Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

Kashe Professor Ahmed Falaki, Ina Aka Tsaya?

Yau shekara daya ke nan da rasuwarsa. A irin wannan ranar ne ya je sada zumunci a Yada Gungume da sauran kauyuka a Jahar Bauchi inda mahaifinsa ya zauna lokacin da yake baturen safiyo na kuza a 1950s.
Yana dawowa ne daga can, shi da direbansa da kaninsa, Abbas - wan uwargidata - suka gamu da yanboko haram da suka kwace Hilux din I.A.R/ A.B.U. da suke ciki. Ashe yanboko Haram din sun fito hari ne da suka kai wani kauye a karamar hukumar Rano.
Da su Ahmad suka isa kauyen, suka ba da labarin yanboko haram sun kwace musu mota. Aka ce ai dazu yanboko haram din suka bar nan. Sai su Ahmad suka ci abinci suka yi salla. Ana haka sai wani dansandan ciki ya ce musu gara su ke caje ofis din kauyen su gaya wa yansanda.
Da suke rubuta sitetmen a caji-ofis din ne wasu yansanda yansintiri suka iso. Wani daga cikinsu, dan Southern Zaria, ya tambayi Ahmad waye shi. Ahmad ya ce shi Farfesan aikin gona ne kuma Darektan Cibiyar Binciken Aikin Noma ta Jami'ar Ahmadu Bello. Ya baiwa dansandan I.D. card dinsa ya gani.
Abu kamar almara sai dansandan ya ce shi bai yarda ba, wai su Ahmad yanboko haram ne, wai ai Jonathan ya ce a cikin jami'an gwamnati ma akwai yanboko haram. Abu dai sai ya gagara, wuri ya rude, kauyawa suka taru. A karshe dai dansandan nan suka harbe Ahmad har lahira. Abbas ne Allah ya sa ya yi rai koda yake da aka ja su aka sa a bayan pick-up, yandandan su aza ya some. Direba ya gudu, aka bi shi aka kamo.
Sai yansanda suka taho da gawar Ahmad suna nunawa yanuwansu a kowane gari a kan hanya cewa ga yanboko haram nan sun buga da su sun kashe. Haka ma suka fada da suka iso Kano har aka kwana ana yadawa a gidan rediyo ana jinjina wa jarumtarsu.
Zuwa kashe gari labari sai ya canza da Abbas ya fara bayani a gadon asibiti. Nan da nan jikin Kanawa ya yi sanyi sanin cewa daya daga cikin fitattun yayansu ne aka kashe aka yi karyar danboko haram ne.
Da farko an aza za a yi wani abu. AIG Tambari Yabo ya rantse za a yi adalci. ASUU suka ce za su je yajin aiki in ba a yi wani abu ba. NHRC suka shigo ciki. Haka dai. Yansandan an kama su da farko inda suka tabbatar wa Tambari da su Prof. Yadudu da abin da ya faru kamar yadda Abbas ya ba da labari.
Dazu na tambayi Abbas a ina aka tsaya a maganar Ahmad. Ya ce mun kowa ya watsar da maganar. Yansandan an sake su an yi reposting dinsu. ASUU suma sun daina zancen. Abokan Ahmad kowa ya kama gabansa. Danginsa da ma ba su son a ja maganar tun da fari. Sun ce sun bar wa Allah.
Nijeriya ke nan. Kamar yadda abokin Ahmad, Prof. Sani Miko, ya fada mun kwanaki, a kasan na sai a kashe ka kuma ba abin da za a yi. Gaskiya ne.
Allah ya jikan Ahmad. Allah kadai ya san dalibai nawa ya taimakawa a A.B.U tsakanin 1975 zuwa 2015. Shi ya tsaya sai da aka ba ni PhD dina a Agronomy bayan shekara 10 da farawa. Miliyoyin manoma sun amfana da shi. Shi ya fara jagorantar shirin Sasakawa 2000.
Banda batun PhD, kafin nan, ya ba ni kanwarsa aure lokacin da ko lefe ba zan iya yi ba, kuma ban yi ba, saboda albashi na na malamin jami'a a lokacin bai isa in ci da kaina na yi hidimar karatu kuma in yi lefe ba. Auren kuma ya yi albarka. Alhamdulillah. Ita ce uwar Hadiya.
Wannan shi ya sa ni ma ba na matsawa duk wanda ya zo auren nawa 'ya'yan. Abin da yake da shi ya wadatar, ko menene, muddin na aminta da halinsa.
Allah ya jikan Yaya Ahmad, ya yafe masa zunubbansa, ya nawwara kabarinsa, ya sada mu da shi gobe kiyama a tutar ma'aiki, sallallhu alaihi wasallam.
Darasi a nan shi ne mu yi fatar Allah ya kare mu. An kashe farfesa kuma darekta ta hukumar gwamnati ma ba a yi komai ba, kuma ba za a yi ba, bare irina da kai, karabiti. Shafawa kanka ruwa kawai.
Ga wakar taaziyya da na masa a kan baharin
5. TA'AZIYYA FALAKIYYA
_____________________________________
Nazarin Aruli:
Bahari: Mudaari’ii
Ƙafafu Gwamau:Mafaa’iilun, faa’ilaatun (2, 4)
Fiɗa: v - - - / - v - -
_____________________________________
1. Mutane ga ƴar wasiyya
Shiri za mui don biyayya
Ga kowanne mui ta niyya
Yaƙini na nan a hanya
Tana tafe ba mai musawa.
2. Kuɗi, mulki sun hana mu
Tunanin Ranar Ƙiyamu
Makwanci sai dai ganinmu
Dawama ce ke rabonmu
Da tsammanin mui jimawa.
3. Faƙiri shi ma shagalta
Ganin tamkar zai wadata
Zato yake zai bar talauta
Zamimi kau bai fahimta
Wadata Allah ka baiwa.
4. A halin yarda da murna
Talauci, ciwo da ɓarna
Kaɗaici, taro da juna
Biyayya, aiki, amana
Ta kan ɗauka ba sanarwa.
5. Da sauri ta ɗau aboki
Masoyi Ahmad Falaki
Prof ɗin noma ga aiki
Hali nai kullum na kirki
Mutum ne mai fa’idarwa.
6. Fari ne zucci da hali
Da kyawun aiki da ƙauli
Masoyin dangi, iyali
Karimi fi kulli hali
Hanu nai ba dunkulewa.
7. Nagoggo da son taimakawa
Ga mainema ba ƙiyawa
Abin kowa sai yabawa
Halin Baaba ba ɗagawa
Ga alheri bai gazawa.
8. Mutum ne mai son zumunci
A hulda ba cin mutunci
Ba shi da cuta sai halicci
Na Goshi da bai ma butulci
Na Miko mai Sasakawa.
9. Ina zan ga ƙanin Husaini?
Ƙanin Hasana ya biya ni
Na Aisha, Balki, amini
Amin, Fatima, Ɗanfulani
Da kyau tamkar Larabawa.
10. Na Balki, Bala wan Abas ma
Na Abdulƙadir da Umma:
Riƙon Safiya ce da Mama
Amana guna muhimma
Ga tarbiyya sai yabawa.
Na Bello fari Ɗan Daneji
Kano birni babu jeji
Da mata, mota, ɗereji
Gida sanyi ba nguleji
Da harka ba ta tsayawa.
12. Na Dokta Ayagi da Nuru
Ƙanin Ya Ma’ruf saburu
Gida nai yau sai a ƙabru
Na Nasir kwanta da khairu
Shahada kai ba musawa.
13. Rahim haskaka kwanciyarsa
Ka yafe mar kuskurensa
Ka kai auni zurriyarsa
Ɗiya duk sui kyan halinsa
Da ba tir sai dai yabawa.
14. Da Allah ya ɗauki bawa
Mu kan riƙa kuka da kuwwa
Marayu don tausayawa
Gani muke ba sa da kowa
Ina wanda ka agazawa?
15. Idan na tuno ƴan Husaini
Na kan riƙa murna: yaƙini
Akwai mu da Allah Mu’ini
Magajin nauyi Amini
Ga bayi mai tallafawa.
16. Fa Yaya Husaini ya yi dina
Gudun dunya ga amana
Abokai, dangi ya auna
Ya bar ƴaƴanai ƙanana
Da Allah yai rungumewa.
17. Hakan Ahmad ya biyo shi
Da dina da himma da kishi
Siyam, salla babu fashi
Ga Allah ya ba da bashi
Da sakayyya mai riɓawa.
18. Zuriyya duk ɗayyyibina
Na Mustapha duk salihina
Mutane ba kha’inina
Ga kowa duka aminina
Halinsu clean sai yabawa.
19. Mu kan ɗau kurɗi da himma
Halal kwaso har harama
Shirin sai wa ɗiya salama
A ƙarshe zai zam nadama
Hisabinmu da ba wucewa.
20. Maso baya zan tunawa
Ta zamto mai kyau daɗewa
Guje wa haram zan kulawa
Ga addini ƙarfafawa
Da lada duk zam biɗowa.
21. Salamar dunya: Gudunta!
Iyakar nema buƙata
Ka bar wawaye su bita
Ta zam musu gunki na bauta
Duhu ne ba haskakawa:
22. Ɗiya duk sai fasiƙina
Da ƙyar ka ga ɗai muminina
Giya, ƙwaya cin amana
Maza, mata zalimina
Da yawo du ba tsarewa.
23. Faɗar Sarki ba musawa
Ɗiyar cuta: cutatarwa
Mu ɗau himma mui kulawa
Halal zanzan kal halawa
Cikin Aaraf ba musawa.
24. Hadisi ma kan haramun
Na manzo ya zo a kanmu
Ciyar da haram sa haramun
'Diyar su haram sai haramun
Ƙazanta mai sa ɗagawa.
25. Bala’in dunya: Ta soka!
Ta ba ka kuɗi zan na hauka
Da yin garari har hana ka
Tsarin salla ba da zakka
Da wargi du mai bugarwa.
26. Abokina ga garanti:
Ka wo tuba kan wafati
Da salla du har salati
Ka zam hairi kulla waƙti
Da sauri ba dakatawa.
27. Mujibu ina yin du’a’i
Nadama zo kan liƙa’i
Da Kalma indal fana’i
Iyalina kau wada’i
A gunka da ba sa marewa.
28. Su Ahmadu Allah jiƙan su
Da Mama da Baaba haɗa su
Da Adamu, Bello dukan su
Halilu, Husaini gama su
A gun Sidin Annabawa.
29. Kira: Gadatu, ya Safiyya
Gama da amarya Ruƙayya
Ku ɗau maganata wasiyya
Ku sa ƴaƴa kan biyayya
Su kai girma ba rasawa.
30. Ƙasidata du ga sautun
Mafaa’iilun Faa’ilaatun
Tunatarwa ce ta mautun
Talatin sa ɗai ga baitun
Tsaya mun nan ba daɗawa.
31. Salati gun Ɗan Amina
Ma'aiki gun alamina
Macecin duk muminina
Iyaye kai salihìna
Da mu duk Ranar Tsayawa.
Tammat walhamdulillah.
14 Fabrairu 2016

No comments: