Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

NASIHA GA BUHARI (1

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
__________________________________
Nazarin Aruli:
Bahari: Hazaj
Ƙafafu: Mafaa’iilun, mafaa’iilun, mafaa’il
Fiɗa: v - - - / v - - - / v - -
__________________________________
1. A mulki ba ya shi Allah Кadiri
Da komai na sa ne ba ma musawa.
2. Sa’annan shi ka iko tunda fari
Hakannan zai zame ba ya gushewa.
3. Кadiri in ya zartar ba musa mai
Halittu sai na’am ba kangarewa.
4. Idan ka samu mulki kar ka manta
Kalilan ne ya baka da jarrabawa.
5. Hakannan kar ka ɗauka zai dawama
Da sannu za ya ƙare ba jimawa.
6. Bala’i na jiran duk masu mulki
Hadisi ne ya zo sai gaskatawa.
7. Кiyama za a kawo kowanensu
Gaban Allah a jibge ba gujewa.
8. Hanunai kan wuyanai za a darme
A gurfanar da shi don tambayawa.
9. Da adalci kaɗai zai warwarewa
Idan yak ko ci zali sai wucewa.
10. Jahannam na ta hauka don ta tarbai
Ta na ce zalumi zan kalacewa.
11. Idan mulki ya zo ma yakamata
Ka zamna kai ta kukan jarrabawa.
12. A adalci ba ai tamkar gwanina
Abu Hafsin Umar mai kyautatawa.
13. Halifa ne na manzon talikai duk
Ya kan kwanta da kuka ba tsayawa.
14. Tunanin ran hisabi har bisashe
Su jawo hallaka in bai kulawa.
15. Nasihata ta farko gunka Mamman
Hisabi na zuwa ranar tsayawa.
16. Ka zam tamkar Umar wancan na farko
Ka zauna kai ta kukan jarrabawa.
17. Da adalci a mulki kulla halin
Hakannan zaka zamna ba gusawa.
18. Ga zalunci ka ce tir ba abota
Ka korai kulla yaumin ba ragawa.
19. Idan ya zo da ta hanyar dan gida ne
Ka ce mar ka ƙiya ba ka kulawa.
20. Mashawarci, minista ko asistan
Idan ya bi su ce mar: “ban biyawa.”
21. Da sauri kowane zam ba shi haƙƙi
Da zalunci idan ka jinkirawa.
22. Ga rayi duk na bayi ƙarƙashinka
Tsare kowa ya zam ba gallazawa.
23. Idan ko an yi gilla ne, misali
Da gangan rayuka sun tallafewa.
24. Ka yo sauri ka nemo masu haƙƙi
Da diyya, gafara za kai biɗowa.
25. Hakannan dukiyar bayi tsare ta
A duk hali ta zam ba tallafewa.
26. Ka kange ko’ina ba cin amana
Ɓarayi ko guda ba tausayawa.
27. Ɓarawo ko na dab ne kakkaɓe shi
Ka korai ba sani ba tausayawa.
28. Mutuncin ƴan ƙasa duk kowanensu
Ka kare kar a zubda kai kulawa.
29. A kul kar don siyasa ko hamayya
Ta sa ai cin mutunci ba kulawa.
30. Idan ko an yi ne tilas a gyara
A nemo yafiya ba dakatawa.
31. Ukun nan in ka tsaida ka wadata
Кiyama ba a komi sai yabawa.
32. Mutane nan na dunya sui ta murna
A kullum ba su tir gun ambatawa.
33. Idan ko an bari an tabka ɓarna
Da zali anka ci ba tausayawa.
34. A filli ko a sirri anka danne
Sanayya ko kusata ta rufewa.
35. Da rana za ta zo tabbas haƙiƙa
Ta hiddo kowane tai fallasawa.
36. A rannan babu lauya babu kurdi
Da mulki sai na Allah mai iyawa.
37. Ta’ala Rabbana kare mu sharri
Mu koma lafiya ranar kushewa.
38. Da tsira mai yawa sannan aminci
A kan manzo zuwa ranar tsayawa.
2 Maris, 2016
__________________
Sashi na biyu zai biyo gobe in sha Allah.

No comments: