Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

An Mai Da Abbas Fago Wurin Aikinsa

Mutane za su tuna wani ma'aikaci matashi da gwamnatin Yuguda ta kora daga aikinsa don ya sake buga (reposting) labarin badakkalar kashe makudan kudin jama'a da tsohon gwamnan ya yi lokacin da ya kai matarsa haihuwa Amurka. Yau ina jin sama da shekaru biyu ke nan.
Tabbas Abbas ya ga bala'i, ga shi da sabon aure a lokacin, har amayar ta haihu, ga dawainiyar lauyoyi da kotu, ga rashin kwabo, dss.
Alhamdulillahi duk wannan ya kau shekaran jiya don sabuwar gwamnati ta nemi a sulhunta kuma a karshe ta mai da shi bakin aikinsa, kuma za ta biya shi albashin da ya rasa a baya. A nan, MA ya burge ni. Allah saka ma sa da alherinsa.
Saura kuma ya yi sulhu da Jibrin Yakubu wanda aka garkame kwanan nan a gidan yari don wallafa wasu sirri na gwamnati a jarida da yanar gizo. Mu sani babba juji ne. Wajibi ne a kansa ya zam mai yafiya kamar yadda ya wajaba a kansa ya zam mai rikon amanar dukiya da lamurran jama'a.
Ina ganin ko a dokokinmu, dokar Official Secrets Act ta 1968 ya zama tsohon yayi don masu shari'a da dama sun soki lamarinta. Abin nema ga mai suka shi ne hujja. Muddin ya bayar kai mai mulki sai ka lura ka gyara gaba.
Kuma, wannan ya zame darasi ga Abbas da mu marubuta. Don Allah ina kira ga duk wanda zai buga abu a yanar gizo, ya rika rubuta sunansa don kar wani ya taka sawun barawo kamar yadda ya faru da Abbas. Shi ya sa nake kokarin rubuta sunana a duk rubutun da na yi tun 1999 don in akwai abin da zai taso, kar a ci zalin wani, a neme ni. Ni zan kare kaina in ina da hujja. In kuwa kuskure ne bayanin, in ba da hakuri.
A karshe, ma'aikatan gwamnati su san cewa akwai dokokin da ke gudanar da aikin gwamnati. Kiyaye sirri na daya daga ciki. Amma in akwai badakkala, taimakawa ha'inci ne mutum ya boye. Don haka sai ya mika wa wani a wajen gwamnati - kamar jarida ko masu sharhi irin mu - a boye don ya fallasa don yanjarida suna da kariya ta doka da ta ba su damar boye sunan wanda ya basu labarinsu. Ta haka, ya taimaki jama'a kuma ya tsare kansa daga sharrin mahukunta.
Abbas! Ina taya ka murna. Alhamdulillahi.
Dr. Aliyu U. Tilde
13 February, 2016

No comments: