A 2003, marigayi Alhaji Magaji Danbatta, daya daga cikin mutum takwas da suka kafa NEPU, ya gaya mun takaicin da mutane masu shekarunsa suke ciki dangane da rashin cigaban Nijeriya, musamman Arewa.
Ya ce mun, a da, zatonsu in aka ilmantar da 'ya'yan talakawa komi zai yi kyau don za a samu jami'ai a gwamnati isassu kuma masu ra'ayin cigaba, duk matsaloli za su warware. Don haka ilahirinsu suka ba da cikakken goyon baya a zamanin turawa da Jamhuriya ta Daya wajen wanzar da ilmi ga dukkan al'umma.
Ya ce, kamar yadda yake gani yanzu, mu wadanda suka ilmantar din mun kasa rike amana kuma mun nuna matukar rashin kishin talakawa yanuwanmu. Mun mai da cin hanci da satar dukiyar jama'a hanyar rayuwa. Haka dai ya yi ta nuna mun bakin cikinsa. Ya ce ashe lokacin da suke kushewa na da gara shi sau dubu.
A shekarunsa a lokacin wanda ya kai saba'in, ya kai ni gonarsa ta shanu da ke wani kauye bayan kampanin 7-up a Kano, ya gaya mun yadda abubuwa suka ta'azzara har yana tunanin barin kiwon. Allahu Akbar. Dattijo mai shekara 70 amma bai zauna ba yana ta famar neman halal. Wanda in da sata ce da tuntuni yana cikin wadanda suka fi dukiya a kasar nan. Allah ya jikan shi. Allah ya gafarta masa.
Yau in na ga wadanda ake ta kamawa a kullum kan badakalar cin hanci sai in ga ni da su duk cikin tazarar shekaru guda muke. Mu ne wadanda su Alhaji Magaji Danbatta da su Tafawa Balewa da su Sardauna suka yiwa tanadin ilmi nagari da kyakkyawar fata. Yau mu ne muka zama ministoci da gwamnonin da manyan ma'aikata da suka ki baiwa na bayansu abin da ya kamata: ilmi mai inganci da rayuwa ta martaba, don kawai mu arzurta kanmu da 'ya'yanmu har abada.
Don haka ko an mana Allah ya isa ni ban ga laifin haka ba. Mu muka janyo haka. Don tsabar gazawarmu, da abubuwa suka tabarbare Allah ya kawo cikin na dauri, dan shekara sama da 70, don ya shugabaci kasar, watakila ko abubuwa za su gyaru. Wannan shi ne abinda muka sakawa Nijeriya da shi bayan ta fiddo mu daga kauye, da fatara, da rashin sutura mai kyau, gidan danga da bukka, kafa ko silipas babu, ta bamu ilmi wadatacce.
Yau mu ke da gidaje a Dubai da Amurka wadanda muka gina ta hanyar sata. Mun bar talakawanmu cikin danga da yunwa. Alhali lokacin da muke Jami'a ba irin alkawarin da ba mu wa Allah ba cewa za mu kawo canji. Allah mun tuba, da fatar abinda ke gudana yanzu zai kai mai tunani a cikinmu ya tuba ya yi ta istigfari da kyautata halinsa har zuwa mutuwarsa.
Kullum nake tuki, in na wuce ta kauyukan da wasu daga cikinmu suka fito ko rugagen da aka haife su amma suka nuna halin bera bayan daukakar da suka samu, sai in tuna maganar wancan dattijon, Alhaji Magaji Danbatta, in ce kaitonmu.
Ko jiya sai da na tuna haka lokacin da na ga hoton wani tsohon minista da aka nuna a Facebook a daya daga cikin titunan Turai. An ce EFCC tana ta tatsarsa, don kwanaki labari ya yadu cewa biliyoyi da yawa aka samu a asusun ajiyar dansa. To ina ga nasa? Kwanaki na wuce ta kauyensu cikin daji.
Haka in na wuce ta wani ruga a jejin da ke tsakanin Barikin Ladi da Dorawar Babuje. Duk dai mu ne. Ga yayanmu nan duk sun lalace sai kwaya, giya, mata da kisan kai. Zuriyya ta munana. Allah mun tuba, mun ci dubu sai ceto. Don Allah na baya kar ku yi koyi da mu. Kar ku shiga halin nadama da muka shiga.
Allah ka yafe wa almajirin da ke cewa cikin wakar Bulalar Gaskiya:
20. Ƙirga a gwamna babu sarki ko guda
Duk mu talakkawa muke wannan tsiya.
Duk mu talakkawa muke wannan tsiya.
21. Kokenmu da can wai ana yin danniya
Sarki da Ɗandoka da Resden bai ɗaya.
Sarki da Ɗandoka da Resden bai ɗaya.
22. To yau faɗa mun gaskiya na tambaya
Waye ya ke danne talakka duniya?
Waye ya ke danne talakka duniya?
23. In za ka ban amsa ka zam yin gaskiya
Ce mun talakkawa suke yin danniya.
Ce mun talakkawa suke yin danniya.
24. An ba su ilmi tun a wancan zamani
Yayin ake cewa ana yin danniya.
Yayin ake cewa ana yin danniya.
25. Canji a kai sai munka zam jamhuriya
Ƴaƴan talakka mun haye can ƙoliya.
Ƴaƴan talakka mun haye can ƙoliya.
26. Da ma a ce mun ɗauki hanyar gaskiya
Da yau gaba ɗai ba talakka duniya.
Da yau gaba ɗai ba talakka duniya.
27. Sai munka ɗau hali na ɓeraye na tir
Fata a gun kowa ya kas Nijeriya.
Fata a gun kowa ya kas Nijeriya.
28. Haƙƙi na milyoyin jama’a zai haɗa
Sannan ya sace don yana tsoron tsiya.
Sannan ya sace don yana tsoron tsiya.
29. Kullum ya zamna yai tunanin can gida
Danga da yunwa sai ya tsoro zuciya.
Danga da yunwa sai ya tsoro zuciya.
30. Sata ya ke, ƙari ya ke, ba dakace
Buri wadata babu dawowar tsiya.
Buri wadata babu dawowar tsiya.
31. Bai san tsiya na nan a gunai har abad
Ranar hisabi za ya zam ba dukiya.
Ranar hisabi za ya zam ba dukiya.
32. Dukkan mutane za su zo nema a gun
Wannan faƙir haƙƙinsu ranar gaskiya.
Wannan faƙir haƙƙinsu ranar gaskiya.
33. Dukkan ibada za a ɗauka ai rabo
Sannan ya ƙare babu komai sai wuya.
Sannan ya ƙare babu komai sai wuya.
34. Ran nan Jahannam za ta ce, “Your Excellence:
Antal aziz, antal karim, sai Hawiya.
Antal aziz, antal karim, sai Hawiya.
35. Tun shekarunai ɗalibi yai tsokaci
Burinsa yai ofis ya sace dukiya.
Burinsa yai ofis ya sace dukiya.
36. Mai ce mu gyara sai mu ɗau gaba da shi
Sharri na dunya duk mu ɗora mai wuya.
Sharri na dunya duk mu ɗora mai wuya.
37. In anka ce ga ɗan vacancy sai ka ga
Mun dandazo kowa ya na son dukiya.
Mun dandazo kowa ya na son dukiya.
38. Ba ɗai na kirki sai ko “illa man rahim”,
Ka san ko dunya ba a zamna lafiya.
Ka san ko dunya ba a zamna lafiya.
39. Yan takara sai alƙawar ba ko ɗaya
Wai don ya hoɓɓasa ya zan mai gaskiya.
Wai don ya hoɓɓasa ya zan mai gaskiya.
40. Azzalumai sai dai ka toge ƴan kaɗan
Sauran umuman ba su ƙaunar gaskiya.
Sauran umuman ba su ƙaunar gaskiya.
41. Yau ga shi nan mun kai kamannin ƴanwuta
Manya su tsine, mu mu tsine, bai ɗaya.
Manya su tsine, mu mu tsine, bai ɗaya.
29 January 2016
No comments:
Post a Comment