Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

AMANA


Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Hafif: ( - v - -/ - - v -/ - v - - )
1. Na yi niyya zan tsara wakar amana
Jalla Ya Rabb! Allahu Sarkin amana.
2. Ba ni hikma har baituka sui halawa
Ba ni dama domin na wake amana.
3. Khaliqinmu yai yo cikakkar halitta
Alkawar ce sunanta yac ce, “amana.”
4. Duk halittu sun san da nauyin amana
Yai bidowa ko za su dauko amana.
5. Yin biyayya in an umarni hakika
Ba kiyawa sai dai a d’a’a, amana.
6. Mai biyayya zai sam rabo masu tsoka
Masu sabo za sui nadam kan amana.
7. Ga sama’u yai ma tayin: “Za ki dauka?”
“Ya Salamu! Ban so na yo cin amana.”
8. Ga duwatsu yac ce da su: “za ku dauka?”
“Mun yi karya in munka ce mun amana.”
9. Ga su kassai, “Shin za ku dau alkawar ku?”
“Mun yi tuba! Karfinmu bai wa amana.”
10. “Dan Adam fa! Ko za ka sanya a kanka?
Sai ya ce, “E! ni adda karfin amana.”
11. Jahili ne, ce mai “zaluman jahulan”
Zai nadama don ba ya imma amana.
12. Tambayata: mun kai sama ne a yalwa?
Duk da fadin, tsoro ta kai cin amana.
13. Shin kuna jin har mun fi dutse a karfi?
An taya mai, sai d’ai ya nok’e amana.
14. In zama ne ko jin daram, mun kasa ne?
Ta yi kuka gun Jalla ba ta amana.
15. Mun ga tosku mu yan Adam sai nadama
Na yi kuka, da ma a ce nai amana.
16. Kan umarni sai dai mu noke a kullum
Kan hani kau sab’o muke ba amana.
17. Mun nadama: Ya laitana mun biyayya
Har da ni nan, da dai Aliy yai amana.
18. Da da hali da nai fadin, “ban sani ba!
Ba ni nan ai ba ni na dauko amana.”
19. “Alkawar ne tun can ga kaka na fari
Ban ciki ai, ya za ku ce mun amana?”
20. Zo biyo ni don zan cire ma jahala
Don ka gane cewa da nauyin amana.
21. Don d’abi’ar duk dan Adam mantuwa ce
Annabawa sun zo da sakon amana.
22. Jaddadarwa, sun wo wa’azu gare mu
Ran kiyama, hujja ta kau kan amana.
23. Dan Adam yau ba d’ai na zabi gare mu
Sai biyayya sai mui ta himmar amana.
24. Mui ibada, mui gaskiya gun bid’armu
Kyautatawa har ma a ce, “dan amana.”
25. Duk amana sai kai riko kam da himma
Kar ka ci ta, ko da da kadan ce amana.
26. Za ta ci ka in dai ba kai hankaliba
Har da ‘ya’ya, har ma da jika amana.
27. Dukiya ce ko da ko sirri na boye
Zan ajewa, zamto mutum mai amana.
28. Kar ka ce wai ai duniya ba amana
Ka yi wauta in za ka zam ba amana.
29. Don mutane sun zam kiyawa ka bi su?
Za ka tab’e, nauyinka ne kai amana.
30. Rabbi roko: da ma ka yafe zunubba
Don Muhammad, wannan da kabba amana.
31. Laifukanmu ba sa kidayo gare mu
Sai ko ceto, don mun gaza gun amana.
32. Faa’ilaatun, mustaf’ilun d’oo mi yus6i
Baitukana, bahrin Hafif kan amana.
33. Zan salati har sallama kan Muhammad
Sa iyaye, har ma da duk muslimina.
Tammat bihamdillah
12 March 2015

No comments: