On my 13th meter, Mujtath, with the help of Allah, I just completed a Hausa poem describing 10 things that will keep a girl decent as she undergoes higher education. It was motivated by the apprehension that many parents develop when sending their wards to high institutions. Four attributes MUST be observed by the parents, 6 by the girl. Below:
WALIDATA
Dr. Aliyu U. Tilde: Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Mujtath: ( - - v - - v - - )
1. Niyya garen ya Ta’ala
Rabbi biya mun bukata.
Rabbi biya mun bukata.
2. Mujtath na dosa da waka
Zam sauwake baitukanta.
Zam sauwake baitukanta.
3. Mata na so in wa waka
Domin su zam fa’idanta.
Domin su zam fa’idanta.
4. Yaran su san yadda za sui
Sharri ya zam bai matsota.
Sharri ya zam bai matsota.
5. Tsoro ya na gun iyaye
Shakka a kan duniyarta.
Shakka a kan duniyarta.
6. Bar ma a ce ja’mi’a ce
Tungar sanin zamaninta.
Tungar sanin zamaninta.
7. Na yo kiran duk iyaye
Horo ga ‘ya’yanku mata.
Horo ga ‘ya’yanku mata.
8. Na san suna nan gidaje
Dukkan su kal Walidata.
Dukkan su kal Walidata.
9. Tsoron iyaye bad’ala
Gun tarbiya kar a bata.
Gun tarbiya kar a bata.
10. Kar dai ya zam an sukola
Tun safe domin a tsabta.
Tun safe domin a tsabta.
11. Sai yammaci ta yi sannan
Wankin ya zam bai da tsabta.
Wankin ya zam bai da tsabta.
12. Hudu na ka ne don kiyaye-
Wa don ka zam fa’idanta.
Wa don ka zam fa’idanta.
13. Sauransu sai tai rikewa
Domin ta sam hankalinta.
Domin ta sam hankalinta.
14. To kai uba gun bidarka
Kai tir haram kar ka so ta.
Kai tir haram kar ka so ta.
15. Domin “wa ma kana da’we”
Ta zo da aya ka santa.
Ta zo da aya ka santa.
16. Ko ka yi himma ga noma
Kyawun hatsi ai kasarta.
Kyawun hatsi ai kasarta.
17. Don ko kasa in da muni
Ba ta hatsi mai wadata.
Ba ta hatsi mai wadata.
18. Har ga hadisi kazalik
Ya tabbatar wagga aya.
Ya tabbatar wagga aya.
19. Kore haram kullihinta
Ko tai yawa bar kwadanta.
Ko tai yawa bar kwadanta.
20. Muni yawa ko ya dala
Ba zai ya mai kyau bajinta.
Ba zai ya mai kyau bajinta.
21. Zanto gudun yin adashe
Tuba idan ya gabata.
Tuba idan ya gabata.
22. In ka ki ko san da tabbas
Ran ramako zai biyota.
Ran ramako zai biyota.
23. Sannan ka zam sa fahimta
Dunya da dina gurinta.
Dunya da dina gurinta.
24. Hadari ka zam bayyanawa
Danne ka zam ba fusata.
Danne ka zam ba fusata.
25. Ko za ta batta da Shedan
Zai zam makami a gunta.
Zai zam makami a gunta.
26. Sannan ka zam yin du’a’i
Allah walin ayyukanta.
Allah walin ayyukanta.
27. Yai kariya zam ta karfe
Shedan ya kasa shiganta.
Shedan ya kasa shiganta.
28. Karshe ka toshe talauci
Domin biyan duk bukata.
Domin biyan duk bukata.
29. In ba kudi kar ka fara
In ka k’iya ka rasa ta.
In ka k’iya ka rasa ta.
30. Mai ba ta ‘yar dukiyarsa
Shi za ta ba zuciyarta.
Shi za ta ba zuciyarta.
31. In zuciya ta gabata
Sauran jiki zai biyota.
Sauran jiki zai biyota.
32. Allah muna yin du’a’i
Tsare mu sharrin talauta.
Tsare mu sharrin talauta.
33. Yanzun a nan sai mu juya
Can gun shida mai jiranta.
Can gun shida mai jiranta.
34. Farko ta daukar nasiha
Tsoro na Allah gareta.
Tsoro na Allah gareta.
35. Duk lokaci kai ta lura
Allah gama na ganinta
Allah gama na ganinta
36. Zan wo nasiha ka zamna
Don jin su sa duk a kanka
Don jin su sa duk a kanka
37. Sannan ta kore tunani
Don tsabtace zuciyarta.
Don tsabtace zuciyarta.
38. Don zuciya in da kyawu
Dukkan jiki zai kamarta.
Dukkan jiki zai kamarta.
39. In ta fi son dayyibati
Allah ya na taimakonta.
Allah ya na taimakonta.
40. In ko ta so tambadewa
Shedan ya na ingizata.
Shedan ya na ingizata.
41. Daukan karatu da himma
Zai zam cikin kariyarta.
Zai zam cikin kariyarta.
42. Burinta kullum karatu
Tai son ta zarce sa’anta.
Tai son ta zarce sa’anta.
43. Sai ko ta zam babu yawo
Daki, karatu a gunta.
Daki, karatu a gunta.
44. In ba muhimmin dalili
Dakinta ne gun zamanta.
Dakinta ne gun zamanta.
45. Zabo da yawo ya gane
Kyauro ka ci nai farauta.
Kyauro ka ci nai farauta.
46. Kar tai k’awance da kowa
Sai mai irin kyan halinta
Sai mai irin kyan halinta
47. Don ko halin tir a kullum
Naso ya ke gun abota.
Naso ya ke gun abota.
48. Duk wanda zai dauki kanwa
Sai kansa ya dau farinta.
Sai kansa ya dau farinta.
49. Mai son ta ilmi da dina
Kama, k’awa ba irinta.
Kama, k’awa ba irinta.
50. Saura ukun zahiri nan
Zan so su kai kunnuwanta.
Zan so su kai kunnuwanta.
51. Aya ta Allah kiyaye
San babu zance kamarta.
San babu zance kamarta.
52. In za ta dinki ta gane
Yalwa ya zam ka’idarta.
Yalwa ya zam ka’idarta.
53. Dinki manunin sifarta
Haram a gun Maihalitta.
Haram a gun Maihalitta.
54. Kofa iri ba kamarta
Gun sa maza ca a kanta.
Gun sa maza ca a kanta.
55. Yadin ya zam bai yi shar ba
Mai boye fatar jikinta.
Mai boye fatar jikinta.
56. Ba nuna sassan jiki sai
Fuska, kafa hannuwanta.
Fuska, kafa hannuwanta.
57. Zance ko kar tai ta mad’e
Gudun macuci ya bita.
Gudun macuci ya bita.
58. Dubo fad’inai a sura
Ahzabi in kai bukata.
Ahzabi in kai bukata.
59. Fuska da murya kiyaye
Kullum ki zam kin rabauta.
Kullum ki zam kin rabauta.
60. Karshe ko in ba muharram
Bar duk maza gun kad’aita.
Bar duk maza gun kad’aita.
61. Malam, classmates gaba dai
Sai in akwai yar’uwarta.
Sai in akwai yar’uwarta.
62. Sannan su je gun a tilas
Sharholiya tai gudunta.
Sharholiya tai gudunta.
63. Party da picnic ta gane
Ganga ta Shedan a gunta.
Ganga ta Shedan a gunta.
64. In ta bi wannan nasihu
Wannan shidan sun wadata.
Wannan shidan sun wadata.
65. Za tai zama ko’ina ne
Sharri da d’ai bai gurinta.
Sharri da d’ai bai gurinta.
66. Fata ta karshe gurina
Allah biya duk bukata.
Allah biya duk bukata.
67. Ya’ya su zam sun yi himma
Hanyar halal duk su bita.
Hanyar halal duk su bita.
68. Sui tarbiya har su girma
Kalma ta tir kar a kai ta.
Kalma ta tir kar a kai ta.
69. Tammat a nan zan ajeta
Waka ta ‘ya’yan mu mata.
Waka ta ‘ya’yan mu mata.
70. Mustaf’ilun fa’ilatun
Baharinta in an bukata.
Baharinta in an bukata.
71. Ko tambaya ko musawa
Tilde, Aliyu ya yita.
Tilde, Aliyu ya yita.
72. Allahu zan yin salati
Gun Ahmadi mai bajinta.
Gun Ahmadi mai bajinta.
73. Yafewa duk muslimina
Zunuba ranar d’imauta.
Zunuba ranar d’imauta.
74. Shiryar ka kare diyarmu
Mata kamar Walidata.
Mata kamar Walidata.
Tammat bihamdillah
22 March 2015
(Walida is the name of my 400 level EE daughter-student)
No comments:
Post a Comment