Na Dr. Aliyu U. Tilde
A fahimtata, mutumin Arewacin Nijeriya ya fi karkata ga adalci a kan tattalin arziki. Wannan ba shaci fadi ba ne. Ina da hujjoji na.
Amma abinda nake kokarin nunawa a wannan post din shi ne lokaci ya yi da za mu fara baiwa tattalin arziki fifiko. Ta haka matsaloli da yawa za su warware, kuma ita ce hanya mafi tabbas ta samun adalci.
In ka duba tattaunawa a kan facebook, masalan, nan da nan za ka ga yana da wuya ka samu post masu yawa kan tattalin arziki. Akasari, kila sama da kashi 80 cikin 100 kan harkar mulki, zamantakewa da kuma addini ne.
Kullum kunnenmu a kasa ya ke mu ji labarin siyasa da badakkala wajen mulki da wa aka baiwa mukami kaza ko wa aka kora daga kujerarsa da sauransu. Dubi dai yadda labarin badakkalar makamai ke kewayawa tsakanin jama'a.
Dubi yawan comment da ake yi a post na siyasa koda kuwa barkwanci ne kawai. Dubi wanda ake yi idan wani ya takalo zancen addini: shi'a, izala ko darika, aikace aikacensu da kyansu ko kuma muninsu. Balle a ce ka ce Buhari ya yi tari kurum...ai sharhi sai ka gaji da karantawa. A wadannan abubuwa, wani ma zai iya tsine maka har kakanninka in raayinka ya saba da nasa.
Kaddara a ce ka yi post kan duwatsu masu daraja a Jahar Bauchi da darajarsu ya kai sama da biliyan 500 na dalar Amurka, wadanda suna jiran a debe su ne kawai. A rubutunka ka nemi gwamnati ta yi wani abu a kai. Mutane kalilan ne za su karanta balle su yi sharhi a kai. Tsakiyar shekaran nan, ma'aikatar man fetur ta ce za ta yi wani muhimmin bayani kan samuwar man fetur a Arewa-maso-gabas. Yanzu har karshen farkon sabuwar shekara zai wuce ba a ce komai ba kuma ba wanda zai tambaya ko ya zargi gwamnati da rashin cika alkawari. Kana yin wannan zargin, za a yi caa a kanka, don ana ganin kamar ka soki annabi ne, wai ba ka son Buhari.
Alhali kuwa, maganar ma'adinan Arewa-maso gabas su kadai da za a ba da muhimmanci a kansu, to da za su canza rayuwar mutane da yawa a Arewa da Nijeriya gaba daya. Amma hankalinmu ba zai kama wannan tashar ba. Nan da nan sai a kamo ta siyasa ya ce don ba ka son Buhari ne. A gunmu, in an so Buhari komai ya yi kyau.
Ina ganin abin da ya sa muke baiwa al'amarin mulki muhimmanci shi ne ganin yadda abokan zamanmu ke yawan sukanmu da kin cigabanmu da tsoron rashin adalcin da zai biyo baya in suna kan mulki. Wannan tsoron ya zama tabbas yau ganin wariya da muguntar da aka rika nunawa Arewa karkashin mulkin Obasanjo da Jonathan. Gani muke idan an mana adalci shi ke nan ko da kuwa halinmu na tattalin arziki bai canza ba.
Wani dalili kuma shi ne daga tarbiyyar siyasarmu, muna yi wa gwamnati kallon uwa ba da mama. Don haka in namu na kan mulki to gani muke zai yi shi da kyau yadda kowa zai samu wadatar tattalin arziki. Watau dai, muna ganin kamar ko yaushe tattalin arziki yana biyo adalci ne. Wannan shi ya sa muke baiwa siyasa muhimmanci fiye da komi.
To ba lalle ba ne sai mulki na hannunka za ka samu tattalin arziki mai karfi ba. A kasashe da yawa da na sani, ba haka abin yake ba. Misali, a Guinea Conakry, Fulani, wadanda 40% ne na al'ummar kasar, sun jima suna ganin tsaku don tarin dangi da sauran kabilu hudu ke musu. A karkashin Ahmed Sekou Toure, fiye da Fulani 40,000 ya kashe wanda suka hada da manyan yanbokonsu da yan siyasa. Amma hakan bai hana su jajircewa a fannin tattalin arziki ba ta yadda a yau su ke rike da 80% na arzikin kasar. Su kuma Mallinke da ke rike da mulki tun da kasar ta samu 'yanci, kamar yadda muke a Nijeriya, suna nan dabaibaye cikin talauci.
A Nijeriya musamman, saboda shimfida irin ta zalunci, karfin tattalin arzikin mutum shi ke sa a daga masa kafa, har a saurare shi, a biya masa bukata. Watau, adalci na biyo tattalin arziki ne. Zan ba da misali.
Mun yi shekaru 'yan Naija Delta suna tafka ta'asa a kasar nan, kamar fasa bututan mai, satar mai, garkuwa da jami'an kamfanonin mai, dss. A maimakon a kama su a daure sai igiya ta saura, sai aka ce a yi sulhu. Cikin sulhun, har da ba su alawus duk wata na makudan kudade suna barcinsu, da manyan kwangiloli. Bugu da kari, a yau, sai jaha guda a wajensu ta samu kaso daga asusun tarayya wanda ya fi adadin na wasu jihohi shida a Arewa. Duk da haka suna neman kari. In ba don suna da man fetur ba, me zai sa a musu wannan goma ta arziki?
Hakaza, ba don Yarbawa na da karfin tattalin arziki ba wanda ya hada da mallakan kafofin watsa labarai ba, da ba dalilin da zai sa a mika musu mulki salun alun, cikin ruwan sanyi kamar yadda aka yi a 1999.
Ashe kuwa ya kamata mu kara zurfafa nazari mu gane cewa mafi muhimmancin abinda zai fid da mu daga cikin halin da muke ciki shi ne mai da hankali kan gina tattalin arziki kwakkwara ta yadda duk wanda ya hau mulki dole ya yi da mu, kuma dole ya bar balbela da farinta. Ta wannan hanya ne kawai rayuwarmu za ta canza har ya zame an zabge marasa aikin yi kuma mukanmu mu rika tinkaho da daga kafada a tsakanin yan Nijeriya.
Kaddara mun fara matsawa gwamnati kan hakar ma'adinai. Ma'adinan dutsi kawai na Jahar Bauchi da muka ambata sun kai su biya kasafin kudin gwamnatin tarayya na shekara goma sha daya ko fiye. In da za mu matsa a fara hako su gadangadan, cikin shekara biyu rak Arewa gaba daya za ta fara canzawa. Bare kuma an wa sauran ma'adinai wannan hobbasa, irin su zinari a Zamfara, ko fetur da ke Borno da Bauchi, da uwa uba aikin gona.
Gwamnati sai da matsi ko da kuwa tana da niyya saboda wasu abubuwa suna iya dauke mata hankali. Matsi a nan ina nufin yawan naci na jama'a wajen kokawa da neman bayanin inda aka kwana kan abu ko manufa daga jama'a da ba da shawarwarin yadda za a gudanar da su, da sa ido da kwakkwafi.
Za mu yi babban hasara in har wannan dama ta mulkin Shugaba Buhari ta shude ba tare da cimma burin habaka tattalin arzikin yankin nan ba, kamar asarorin da muka sha yi a baya. Lokaci ya yi da za mu karkata akalar tunaninmu da maudu'in tattaunawarmu a kafofi dabam dabam zuwa taimaka masa da kuma kanunmu wajen cimma wannan burin, ba kawai mu yi ta bata lokaci wajen zantukan da ba za su kare mu da taro ba balle sisi.
Wannan magana haka take. In ba ka da arziki, ko adalci a magana ba za a maka ba balle a aikace. Kamar yadda Musa Naya'u Maimandula ya ke cewa ne a cikin wakarsa, Ceede, ya ce: Ko matarka ka fada wa gaskiya, in ba ka da kudi, ba za ta kula ka ba ko ma ta cukume ka, ta ce ka sau ni.. Amma in kana da kudi, ko sanda ka kwada mata a ka, ba inda za ta.
Yau in kana da abin hannu, sai a saurare ka, ko a gaban alkali ne, komi karyar da za ka fada. In kuwa ba ka da naira, in ka fadi gaskiya, sai a ce, "Ku rabu da shi. Talauci ne ya dame shi."
Arewa ga arziki a kasa. Amma sai an haka. Ga ruwan sama da na tabki mai yawa don noma, ga kasa mai fadi, ga hasken rana, ga iska, ga tsaunuka da koguna, ga rani, ga damina, ga hunturu, ga jama'a da matasa majiya karfi, ga hayayyafa, ga kasuwanni a duniya da makwabta, dss. Sannan dadin dadawa, ga Allah mai arzurtawa in aka tambaye shi kuma aka sa himma da ilmin yin abin da tattali da rikon amana.
Ga wani abu a kan matar sarki... hanya ta samun adalci mai dorewa: tattalin arziki mai karfi.
9 Janairu, 2016
No comments:
Post a Comment