Shekaranjiya na dau hotunan nan guda uku a wani kauye kusa da Pambegua. Ina kaunar wannan wuri tun sama da shekara talatin don kusan a nan ne na fara ganin ciyawar shanu. Kuma kullum na iso wurin daga Kaduna, na san na iso Pambegua.
Yau an yi shekaru wurin ya ragargaje. Duk gine-ginen, banda ginin ofis da ke gaba, ko jinka ba su da shi. Wasu ma hatta windojin an sace. Ciyawa kuwa, Allah ya jikanta. Ta mutu tun shekara ashirin ko fiye. Babu ita, sai dai tohonta. Ba dan adam sai wani mai gadi guda da na hanga yana kwance a kofar ofis din da tsakar rana.
Wannan cibiyar raya ayyukan dabbobi ba ita kadai ce ta lalace ba a cibiyoyi da ma'aikatun bunkasa ayyukan gona a kasar nan.
Nan kusa da ni, a Nabordo, da, akwai ADP zonal headquarters, wanda har da filin saukar karamin jirgin sama, da dam mai girma sosai, da gidajen ma'aikata kamar a Turai, da yanayi mai dadi, da workshops kala kala, da store iri iri makil da taki da iri da maganin feshi, da tarakta an fi a kirga, da ma'aikata na kaiwa da komowa. Wallahi abin ban sha'awa muna dalibai da sabbin ma'aikata a lokacin.
A yau wannan wurin ya zama abin tausayi. Komi ya rushe an masa warwas, kamar na Pambegua. Kusan ba kowa kuma ba komi, in banda hana rantsuwa. Sauran tagwaye biyu irinta suma duk fayau ne. Hawaye su ne amsar zuciya duk lokacin da ka shige su.
A Gubi, kilomita goma bayan garin Bauchi, akwai gonar shanun nono da masana'antarsa da aka gina a 1970s. Filin noman ciyawa kawai hekta (kamar filin kwallo) 800 ne. An fi shekara 20 ko hekta daya ta ciyawa ba a nomawa a gun, ko lita daya na nono ba a sayarwa. Shanu kuwa tun lokacin sojoji aka sace su, wasu cuta ta rabke... Akwai irin wannan ma'aikatar a Galambi, da Darazo da Azare. Duk ba ko daya na mora. Komai ya lalace ko an sace.
Yau in na wuce Maigana, ko Funtua, ko Kankia, takaici yana ci mun rai. Haka in na wuce Gusau, Miyanci, Bakalori balle kuma uwa uba, SRRBDA, ta Sakkwato. A dam din Bakalori ko lita daya ba a turawa, ko kadada daya ba a nomawa. A helkwatar Cibiyar Raya Kogin Rima (SRRBDA) kuwa, banda tsagaggun gine-gine ba abin da kake hanga.
Haka dai haka dai. Larbarin aikin noma da kiwo ya zama tarihi a duk Arewa. Ya mutu. An binne shi...Allah ya jikansa.
Ina gwamnatocin jihohinmu da ke alkawarin raya akin gona? Wadannan wurare wallahi shaida ne a kanku. In har mulkinku ya kare ba tare da raya wadannan wurare ba, wadanda mallakarku ne, to ku sani kun fadi warwas!
Haka Gwamnatin Tarayya. Aikin da za ta yi a fannin gona a zayyane ya ke tun ran farko. Ta raya abinda ta tarar, ta inganta na raye, kafin ta yi tunanin sabo. Wallahi ba abinda Shugabannin baya tsakanin 1950 da 1983 ba su tanada ba a fannin noma da kiwo. Sojoji ne suka zo suka lalata su, kuma yau shekara 16 'yan siyasa sun kasa raya su, in ka debe gwamnatin jahar Kano. Ko su aka dawo da su, za a samu aikin yi mai yawa.
PMB ka tasamma raya hukumomin raya kogunan Rima, Hadejia, Tafkin Chadi, Benue ta Sama, Benue ta Kasa, da Kwara ka ga in za a samu matasa marasa aikin yi... Su ma gwamnonin APC su yi haka a jahohinsu. Kan a ce kwabo kowa zai murmusa. Talauci mai jawo hassada da yawan korafi zai rasa wajen zama.
Ku tashi tsaye, kafin lokaci ya kure. In 2019 ta zo sannan cibiyoyin aikin gona da kiwo na Pambegua, Nabordo, Gubi, Galambi, Maigana, Funtua, Kankia, Gusau da Rima duk suna nan kamar yadda suke a yau, ku sani haka bata cimma ruwa ba...
No comments:
Post a Comment