Ta Dr. Aliyu U. Tilde
__________________________________
Nazarin Aruli:
Bahari: Hazaj
Ƙafafu: Mafaa’iilun, mafaa’iilun, mafaa’il
Fiɗa: v - - - / v - - - / v - -
__________________________________
__________________________________
Nazarin Aruli:
Bahari: Hazaj
Ƙafafu: Mafaa’iilun, mafaa’iilun, mafaa’il
Fiɗa: v - - - / v - - - / v - -
__________________________________
1. Jama’a ga Dola ta kai ƙurewa
Ga waye za mu koka mai iyawa?
Ga waye za mu koka mai iyawa?
2. Ya sassauto da Dola don mu rintsa
Farashi duk ya sabko ba dadewa?
Farashi duk ya sabko ba dadewa?
3. Talakkawa mu sai gero da dawa
Da shinkafa da maiwa don ciyarwa?
Da shinkafa da maiwa don ciyarwa?
4. Iyalai kowane in zai ɗa’ami
Da yalwa za ya yo ba ya gazawa?
Da yalwa za ya yo ba ya gazawa?
5. Ga dukkan mai kudi birini da ƙauye
Ya wala ko’ina ba takurawa?
Ya wala ko’ina ba takurawa?
6. Hakan nan babu tsoro zuciya tai
Na cewa za shi karye yai rasawa?
Na cewa za shi karye yai rasawa?
7. Ga Allah shi kaɗai za mui du’a’i
Da hannaye na bawa mai gazawa.
Da hannaye na bawa mai gazawa.
8. Suna kallon sama an buɗaɗasu
Da gwiwa sha-ƙasa don durƙusawa
Da gwiwa sha-ƙasa don durƙusawa
9. Da goshi mai tabo domin sujuda
Idanu kau hawaye ke zubowa.
Idanu kau hawaye ke zubowa.
10. Mutane yanƙasa mun tambaye ka
Bare manya a Kaaba sun tsayawa.
Bare manya a Kaaba sun tsayawa.
11. Muna neman ka kawo naka ɗaukin
A bayan duk dabara ta gazawa.
A bayan duk dabara ta gazawa.
12. Zato yau ya zame ba a batunai
Ɗabibi ya gaza ba ya iyawa.
Ɗabibi ya gaza ba ya iyawa.
13. Idan ciwo ya kai wannan muƙami
Fa Allah shi kaɗai zai sauwakewa.
Fa Allah shi kaɗai zai sauwakewa.
14. Idan iska ta taso masu jirgi
Na kan teku ga wa za sui kirawa?
Na kan teku ga wa za sui kirawa?
15. Ga Allah Wahidun ne za su koma
Kira za sui dawaman ba tsayawa.
Kira za sui dawaman ba tsayawa.
16. Fari shi ma idan ya sabka mugu
Da yunwa duk ƙasa ba ƙosasarwa -
Da yunwa duk ƙasa ba ƙosasarwa -
17. Ga waye za a koma don ya amsa
Ruwaye sui ta sabka ba riƙewa?
Ruwaye sui ta sabka ba riƙewa?
18. Ga Allah ne mukan koma gaba ɗai
Da manya har da yara ba ƙiyawa.
Da manya har da yara ba ƙiyawa.
19. Ya amsa mui ta murna har mu gode
Mu ce hamdan ga rai mai tausayawa.
Mu ce hamdan ga rai mai tausayawa.
20. Gaban zaɓe mukai wannan du’a’i
Muna neman ka bai wa mai kulawa.
Muna neman ka bai wa mai kulawa.
21. A sannan ga bala’i kulla nau’in
Da sata ba tsaro sai cutatarwa.
Da sata ba tsaro sai cutatarwa.
22. Ka amsa kai kaɗai mun shaida wannan
Ka kawo shugaba mai kyautatawa.
Ka kawo shugaba mai kyautatawa.
23. Ƙasa duk tai ta murna don ijaba
Ta sa rai za ta canza ba jimawa.
Ta sa rai za ta canza ba jimawa.
24. Da farko mun zata an kama turba
Lamurra sun yi sauki ba dadewa.
Lamurra sun yi sauki ba dadewa.
25. Ɓarayi anka gurfanar a kotu
Kuɗaɗe anka kwace ba ƙidawa.
Kuɗaɗe anka kwace ba ƙidawa.
26. Dola ma sai ta sabko lokacin nan
A Wafa har a metan sun sayarwa.
A Wafa har a metan sun sayarwa.
27. Ta fetur kasuwa ta zo da nauyi
A kullum faduwa ne ba tsayawa.
A kullum faduwa ne ba tsayawa.
28. Da kaiwa tai talatin sai ya zango
Farashi babu ƙari ba ragewa.
Farashi babu ƙari ba ragewa.
29. Ga ma Naira da gangan tab biyo shi
Yana sauka ta na bi ba tsayawa.
Yana sauka ta na bi ba tsayawa.
30. Dola kau sai ta culla can sama’u
Ta ninka har ta zarce ba ragawa.
Ta ninka har ta zarce ba ragawa.
31. Farashi duk na kaya sai ya miƙe
Hawa komi yake ba tausayawa.
Hawa komi yake ba tausayawa.
32. Ashana, dankali, dawa, timatir
Suga, magi da mai sai tsawwalawa.
Suga, magi da mai sai tsawwalawa.
33. Talakkawa muna kuka a kullum:
Dola da ma ki sabko ba jimawa.
Dola da ma ki sabko ba jimawa.
34. Farashi kau na fetur yai sama’u
Ya culla har ya metan ba ragewa.
Ya culla har ya metan ba ragewa.
35. Basira tai yawa gun shugabanni
Su sa himma ga noma sui riɓawa.
Su sa himma ga noma sui riɓawa.
36. Kaza himma ga tono madinanmu
A sa jari a duk ba togacewa.
A sa jari a duk ba togacewa.
37. Matasa sui ta aiki kulla yaumin
Kwafa, yunwa su kau ba dakatawa.
Kwafa, yunwa su kau ba dakatawa.
38. Mu zan ƙwambo da yanga don wadata
Gida har ma maƙwabta sui yabawa.
Gida har ma maƙwabta sui yabawa.
39. Wurin aiki su nema duk su samu
Su koma sui ta hirar walwalawa.
Su koma sui ta hirar walwalawa.
40. Ta’ala mun kira ko za ka amsa
Cikin tsoro da sa rai ba ƙiyawa.
Cikin tsoro da sa rai ba ƙiyawa.
41. Aliyyu zai tsaya ƙarshen ƙasida
Hazaj tuƙa ya kawo ba musawa.
Hazaj tuƙa ya kawo ba musawa.
42. Ya tura can ga Farfesan Aruli
Bala ɗan Zulyadayn don bincikawa.
Bala ɗan Zulyadayn don bincikawa.
43. Salati ko da yaushe ba iyaka
Bisa Manzonmu har ranar tiƙewa.
Bisa Manzonmu har ranar tiƙewa.
Tammat bihamdillah
27 Fabrairu, 2016
No comments:
Post a Comment