Na Dr. Aliyu U. Tilde
Tafiya ta fara kankama, mun fara shiga jarrabawa a canjin da akasarin masu zaɓe suka buƙata a 2015 yayin da suka zaɓi jami’iyya mai ci yanzu, watau APC, a matakai dabam dabam, amma musamman na Shugaban Ƙasa inda suka zaɓi Muhammadu Buhari, Yayana. Mu kam dama mun yi shekara 16 ke nan muna rubuce-rubuce kan jama’a su tashi a kawo canji. Alhamdulillahi, abin da ya rage yanzu shi ne canjin ya tabbata.
Amma tun kafin a je ko’ina, sai ga wasu abubuwa suna faruwa. Misali, shekaranjiya jaridar Daily Trust ta buga labarin yanda majalisa suke watanda da kuɗin jama’a, inda suka sayi jip-jip guda 108 a farashin kasha-mu-raba. Ga su kuma suna ƙoƙarin canza doka don su yi wa shari’ar da ake wa shugabansu Bukola Saraki ƙafar angulu. Ga joji-joji da lauyoyi sun daina cin hanci. Ga ƴan kasuwa na fetur da uwa-uba ma’aikata suna cin karensu ba babbaka wajen gasa mana aya a hannu. Ga jami’an tsaro na ci gaba da karɓar cin hanci a hanyoyi da ofisoshi da bai wa masu laifi haɗin kai. A ƙarshe, muma talakawa masu ƙin doka a cikinmu sun saki jiki kowa na abin da yake so. Kai ka ce ba Buhari ba ne a kan mulki.
A dandalolin sada zumunta, sau da yawa hayaniya takan kaure tsakanin mutane kan yadda gyaran ya kamata a yi shi, da kuma ko yakamata a ɗorawa Buhari laifi na rashin nuna isasshen tsananin da ya kamata don hana miyagu cigaba da tabka ta’asa.
Wasu suna ganin sai mu ƴan Nijeriya mun gyara kanmu ne kasar za ta gyaru. Wasu na ganin cewa yakamata Shugaba ya jagoranci gyara ta hanyar inganta hukumomin tsaro da tilasta wa jami’ansu wanzan da doka.
Hujjar kashin farko ita ce Yaya Buhari ba zai kasance a ko’ina ba. In mun azuma muka ce za mu tsai da munanan ayyukanmu, to canji zai samu cikin ruwan sauki. In ba haka ba, komi ya yi a cikin ofis dinsa, a can sama, Yaya Buhari ba zai iya canza na kasa ba. In canjin nan bai yiwu ba, masu wannan ra’ayin suna ganin laifin mu talakawa ne don ba mu tashi tsaye ba.
Misalin wannan ra’ayin shi ne na karanta ɗazu lokacin da wani makaranci ya yi ta’aliƙi a shafin Facebook na Dr. Sheriff Almuhajir bayan Doktan ya liƙa wani bidiyo na wata a-kori-kura da take shirin pakawa don a zuba mata fetur a cikin wasu maka-makan duron a gidan man NNPC (Megastation) na Damaturu. Ga abinda makarancin ya ce don waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi:
“Yanzu jama'a idan za muyi ma kanmu adalci ina laifin Buhari anan? Wannan duk irin abunda ke faruwa ne a kowanne gidan mai fadin kasar nan… Imagine, ga yan sanda, civil defense and other security agencies, station manager and pump attendants, ga jamaar gari kuma haka yana faruwa. Walahi muke azabtar da kanmu. Muke jawo ma kanmu masifa muna yima shuwagabanni sharri domin son rai… Yanxu don Allah a haka zamu gyara kasar nan? Don Allah a haka zamu dunga zagin Buhari bacin muke haddasa ma kanmu fitina?
Bari mu yi nazari mai ɗan zurfi a kan wannan ra’ayin kafin mu je kan ra’ayi na biyu a kasha na biyu na wannan sharhin.
To idan ba inda talakawa aka jagorance su suka yi juyin juya hali ba – watau revolution – yana da wuya a ce a tarihi akwai yadda aka kawo canji a tsarin demokradiya mai tsarin doka ta hanyar bijirewar talakawa. Ko an samu wani canji, na ɗan lokaci kaɗan ne kawai. Daga nan azzalumai za su dawo da cin karensu ba babbaka. To, in ma talakawan sun cije a wani garin, a wani ba za su cije ba, kuma tsara su yadda za su cije din su yaƙi zalunci a ƙasa baki ɗaya ba ƙaramin aiki ba ne. Haka kuma, in sun cije a kan cuwa-cuwar man fetur, ya za su yi da sauran fannonin rayuwa?
Iya sanina, ɗan adam yana iya tsaida shawara a ƙashin kansa ya daina laifi. Hakan yakan faru da mutane ƙalilan waɗanda Allah ya nufa da shiriya ko kuma ɗan Adam ɗin wayewarsa ta kai ya ma kansa karatun ta-natsu, amma ba zukatan mutane su gamu a lokaci guda su yarda cewa za su gyaru ba. In ba doka aka tsaida ba, ko aka kawar da dalilin da ya jawo aikata laifin – kamar a wadatar da mai a ko’ina – to fa akwai ƴan Adam da yawa a ƙasashe dabam dabam da za su gwada yin laifi ta yadda za su biya wa kansu buƙata, Allah bashin sauran mutane su ci gaba da wahala. In doka bata tsaida su ba, to fa za su zarce, su dauwama akan laifi har wasu su kwaikwayesu.
Dalilin wannan shi ne tabi’ar ɗan adam da Allah ya hallice shi da ita, kamar yadda ya faɗa a Alqur’aninsa maigirma, cewa ɗan adam na son aikata ɓarna (Al-Kiyamah), mai matukar son dukiya ne (Al-‘Adiyaat), mai handama ne (Al-Isra ) da sauran ayoyi. Inda duk abu ya zame halitta, to fa kau da shi a taron mutane sai an shirya.
Wannan shiri shi ne tsara doka da wanzar da ita. Ai ka ga da tsarin dokokin addini aka tarbiyattar da mutanen jahiliyya har suka zame mutanen kirki, suka gina al’umma mafificiya mai dokoki da tsare-tsaren tafiyar da lamurran ɗan Adam. Haka kuma da daular musulunci ta bunƙasa ta kai ga Sham da Farisa, sai suka ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren aikin hukuma da abinda suka iske ana yi a waɗannan kasashen. Shugabannin ba su bar mutane da imaninsu ba kawai. A’a. Sun ɗora su ne bisa doka har kowa ya saba. Mai laifi a hukunta shi, mai biyayya a sama masa sarari. Ko Zul-Ƙarnaini ma haka ya yi (Al-Kahf ).
A yau, akasarin mutane suna son doka suna bin ta albarkacin addini da wayewar ɗan adam, ko tsoron horo ko tsammanin samun amfani daga bin dokar. Amma a cikin kashi ɗari, dole sai ka samu kashi biyar ko ƙasa da haka na waɗanda suke son aikata laifi, su take doka don su biya bukatarsu in sun samu dama. Da farko za a yi doka, a sanar da ita kuma mutane da yawa za su bi ta. Amma don an san akwai waɗancan tsirarun da za su karya doka, sai aka dauki jami’an tabbatar da doka da zaman lafiya (law enforcement agents, jami’an tsaro). Doka ta kowa da kowa ne, amma jami’an tsaro na masu karya doka ne. In ba ka yi laifi ba, ba ruwanka da dansanda. Don haka bahaushe ya ce, kowa ya kwana lafiya shi ya ga dama.
Don haka zan rufe wannan kasha na farko da cewa a kafaffiyar ƙasa, wayayyiya, mai bin tsarin demokraɗiya da sanin haƙƙin ɗan adam, yana da wuya dukkan mutane su taru a kan bin doka bisa rajin kansu. A kullum masu laifi na nan wanda basu da yawa in ana aiwatar da doka, amma suna da yawa in jam’i’an tsaro ba sa aikinsu.
Daga wannan fuskar, sai muce ba a ɗorawa mutanen Yobe zuwa su hana saida wa ƴan bumburutu mai a gidan mai ba don yin haka yana da kamar wuya kuma zai iya haddasa fitina fiye da ta rashin man. Jam’i’an tsaro ne ya kamata a matsawa su aiwatar da aikinsu wanda ake biyansu albashi a kai kuma wanɗanda suka rantse za su yi. In suma sun ƙi yin haka, to kallo dole ya koma sama, kamar yadda za mu gani a kashi na biyu na wannan maƙalar.
Sai mun sadu anjima. Bari mu yi azahar.
18 April 2016
No comments:
Post a Comment