Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

ALLAH DAYA

Ta
Dr. Aliyu U. Tilde
____________________
Mizani: Mutakarib
____________________
1. Bismillah da sunan
Sa sarkinmu Allah
Da yai yo mu bayin
Sa Allah daya.
2. Tsira har da sala-
Ma dora su kansa
Muhammadu bawan
Ka Allah daya.
3. Sunayensa Asma’-
U Su zan wa wake
Da sunanta wakar
Sa “Allah Daya.”
4. San Allahu shi ne
Ko sunansa babba
Sauran ko sifofin
Sa Allah daya.
5. Al’awwal na farko ga-
banin Halitta
Al’akhir na bayan-
Ta Allah Daya
6. Da ba ko halitta
Ga tun can da fari
Al-Mubdi’ ya fara
Ta Allah daya.
7. Al-Khaliq yai halit-
Ta, ba kwaikwayawa
Al-Bari’u sunan
Sa Allah daya.
8. Hakaza ka duba
Man sammai da kassai
Albadi’ mak'irin
Su Allah daya.
9. Hado mun da kome
Ne yaz zam yana nan
Al-waajid ya samas
Shi Allah daya.
10. Siffofi na bayin
Sa ya sauwara Al-
Musauwir ga daman
Sa Allah daya.
11. Duk mai ji da mulki
Ya na kas da Allah
Madaukaki Al-A-
Liy Allah daya.
12. Duk hali na bayin
Sa ya zarce wannan
Shi ne Al-Muta’aa-
Li Allah daya.
13. Kai Komai da ke ra-
Ye kab zai macewa
Al-Hayyu da rayin
Sa Allah daya.
14. Masu ji da girma
Ko sai durkusawa
Al-Azimu Maigir-
Ma Allah daya.
15. Al-Jalilu girman
Sa ya kai ga komai
Zukata da aikin
Mu Allah daya.
16. Duk mai ji da karfin
Sa sai Ya buwayai
Shi ne Al-Aziz Sar-
Ki Allah daya.
17. Wanene halittu
Suke girmamawa?
Al-Majiidu sai shi
Dai Allah daya.
18. Dau komai na fili
Da komai na boye
To Al-Basiru ya gan
Shi Allah daya.
19. Ko sirri ka aiko
Mun zance na boye
As Sami’u na jin
Sa Allah daya.
20. Ko aiki na tun da
Can kawo na yanzu
Al-Khabiru ya san
Shi Allah daya.
21. Sa aikin da du za
Ai ko ban gani ba
As-Shahidu ya shai-
Da Allah daya.
22. Halittu da aikin
Mu mai kyau da muni
Al-‘alimu ya san
Shi Allah daya.
23. Sai kowa kadan
Ne ko ka ga girma
Al-Kabiiru ya fi
Shi Allah daya.
24. Kaza mai darajja
Duk bai kai garai ba
Sai Al-Maajidu ya fi
Shi Allah daya.
25. Sa ikonsa nan fi-
Li kaza har na boye
Az-Zahiru, Al-Ba-
Din Allah daya.
26. Ba girma da dauka
Ka in ba garai ba
Zul jalali wal Ik-
Ram Allah daya.
27. Ga haske na sammai
Duk kaza da kassai
Kira shi An-Nu-
Ru Allah daya.
28. Kowa na da aibin
Sa sai dai Ta’ala
Al-Quddusu ba ai-
Bi Allah daya.
29. Halitta tagwaye
Ne duk anka yi su
Al-Wahidu shi d’ai
Na Allah daya.
30. Gaskiya na zatin
Sa waninsa karya
Ce sunansa Al-Haq-
Qu Allah daya.
31. Shi ne ma amintac-
Ce la shakka fihi
Don sunansa Al-Mu’-
Min Allah daya.
32. San kowa da ko
Mai duk za su kare
Al-Wajiidu bai kau-
Wa Allah Daya.
33. Da yai yo halittar
Sa ba sa ga kowa
Sai Al-Malik sarkin
Mu Allah daya.
34. In ya ba ka mulkin
Sa don ya ga dama
Ne Al-Maalikul mul-
Ki Allah daya
35. Al-Kadiiru mai i-
Kon komi da kowa
Ba mai gagarar Sar-
Ki Allah daya.
36. Al-Muhyiyyu ke ra-
Ya kowa da komai
Duniya Kiyama
Duk Allah daya.
37. Al-Mumitu ne zai
Kas kowa da komai
Sai Zatinsa zai zam
Na Allah daya.
38. Alqawiyyu Allah
Ba karfi iyarsa
Al-jabbaru ko an
Ki Allah daya.
39. Al-Qahharu Allah
Mai tilas ga kome
Rinjayarsa ce kul-
Lum Allah daya.
40. Shi Al-Mutakabbir
Ne ba mai isarsa
Mulki har da iko
Ma Allah daya.
41. Sa dukkan kwatancen
Ka Al-Muta’ali
Ya kere shi subha-
Na Allah daya.
42. Mai jujjuya komai
Na duk halittu Al-
Muhaimin a sunan
Sa Allah daya.
43. Komene iyawar
Ka zan dangana shi
Ga Al-Muqtadir gwa-
Ni Allah daya.
44. Al-Qayyumu tsayay-
Ye kan du bukatu
Ba d’ai mai maraita
Mu Allah daya.
45. Wa ke bibiyar ba
Yi ko da ina? Sai
Al-Raqiibu Maibin
Mu Allah daya.
46. Al-Matiinu kakkar-
Fa ba ya kumaici
Kore duk gazawa
Gun Allah daya.
47. Wa ye ke gabatar-
Wa? sai Al-Muqaddim
Jinkirin Mu’akkhir
Ne Allah daya
48. Komai mun ka mora
Ko ba don dabara
An Nafi’ ya amfa-
Nar Allah daya.
49. Kaza inda cuta
Ma Ad-Darru yai ta
Sauwaketa ya Sar-
Ki Allah daya.
50. Allah mai azanci
Ne ce Al-Hakimu
Ko ya bai da wauta
D’is Allah daya
51. Mai adalci tsakanin
Mu kowansa mowa
Al-Muqsitu bai bo-
Ra Allah daya.
52. Al-Wakeelu bangon
Mu komai mu bar mar
In ko mai ya dame
Mu Allah daya.
53. As Samadu ya na
Nan don damuwata
Sai in zo garai kul-
Lum Allah daya.
54. In ka k’i ni kai ban-
Za ko mai nufinka
Al-Mukeetu zai ce-
Cen Allah daya.
55. Shi kiransa d’ai za
Kai zai ba ka amsa
Al-Mujibu zan am-
Sa Allah daya.
56. Mu roka ya ba-
Yar shi bai asara
Al-Mu’ti ka bayar
Wa Allah daya.
57. Al-Basit ka buda-
Wa yayin rasawa
Sai yalwa ta sassab-
Ko Allah daya.
58. Gun halin tsananta
Kau kai agajinmu
Al-Mugheethu ne gau-
Su Allah daya.
59. Roko bai matsa mai
Sam! yalwa gare shi
Al-Waasi’ ga kowan-
Ne Allah daya.
60. Kaza in wadata
Ce Allah ya ba mu
Al-Mughniyyu arzur-
Ta Allah daya.
61. Rokona da ba hai-
Ri ka zan hanawa
Al-Mani’ ga sharri
Duk Allah daya.
62. Sannan bai bukatar
Mu komi na gun mu
Al-Ganiyyu isas-
She Allah daya
63. Al-Fattah ka bude
Mun kofa ta hairi
In hanya ta tushe
Allah daya.
64. Al-Walii garemu
Mu bayi gaba dai
Jib’e duk lamurran
Mu Allah daya.
65. Mai neman muk’ami
Kai, ga Al-Rafi’u
Shi zai kaika burin
Ka Allah daya.
66. In kai cin amana
Kau sak za ka sabko
Al-Khafid ya na nan
Ai Allah daya.
67. Dukkan mai bid’ar mul-
Ki in za ya samu
Al-Mu’izzu ke ba
Shi Allah daya.
68. In ko yai d’agawa
Don ba ya mutunci
Al-Muzillu kaskan
Tar Allah daya.
69. Zo nan mai bidar riz-
Ku jefar da boka
Al-Raziq ka arzur-
Ci Allah daya.
70. Ko kullum ka roka
Don ba ya bukata
Al-Wahhab ya bayas-
Wa Allah daya.
71. Al-Karim ya kan ba-
Yar kyauta ga kowa
Ko ba tambayar ba-
Yi Allah daya.
72. Mai kaunar halittun
Sa ba ya mugunta
Al-Wadudu zan son
Mu Allah daya.
73. Al-Hafiz ka kare
Mu mu sam kariya
Kar komi ya cuce
Mu Allah daya.
74. Mai hulda da bayin
Sa kan kyautatawa
Al-Barru ga kowan-
Ne Allah daya.
75. Mai shiryar da bayin
Sa kan maslaharsu
Ar-Rasheedu shirye
Mu Allah daya.
76. Jagora ga hanyar
Sa mik’akkiyaa sak
Al-Haadi ka dora
Mu Allah daya.
77. Mai gode wa aikin
Mu ko dan kadan ne
As-Shakuru ba re-
Ni Allah daya.
78. In kai mai nagar-
Ta shi zai yaba ma
Al-Haamid ga bayin
Sa Allah daya.
79. Al-Halim a halin
Sa ba ya fushi gab
Sai ya ba mu damar
Sa Allah daya.
80. Al-Ra’ufu Sarkin
Mu ko mun gazawa
Rangwama ga bayin
Ka Allah daya.
81. Wa ke son amincin
Sa kan du halittu?
As-Salamu amsar
Ka Allah daya.
82. Gun roko da laifin
Mu ba ma k’ure shi
As-Sabuuru ya ju-
Re Allah daya.
83. Sai mai tausayin ko-
Wa nan duniya kab
Ar-Rahman ka tausan
Mu Allah daya.
84. Ar-Raheemu jink’an
Sa gobe Kiyama
Wannan sai rabautac-
Ce Allah daya.
85. In komi ya kare
Allah zai ragewa
Al-Baki ya na nan
Shi Allah daya.
86. In komai yai gushewa
Ai ba d’ai magaji
Al-Warith Magaji
Ne Allah daya.
87. Shi zai mai da ba
Yi bayan macewa
Al-Mu’idu zai ra-
Ya Allah daya.
88. Zai tado mu bayin
Sa ranar Kiyama
Al-Ba’ith ga Ranar
Sa Allah daya.
89. Sai Al-Jami’ ya tara
Mu dukkanmu guu dai
Wa ye zai guje mar
Ne? Allah daya.
90. Ga ayyukan mu Al-Muh-
Si ya zan kidewa
Bai choge da zarra
D’ai Allah daya.
91. Ayyukanmu zai au-
Na ranar Hisabi
Al-Hasibu bai cu-
Ta, Allah daya.
92. Shi zai yo hukuncin
Sa hakki ga bayi
Shi ne Al-Hakam Sar
Ki, Allah daya.
93. Ja’irai su san Al-
Lah zai dauki fansa
Shi Al-Muntaqim Rab-
Bi Allah daya.
94. Muminai kuraran
Su ko ba iyaka
Al’afuwwu zai ya-
Fe, Allah daya.
95. Al-Ghafur da Al-Ghaf-
Far, suna guda ne
Mai yafe zunubban
Mu Allah daya.
96. Ga tarin Zunubban
Nan mun zo mu tuba
At-Tauwab ka karbe
Ta Allah daya.
97. To tammat fa waka
Ta nan zan aje ta
Ga baitinta Asma’-
U, Allah daya.
98. Ko da za a musa
Ma, ce ne Aliyu
Na Tilde ya k’ago
Ta Allah Daya.
99. Taro du iyayen
Mu Allah jikansu
Ka sa mu a Jannar
Ka, Allah Daya.
Alhamdulillah
14 January 2015

No comments: