Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

GA IRINTA NAN, KOSTAN SUN CAFKE DAN SENATOR BALA MUHAMMED KAN DUTI NA MOTAR MILIYAN 80

Lokacin da a bara wasu kafofin labaru suka ce an wai an samu sama da
biliyan talatin a asusun wani ɗanmu Abdullahi Bala Mohammed mun ɗauka
hayaniya ce kawai irin ta ƴan jarida waɗanda abokinmu tsohon Ministan
Tarayya Habuja ya hanawa pulotai. Haka ma rahotannin da ke tsegunta
cewa wai EFCC na tatsar tsohon ministan, tunda dai ba wata hujja da
waɗannan kafofin suka bayar.
Kwatsam sai dara ta ci gida a satin da ya wuce. Hukumar Kostan a
ƙarƙashin yayanmu, Col. Hamid Ali mairiytaya, ta ba da sanarwa cewa ta
cafke ɗan ministan kan kaucewa biyan cikakken kudin duti na wata mota
kirar McClaren 650s Coupe wanda kudinta wuri na gugan wuri ya kai har
Naira miliyan tamanin (N80m)! Ko kuɗin garken shanu nawa ke nan
oho? Ku taya wannan Bafilatani kwatance don ya fahimta. Kudin sun
ɗaure ma sa kai.
A maimakon Abdullahi ya biya hukuma dutin miliyan dari da uku (N103m)
sai kawai ya biya naira dubu dari uku (N300,000), inji Hukumar Kostan
a Lagos. To kuma sai allura ta tono garma. Yanzu haka, Kostan sun
duƙufa wajen binciko dutin sauran motoci irin wannan da ɗan namu ya
mallaka, ta na so ta san ko su ma akwai rinton da ya yi wa dutinsu. Da
ma kostan yaya, bare Baba Buhari ya ɗaure musu gindi ya tura yaya
Hamidu can? Cinnaka, baka san na gida ba. Ai Audu kam sai abinda hali
ya yi. Duk da dai an ba da belinsa, kuɗi kam za a zaƙulo su in ma ba a
dangana da kotu ba.
Ga link ɗin labarin in mai karatu zai so karantawa:
Mu dai mutanen Bauchi wannan abu ya zo mana da damuwa don muna cikin
masu ɗaga kafada muna zargin cewa badaƙƙalar Dasuki yan
Arewa-maso-yamma ne kawai ta shafa, mu a Arewa-maso-gabas fes muke ba
ruwanmu da cin hanci. To ga Audu ya jawo tsiya, dole yanzu kam mu kama
bakinmu mu yarda cewa kowace kanwa ja ce.
Wani shahararren marubuci, Alhaji Na-Allah Muhammad Zaga, daga Jahar Kebbi,
ya ce ya kamata a binciki yayana Bala Abdullahi, uban wannan yaron, shi
ma. In ɗansa kaɗai zai hau motar miliyan 80, to nawa shi kuma
uban ya mallaka? To mu dai sai mu kame bakinmu don ba za mu iya kare
shi ba a nan. Dabararmu ta ƙare. An sa biri a buhu.
Muna fata irin waɗannan abubuwa da muke kushe wa ba za su faru ba in
matasan da ke karanta rubuce-rubucenmu a Facebook sun girma sun zama
ministoci su ma. Allah sa kar su zame gaggan ɓarayi kamar yadda na
gabansu suka zame, kuma Allah sa ƴaƴansu ba za su riƙa facaka da kudin
jama’a ba a lokacin da danginsu a ƙauyen-ƙayau suke fama da fatara da
jahilci.
Ga irinta nan. Mu kam mun ci dubu sai ceto ran kiyama bayan mun
amayarwa EFCC a nan duniya.
(Ba kamar yadda wasu su ka buga ba, motar ta miliyan tamanin ne kawai (80m), dutinta kuma miliyan 103 kawai.)
Ga abinda www.today.ng.news suka rubuta:
START
Customs arrests ex-FCT minister’s son for underpaying luxury vehicle duty
In NATIONAL, TOP NEWS
January 30, 2016
Ayodele Filani
Senator Bala Mohammed
Operatives of the Nigerian Customs Service (NCS), Federal Operations Unit, Zone A, Ikeja, Lagos, on Friday, arrested Abdullahi Bala, the son of the former Minister of FCT, Senator Bala Mohammed, for alleged import duty underpayment on his exotic vehicle, a McClaren 650s coupe.
A top Customs source, who confirmed Abdullahi as the former FCT Minister’s son, said investigations to unravel whether there were other vehicles in his custody that either underpaid or evaded duty payment, was ongoing.
According to the spokesman of the unit, Uche Ejesieme, the vehicle’s duty ought to be N124 million but upon investigations, it was discovered a mere N300,000 was paid, thus defrauding the government of about N123,700,000.
Ejesieme said the man has been released on bail, while investigation into the matter was ongoing.
“The man claims to be former minister’s son. He was arrested on Friday. But has been released on bail since it’s a bailable offence. The investigation is ongoing at least to know how he was able to get away with paying just over N300,000. Our Officer in Charge of the Legal department says the duty should be about N124 million,” the spokesman stated.
Findings also show the vehicle costs about $280,000 in the US.
The MaClaren 650S Coupé starts at USD $265,500 and USD $280,225 for the 650S Spider in the US, while in Canada, pricing is CAD $287,000 and CAD $305,500 respectively.
It is a sport car in the range of the Ferrari and other luxurious coupes.
The latest addition to the McLaren range accelerates from 0 to 60 mph in just 2.9 seconds, and can reach 100 mph in just 5.7 seconds.
The standing quarter mile takes 10.5 seconds, and top speed is 207 mph in Coupé form.
This performance puts the latest model from McLaren 0.6 sec faster over the standing quarter mile than the iconic McLaren F1 road car, and a full second quicker to 124 mph, underlining its performance focus.
END
_________
Dr. Aliyu U. Tilde
1 February, 2016

No comments: