Kullum na tuna cewa Allah muke bautawa, kuma dominsa ake kokarin kamanta gaskiya da hulda da mutane, kuma a karshe shi zai mana sakamako ba dan adam ba, wallahi duk da dai nakan ji tsoro don rashin sanin tabbas, amma nakan nutsu da cewa Shi Allah ba kamar dan adam ba ne. Kuma, sai in ji wani dadi a zuciyata, in yi ta godiya da samun ubangiji da kuma madogara irinsa.
Da dan adam ne, da mun shiga uku. Don dan adam ne za ka taimaka masa sau dubu, rana daya ya juya maka baya don wani ya kawo sararka wurinsa ba tare da ya ji bayaninka ba, ko soyayya ta hadalu rana daya ya ki ka don jin wani gulma a kanka. Dan adam ne za ka taimakawa sau dubu cikin biyayya da girmamawa, ka sha wuya dominsa, ka kashe dukiyarka saboda shi, a gallaza maka saboda shi har ma a tsaneka saboda shi amma saboda kuskure na rana daya, ko rashin fahimta, ya dau karan tsana ya dora maka. In da ma.saboda akida ka yi, sai ka share kawai ka yi dariya ka ce, "Ho, dan asam."
Mu dai yan adam ajizai ne. Ko wane martaba muka kai, ajizai muke, ba za mu wuce wannan zangon na dan adam ba. A wannan zangon nake nima, ba zan iya ketara shi ba. Wane ni!
Babban magani a nan shi ne duk abin da za ka yi, ko aiki, ko so, ko ki, ko taimako, ko dafawa wani, ka yi da niyyar samun sakamako wajen Allah, bisa akida. Shi ke nan. Ladanka na wurin Allah.
Allah ba ya mantuwa. Komai ya na nan gunsa kididdige. Allah ba ya riko, mai yawan yafiya ne. Allah ba jahili ba ne bare wani ya kai masa sara, don shi masanin komi ne, mai labarin komi. Kuma, rahamar Allah ta fi azabarsa yawa. Allah ka yafe mana. Waye za ka rike da ya fi shi?
Madalla da wannan Ubangiji. Mun gode ma sa da ya shirye mu bisa wannan tafarki tun da safiya. Mun gode ma sa da ya ba mu Manzo da ya nuna mana wannan hanyar. Mun gode ma sa da ya ba mu iyaye salihai da suka dora mu a kanta.
Na fadi wannan ne saboda na baya. Ku rike akidar gaskiya a rayuwarku. Allah shi ne gaskiya, shi ke da gaskiya. Allah shi kadai zai iya saka wa gaskiya. Har abada, kar ku zaci ko tsinke wajen dan adam da kuka taimaka wa ko kuka yi hulda ta kwarai da shi saboda dan adam ne irinku, ajizi, kamar Dr. Tilde.
Za ku sha wariya kam da sabawa da mutane, da kazafi, amma za ku fi kowa samun natsuwa a duniya. Kuma har abada, Allah ba zai ba ku kunya ba. In kun riki gaskiya, ko k'asa kuka kasa a kasuwa za a saya don Allah zai dafa muku.
Haza wasalam.
Dr. Aliyu U. Tilde
No comments:
Post a Comment