Na Dr. Aliyu U. Tilde
Bayan kammala zaɓen 2011 ba da jimawa ba na ziyarci wani babban aminina, Abba Bello Ingawa, a Kaduna, na iske shi cikin baƙin ciki da takaici. A lokacin, Jamhuriyar Nijer, maƙwabciyarmu kuma ƙasarmu ta biyu, ta gudanar da zaɓe mai inganci har an ce Muhammadu Yusuf ne ya yi nasara. Wannan abu ya burgemu, yayin da muke cikin takaicin tafka maguɗi a namu zaɓen wanda aka ƙare ba da jimawa ba a lokacin. Nan ne Malam Abba ya rantse ya ce mun, “Sheik, wallahi, na gwammace a ce ni ɗan Nijer ne.”
Takaicin aminina Abba ya bijiro ne daga daɓi’ar ɗan adam na ƙin zalunci, don zalunci na tilasta masa yanke ƙauna da daƙile duk wata kafar alheri, alhali adalci na buɗa masa kykkyawan zato na kyautatuwar rayuwa da sakamako nagari. Ga mutum irin Abba, wanda yana cikin manyan ‘yanboko masu zaman kansu a ƙasan nan, da ya zauna a ƙasa mai arziki inda yake gudanar da ayyukan samun kuɗi a ilmance na miliyoyin naira duk shekara, da ƙaton gida a Kaduna, da iyali abin sha’awa masu karatu da rayuwa cikin ni’ima, ya gwammace a ce a Nijer yake, duk da cewa Nijer ba ta da tattalin arziƙi mai ƙarfi kamar Nijeriya kuma ba za ta ba shi ni’imar duniya kamar yadda Nijeriya take ba shi ba.
Gun ɗan halal irin Abba, mutunci ya fi komai. Kuma ina mutunci in wasu za su yi amfani da hukuma su yi ta tafka ɓarna a bayan ƙasa, su maida jama’a bayinsu, kuma su hana musu ƴancin zaɓen da zai sauya rayuwarsu zuwa mafi inganci? Ga mutum wanda yake da abin hannunsa irin Abba, ba mutunci a nan. Don haka ban ɓata lokaci ba, na amsawa wa Abba da cewa, “wallahi, ni ma haka. Ina ma da ɗan Nijer ne nima?”
Haka muka zauna shekaru a Nijeriya muna kwaɗayin rayuwar wasu maƙwabtanmu kamar Ghana da Nijer musamman don ganin suna zaɓe nagari kuma akwai wanzuwar doka da oda a cikinsu. Kuma ba mu kaɗai ba, duk Afirka na takaicin yadda Nijeriya, wacce suke ganin uwa ce ba-da-mama ga dukkan nahiyar da baƙaƙen fata a duniya, ta kasa ƴantar da kanta daga miyagun ƴaƴanta, baƙaƙen azzalumai, na tsawon shekaru masu yawa har mutuncinta ya zube a idon duniya. Takaicin da marigayi Nelson Mandela ya gayawa yayana Hakim Baba Ahmed ke nan lokacin da ya kai masa ziyara gidansa a 1998.
To, ashe muna namu Allah na nasa. Sai zaɓen 2015 ya zo da babban sauyi. Allah ya haɗa kan akasarin mutanen ƙasa kan cewa dole a samu canji musamman saboda lalacewar lamurran tsaro a Arewa-maso-gabas wanda rikicinsa yake neman hallaka ƙasar baki ɗaya. Zaluncin ya kai intaha. An yi addu’a Allah ya karɓa. Sai ya kawo mana fasahar zaɓe a inda aka inganta rijista kuma aka fara amfani da na’ura wajen tantance masu jefa ƙuri’a, ba tare da jam’iyya mai mulki ta ankara da haɗarin da ingantaccen kundin da na’urar za su jawo ba wajen hana maguɗi ba. Hakaza, aka samu ittifaƙin manyan ƙasashen duniya – musamman kanwa uwar gami, ko an ƙi ki sai an yi da ke, Amurka – kan cewa canji ya zama wajibi a Nijeriya. Allah kuma ya kau da duk banbance-banbance na siyasa, ƙabilanci da addini a zukatan mutane da yawa suka azuma kan goyawa gaskiya baya.
Tun kafin zaɓe ƴar manuniya ta nuna cewa za a samu canjin jam’iyya wajen mulki. A ƙarshe aka yi zaɓen aka canza daga jam’iyyar PDP zuwa APC, canji irinsa na farko tunda aka samu mulkin kai shekaru hamsin da biyar da suka wuce. Allah Madaukaki shi ya mana wannan gatan. Muna kuma godiya gare shi. Ya sa muma za mu ɗanɗana halawar zaɓe nagari irin wanda Nijer da Ghana suke yi a baya.
Albarkacin wannan zaɓen da sanin halin wanda aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa, martabar Nijeriya ta dawo a idon duniya har ta kai ƴan ƙasashen Ghana da Nijer suna fata hukumominsu za su inganta zaɓensu ya kai matsayin na Nijeriya. Har yanzu ana rikicin inganta kundin masu jefa ƙuri’a a ƙasashen biyu. A Ghana ana kukan tsohon kundin na ɗauke da sunayen ƴan ƙasashen waje da yara ƙanana. A Nijer kuwa har sai da ta kai jam’iyyun hamayya sun kai ƙarar gwamnati wajen Ƙungiyar Ƙasashen Renon Faransa kan rashin ingancin kundin zaɓe da wasu abubuwa da suke ganin ƙofofi ne na maguɗi da jam’iyya mai mulki ke son amfani da su wajen murɗe zaɓe mai zuwa. Ƙungiyar ta aiko da masu bincike kuma sun gano tabbas akwai mazaɓu na boge da sunaye masu yawa na waɗanda ba su cancanta su yi zaɓe ba.
Mu yau a Nijeriya mun zama misali ga sauran Afirka, kuma abin yabo da jinjinawa. Don haka da na ziyarci abokina Abba a Kaduna kwanakin baya, mun yi hira mai tsawo wacce a ciki muka nuna murnarmu da yanda Allah ya kawo canji a al’amurran zaɓe sannan muka yi ta tababan ko ƴan Nijeriya – masu mulkinsu da mu mabiya – za mu dace wajen yin abin da ya kamata wajen haɓaka tattalin arziki da sauran fannunnuka na rayuwa. Amma duk da ƙalubalen da ya rage, ba wata tantama cewa a yau muna shirye mu amsa sunanmu na ƴan Nijeriya da babbar murya a ko’ina ne.
Nijeriya tana da dama ta ci gaba da inganta sunanta a idon duniya ta hanyar tabbatar da anci gaba da inganta hanyar zaɓe da kuma an yi mulki mai adalci wanda ba cin hanci, zalunci ko jahilci a cikinsa. Ina murna ganin INEC tana ta ƙara jefa fasahar zamani a cikin harkarta, bata tsaya wuri daya ba don jin kirarin da ake mata. Ta cira gaba daga inda take a Fabrairun 2015. Da aka yi zaɓen jahar Kogi, INEC ta ce a helkwatarta ta Abuja ma tana da fasahar da take sanin ƙuri’un da ake tattarawa a mazaɓu a mataki dabam dabam tun kafin a kawo mata rahoto daga jaha. Kaga ke nan, batun canza sakamakon zaɓe bayan an bayyana shi a mazaɓa ko ƙaramar hukuma ko jaha ya tashi har abada a Nijeriya.
Gaba dai, gaba dai, ƙasata Nijeriya! Ina miki wasiyya da abu biyu, ki riƙe su kam kar ki yi wasa da su: doka da fasahar zamani, kamar yadda na ce a waƙar Card Reader bayan kammala zaɓen bara. Waɗannan biyun su ke mai da ɗan Adam ɗan ƙasa ingantacce a maimakon dabba. Doka ita za ta hana ko ta bari a yi abu; fasaha – watau technology – shi kuwa shi ne zai ba da damar yin abin ta hanya mafi inganci a wannan zamanin.
Ina fata da raina, kamar yadda na sha faɗa, rana za ta zo wacce a cikinta za mu ga ana amfani da zaɓen na’ura – watau electronic voting – a Nijeriya. Ƙila a lokacin, ni da Abbana muna da sauran ƙarfinmu; kila kuma mun gama tsufa amma dai za mu bar duniya cikin mutunci da fata nagari ga na bayanmu.
A ƙarshe, zan so in gutsurowa mai karatu wasu baitoci inda na waƙe wannan fatar a waƙata ta Card Reader:
Yardar Allah ta tabbata
Wa zai ce yau wai ya ƙiya?
Wa zai ce yau wai ya ƙiya?
Duk mai hairi murna yake
Ƙarya ta bar Nijeriya.
Ƙarya ta bar Nijeriya.
Wannan baiwa wa zai mana
Ce ne Allah Sarki ɗaya.
Ce ne Allah Sarki ɗaya.
Card Reader yac ce: zan sabab
Tafiya sak ba wata laulaya.
Tafiya sak ba wata laulaya.
Wannan hanya farko a kai
Rahmanu ka ƙaro gaskiya.
Rahmanu ka ƙaro gaskiya.
Nuna mana rana mai zuwa
E-voting za mui lafiya.
E-voting za mui lafiya.
Ranar shiyya ta mutan gabas
Da Taraba za su yi gaskiya.
Da Taraba za su yi gaskiya.
Ba sauran tashin hankali
Zaɓe za ai gangariya.
Zaɓe za ai gangariya.
In ba an kai wannan gaɓar
INEC kar ma tai dariya.
INEC kar ma tai dariya.
Wannan wa’azi ne ƙanƙani
Duk mai mulki ya yi gaskiya.
Duk mai mulki ya yi gaskiya.
Yai adalci yai ayyuka
Kowa ya riƙe ba wariya.
Kowa ya riƙe ba wariya.
Da mutunci bayan rayuka
Zai kare har ma dukiya.
Zai kare har ma dukiya.
Cin hanci har sata duka
Ya kashe ba a sharholiya.
Ya kashe ba a sharholiya.
Bai cin haƙƙin mu Ƴan Adam
Balle ko a ce yai danniya.
Balle ko a ce yai danniya.
Samun kowa zai haɓɓaka
Mui walawa mui kwalliya.
Mui walawa mui kwalliya.
Har in mun je mu balaguro
An zo da kammanin zolaya:
An zo da kammanin zolaya:
Wai kai bawa waye kake?
Mu bugun ƙirji mui fariya:
Mu bugun ƙirji mui fariya:
Kalle ni da kyau Mr. Man
Sunana ɗan Nijeriya.
Sunana ɗan Nijeriya.
Rannar giwa za tai tsaye
Mama ga dukan Ifrikiya.
Mama ga dukan Ifrikiya.
In ko an ƙi wa’azinmu kau
Rana na nan za ai biya.
Rana na nan za ai biya.
Twenty-nineteen na nan zuwa
Card Reader za tai gaskiya.
Card Reader za tai gaskiya.
Duk zalunci zai sha ƙasa
Tamkar wada yash sha can jiya.
Tamkar wada yash sha can jiya.
Sai kui himma kui hankali
Kui aiki duk kui gaskiya.
Kui aiki duk kui gaskiya.
Yayin ba kwa wani fargaba
Talakawa bi ba tambaya.
Talakawa bi ba tambaya.
Ni kam Tilde nai gargadi
Na ja muku kunne kun jiya.
Na ja muku kunne kun jiya.
Ƙarshe Allah nai addu’a
Ya daɗemu fasahar gaskiya.
Ya daɗemu fasahar gaskiya.
Na’ura duk mai fa’ida
Kawo ta ƙasar Nijeriya.
Kawo ta ƙasar Nijeriya.
Dokar zaɓe ita ma haka
Sanya a yi gyara bai ɗaya.
Sanya a yi gyara bai ɗaya.
Doka da fasaha tun a da
Su ke saka bawa gaskiya.
Su ke saka bawa gaskiya.
In ba su ai ba ɗan Adam
Sai dabba mai ƙin gaskiya.
Sai dabba mai ƙin gaskiya.
Tsira Allah har sallama
Kai wa Manzon duk duniya.
Kai wa Manzon duk duniya.
Sannan ka jiƙan bayi duka
Yafe mana Ranar Gaskiya.
Yafe mana Ranar Gaskiya.
Ka daɗo haske gun rayuwa
Mui walawa mui dariya.
Mui walawa mui dariya.
Card Reader ko ƙaro mata
Albarka don tai gaskiya.
Albarka don tai gaskiya.
Har in za ai zaɓe gaba
E-voting za mui bai ɗaya.
E-voting za mui bai ɗaya.
Warkar Card Reader ta cika
Allah Sarki nai godiya.
Allah Sarki nai godiya.
5 Janairu, 2016
No comments:
Post a Comment