kan girmama bako. Ya ce, "wanda ya girmama bakon da ya sani kamar ya girmama ni ne; wanda kuma ya girmama bakon da bai sani ba kamar ya girmama Allah madaukaki ne."
Haka muka tashi muka samu iyayenmu suna yi, wadanda ba su yi ilmin bokon turanci ko bokon arabiyya ba. In bako ya zo an yi ta gaisuwa ke nan ba iyaka: marabba, marabba, marabba...ba karewa. Sannan a shiga tambayar iyali, dabbobi, yara, kowa sai an kira sunansa. Sannan a shiga kiran dangi dabam dabam. Daga nan za a shiga gida a kawo ruwa a mika kafin abinci ya nuna, dss.
Wannan tarbiyyar ita ta sa a kasar Hausa, a da, ko otel babu. Duk inda dare ya yi wa bako sai ya yi sallama, za a sauke shi, ya ci ya sha har ranar da zai tafi.
Sai dai kash! Albasa ba ta yi halin ruwa ba. Karif dinmu, mun kasa rike wannan muhimmiyar tabi'a. Bako in ba mai maiko ba ne, to ba abin kulawa ba ne a gurinmu . Da farko, kallon banza ake maka sai ka ce kai ne wane kafin a fara maraba da kai.
Ko a waya haka muke. In ba mu san lamba ba, ba ma kulawa. In ma mun amsa wayar, sai mu yi da wata murya marar dadi kamar an matsa mana ne. Sati biyar da suka wife na tafka irin wannan ta'asar. Gwamnan jaharmu ne ya kira ni don yana son ganawa da ni. Da ya bugo sai na amsa da, "yauwa, barka", a kan ban san lambar ba. Sai ya ce, "Dr. Sunana Barrister M.A. Abubakar." Kan ka ce kwabo, Dr. ya tashi ya zauna, ya canza murya: "Ah. Your Excellency. Barka sir. Ina wuni sir. Ina gajiya sir..." Ka ji fa!
Haka abin yake hatta a tsarin ma'aikatunmu. Ba a damu da bako ba ko lafiyar dukiyarsa. A ma'aikatu, da kyar za ka ga an yi wa baki wajen ajiye motocinsu, misali; sai dai bako ya san yadda zai yi. In ya ga guri ya paka, sai ka ji an ce mar Malam ba a pakin a nan. To ina zan paka? In ka ci sa'a, sai a nuna maka wani wuri can gefe, mai tabo da ramuka da zafin rana, ba tsaro a gun ba komai. Komi ya faru da motar ma ba ruwansu.
Haka na gani a JUTH yanzu. Ga wuraren parking kala kala duk da kwalta. Amma na baki na can, daga wajen sai daji, sharrare, da ramuka kuma kukanka banza.
Ba a Jos ba kadai. Na sha zuwa Jami'ar Bayero a mazauninta na dindindin. Wajen pakin din baki wani wuri ne mafi muni a site din, mai yawan laka da ramuka a mashiginsa, marar kwalta, marar tsaro. Kano kuma a jami'a matattaran ilmi. Wallahi ka ce an yi tirenin security dinsu ne don su ci zarafin baki. Balle kuma uwa uba, A. B. U. Zaria. Akwai abokina pharmacist, marigayi, da security suka taba kulle shi siddan lokacin Kwantagora. Tir!
Irin wadannan abubuwa suna ba ni mamaki har sukan sa in ce: anya karatun nan namu yana gaya mana gaskiya ko kuwa son kai kawai mu ke koya? Wanda ko bako ya kasa girmamawa, ina zai tuna da talakan da bai gan shi ba har ya ji tausayinsa a kan lamarin mulki?
Da sakel in muna son gaskiya. Ga mu da saurin kawo sunna a baki amma ayyukanmu sun fi komi nisa da sunna, yanbokon turanci da yanbokon arabiyya duk sawa'un.
Anya mun waye kuwa?
Ku dai na bayanmu kar ku yi koyi da mu. Allah sa da raina in ga Allah ya ba ku mulki kuna girmama baki kamar yadda gadonmu da addininmu suka nuna mana. Da na yi murna matuka. Allah sa in kun zame VC, misali, ku yi fankamemen wajen pakin a jami'arku, da katon dakin karbar baki inda za ku sa firji manya manya masu ruwan sanyi don baki, da AC na busa musu iska yayin da ake karbarsu, da kun raya sunnar Annabi (SAW).
Mu kam tamu ta kare. Mun ci dubu sai ceto. An yi karatu amma ba a waye ba.

Dr. Aliyu U. Tilde
6 April, 2016

No comments: