Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

Dole A Bar Mutane Su Koka

Duk mulki na adalci yana bukatar abinda ake cewa feedback, watau samun bayani na abinda manufofin gwamnati ke haddasawa a rayuwar al'ummanta. Daga cikin abinda ya bata gwamnatocin baya, babbansu shi ne rashin damuwa da feedback. Shugabannin sun aza talakawa ba su da iyaka wajen juriya. Da haka da haka, har suka rufta.
Take-taken wasu magoya bayan Shugaba Buhari na neman dora shi kan wannan hanyar. Shugaba Buharin nan shi ke yawan cewa, "Jiki magayi". To lalle kam. In jiki magayi ne, dole a bar shi ya fada in ya ji. Amma ya ji, sannan a ce kar ya fada, wannan ba magayi ba ne.
Ya zama al'ada idan mutane suka yi korafi wasu magoya bayan Buhari sai su jefe su ko su zage su da tsammanin yin haka wai zai tsorata mutanen su yi shiru. Ni kuwa ina ganin haka ba halin mutum nagari ba ne. Allah ya baiwa Buhari mulkin nan bayan ya nema. Don haka ya hau kujerar hakkin jama'a. Yana da niyyar gyara kuma yana iya kokarinsa a fannoni da dama. Amma duk da haka, wannan ba dalili ba ne a ce komai daidai ne saboda Buhari ne. Sam. Dan adam ne, inda bai yi daidai ba, dole a fada masa. Zabensa aka yi bisa demokradiya wacce ta ginu ne a kan yancin fadin albarkacin baki.
Don haka, dole a hankaltar da mutanen da ke da wannan tabi'a ta jifan mutane da zaginsu a kan hadarin yin haka. Hadarin kuwa shekara sama da dari biyar Machiavelli ya fade shi: "Abu ne mai hadarin gaske ka yi kokarin yanta wanda yake son ci gaba da bauta, kamar yadda yake da hadari ka nemi bautar da 'ya'ya da ke son rayuwar yanci. To. Demokradiya yanci ne, danne bakin mutane bautar da su ne.
Akwai abubuwa da tilas a yi wa Shugaban Kasa uzuri don gyaransu zai dau lokaci. Amma akwai abubuwa da bai kamata a ce an dau kusan shekara ba a fara ganin haske wajen daidaita su ba. Man fetur na daya daga cikin wannan. A kasa kamar Nijeriya, rashin mai bai kamata ya ta'azzara ba har a rika sai da lita N170 zuwa N200, boro-boro a rubuce, ba tsoro ba komai yanzu kam, a gidan mai ba a black market ba. Ko lokacin Jonathan ba a kai haka ba a gidan mai, a sani na.
In matatunmu ba sa aiki ko ana fasa bututun mai, dole ne kawai gwamnati ta shirya shigo da mai daga waje, ko da kanta ko ta hanyar yan kasuwa, a farashin da ya kama, ba farashin da take so ba. Harkar kasuwa ce, ba wani surkulle ba ne da zai gagara.
Kuma in an shigo da shi, dole shugaba ya yi tsayin daka ya tabbatar da jami'ai sun sa ido. Wanda duk ya karya doka a hukunta shi a take, ko ma'aikaci ne ko dan kasuwa ne. Wannan abinda duk duniya ta zata Buhari zai yi ke nan. Shi ya sa da farko aka rika jin tsoronsa. Yanzu kuwa kowa ya koma gidan jiya don an ga bai nuna wannan kuzarin horon ba. Rashin horo kuwa, yana lalata mulki komi kyawunsa.
Don haka in mutane sun yi korafi a kan rashin wanzuwar man fetur sun yi daidai. Sun saba lokacin Jonathan suna sha a kasa da N100. Yakamata duk sabon tsarin da za a kawo, kar ya jawo karanci - saboda ganganci ne - da haka har sabon tsarin ya kankama. In ba haka ba kuwa, dole mutane su koka don ba bayi ba ne su da za a kulle bakinsu.
Sannan akwai rashin tabbas a kan matakan da gwamnatin ke dauka dangane da wannan matsala ta fetur. A kullum Minista Kachikwu na canza magana, abin kamar da yaudara a ciki. A Nuwamba ya ce, za a samu mai wadatacce a Fabrairu. Fabrairu ta wuce, ahiru. Sati biyu da suka wuce, ya ce litinin din satin da ya wuce za a samu mai birjik a gidajen mai a duk fadin kasar nan. Sai ga shi ba a samu ba, abin ma sai kara lalacewa ya yi. Jiya kuma ya canza magana, wai wannan wahalar fa za a kai watan mayu a cikinta. Ya Ilahi! Gaskiya wannan ba daidai ba ne. Kuma dole 'yan Nijeriya su fada don shugaban kasa ya gyara.
A bar ganin ana girmama Buhari a yi tsammani ya wuce a soki shirye-shiryensa in ba su wanzar da d'a mai ido ba. Duk martabarsa a idanunmu bata kai ta khalifofin Manzon Allah ba (SAW). Kuma duk adalci da wuya ya yi kamar Sayyidna Umar (R.A.). Amma haka ya gamu da wata mata lokacin da yake yawon neman raayin jama'a a kan mulkinsa (feedback) a asirce cikin dare. Matar bata san shi ne Umar ba. Sai ta ce: Allah ya isan mana da Umar. Sai hankalin Umar ya tashi ya ce mata: "To menene laifin Umar kuma baiwar allah?" Matar ta ce: "Ahaf! Yana shugabantar mu amma bai damu da lamarinmu ba." Ta nuna masa halin yunwa da take ciki tare da kananan 'ya'yanta da ta dora duwatsu cikin tukunya don su ga kamar sanwa ta dora, da haka har barci ya dauke su.
Nan da nan Umar ya ruga baital mali, ya debo abinci, ya hana Abdulrahman dauka, ya ce, "dora min." Abdulrahman ya ce, "In dora maka ko in dora a kaina." Umar ya ce, "A'a, a kaina. Za ka dauke mun zunubi na ne gobe kiyama?"
Suka isa wajen baiwar Allah. Umar ya bata kayan abinci. Ta yi murna. Ta ce, wallahi kai ka fi cancanta da ka zama khalifa ba Umar ba. Abdulrahman ya ce wa Umar, "to mu tafi." Umar ya ce: "Wallahi ba zan bar gun nan ba sai na ga yaran nan suna murna don koshi kamar yadda na same su suna kuka don yunwa"... Haka kuma aka yi.
Umar ke nan, Abu Hafs, wanda ya yi sanadin saukar ayoyi da dama a kur'ani kuma sau da yawa Kur'ani na tabbatar da raayinsa. Shefan ba ya zama inda yake. Amma duk da haka, a kan kayyade sadaki, mace ta canza masa ra'ayi har ya ce: "Umar ya yi kuskure, mace ta fadi daidai."
Umar yana Madina za a kawo masa korafin gomnoninsa, ya sa a kira su sai ya ji hakikanin abinda ya faru. Mafi shahara da aka fi buga misali da shi shi ne korafin mutanen Hims, ko Homs da ake kira a yau, a kasar Syria. Gwamnan, wanda rigarsa guda daya ce a duniya, ba yi da yaron gida ya zo ya kare kansa. Da Umar ya tambaye shi me ya sa ba ya fita da dare don lura da harkokin mutane, sai ya baiwa Umar amsa: "Rana ta Umar ce, amma dare na Ubangijin Umar ne." Kun ji maza, masu fadawa mulki gaskiya!
Duk duniya ta shaida adalcinsa Umar. Duk mai adalci a shugabanni a yau sai dai ya yi kamarsa a sahun muminai. Amma feedback a wurinsa yana da matukar muhimmanci. Har fita yake yana nemansa da kansa. Ya saurari korafi, kuma ya dau mataki na gaggawa kuma ami aikatuwa. Takobin gaskiya dan Khattabi!
Na ji wasu malamai suna cewa ai korafe korafen da mutane suke yi alamar butulci ne ga Allah. Sun fi sahabbai sanin Allah ne ko wanda suke kokarin karewa ya fi Umar ne? Gaskiya itace, dole a masa uzuri a kan wasu abubuwa, wasu abubuwan kuwa dole a yi korafi don ya tashi tsaye ya gyara. Su yi mar addu'a da ba shi shawarwari shi ya fi ya fi wannan sigar ta kokarin shiga tsakanin talakawa da Ubangijinsu.
Don haka a musulunci akwai cikakken yancin korafi don bai yarda da danniya ba, kowa a masa gum. Yakamata duk maso Buhari mu san da haka. Wannan ita ce mafita gare shi, ba kokarin daukaka shi zuwa ga halaka ba.
Ina son mu gane cewa shugabannin baya an musu korafi da yawa, su ma da suka hau mulki da karfin bindiga ko ta hanyar magudi. Shugaba Buhari da ya hau mulki da cikakken goyon bayan talakawa shi ya fi cancanta su kai korafinsu wurinsa, don shi nasu ne. Kar kawai a shantake za su yi ta goyon bayansa, kamar wata Salamatu, saboda jiki fa magayi ne. Tutsun talaka ba kyau.
Mu dai za mu ci gaba da bayyana ra'ayinmu akan al'amurra kamar yadda muka yi wa shugabannin baya, kuma kamar yadda za mu yi wa na gobe idan muna da rai da lafiya.
Abinda Shugaban kasa ya kamata ya yi shi ne ya tashi gadan-gadan kan maha'intan manyan jami'an gwamnati da yan kasuwa. Dole kuma ya sayo fetur daga waje ya baiwa yankasa komi tsadarsa saboda muhimmancinsa a rayuwar kasa. Dola da ake tarawa ba ta da amfani muddin ba kawo sauki za ta sayo wa jama'a ba. In an shigo da shi dole a tattaro duk karfin gwamnati don tabbatar da wanzuwarsa a ko'ina. Ka ko san karfin gwamnati yawa garai: Shugaban Kasa, Ministoci, NNPC, DPR, yan sanda, soja, EFCC, SSS, civil defence, customs, kotu da sauransu. A ce duk wadannan wanzar da man fetur ya gagare su? Sai dai idan an kyale maha'inta ko ba a dauki matakin da ya dace ba.
A karshe, dole shugaban kasa ya rika hadawa da muzurai da tsawatarwa, da cizo, da sara da suka, da harbi da hantara ga duk wanda ya yi karan tsaye kan manufofin mulkinsa....Rikon tausayi da yake wa jami'ai ba zai yu ba. Hahaha. Sunci sa'a ba su zo a 1984 ba.
Rashin horo yana cutar da mulki
Ya zare mai laka yai laulayewa.
Rashin horo a mulki bai yi kyau ba
Alama ce ta bawa mai gazawa.
A tarihin ƙasar sam ba kamatai
A mulki ba ya shi gun raunanawa. (1)
Ya bai wa NNPC dateline na samar da mai ko kuwa manyansu kaf za su rasa mukamansu ka ga. In ya rushe su ya sa wasu, dole za su kama aiki bil hakki.
Muna fata Allah zai taya masa wajen tashi tsaye kan yan iskan kasar nan. Suna nan da yawa. In ba a nuna za a taka su ba, ba za su bi gaskiya ba. Inji Dankwairo a wakar Sarkin Daura Bashar: "Sai an canza masa hali, talakka bai san talakka ne ba..."
Dr. Aliyu U. Tilde
24 March, 2016
_____________________
(1) Wakar Nasiha Ga Buhari

No comments: