Dazu shugaba Buhari ya sadu da shugabannin Benue.
Ina ma a ce zai saurari shugabannin Fulani ko da sau daya ne?
Mataimakinsa Osinbajo da aka tuhume shi da nuna bambanci bayan daukan fansar Numan don ya kai ziyara wajen shugabannin Bachama amma bai ziyarci Fulani ba, sai, a kashin kansa, ya kira shugabannin Fulani don ya ji nasu bayanin.
Sarkin Kano da Lamidon Adamawa da shugabannin kungiyoyin Fulani da na mazauna lardin Adamawa da Taraba duk suka halarci taron. Ina cikin wadanda suka je.
Da ya gama saurarensu, sai ya ce wannan matsalar abin da ya sa ta gagara karewa rashin kiyaye doka ne a Nijeriya. Ya ce su a gwamnati suna da duk rahotannin abin da suke faruwa. Don haka ba zai bata lokaci ba wajen tattauna baya. Abin da za a yi shi ne a fito da hanyar daukan matakai na dakile wadannan rikice-rikicen.
Nan take ya ce a kafa kwamiti na hadin gwiwa tsakanin Fulani da jami’an ofishinsa don tattauna matakan. An tura da sunaye bakwai a bangaren Fulani tun a lokacin. Aka ci gaba da jira... Jira ake har yau, bai samu izinin cigaba ba daga “sama”. Shiru kake ji, wai Malam ya ci shirwa.
Sai ga abin da ake tsammani ya faru: An kai wani harin daukan fansa kan yanbangan da ke kashe Fulani da kwace shanunsu a Jahar Benue da sunan aiwatar da dokar hana kiwo. An kashe wadannan dakarun hana kiwo da yawa. Nan da nan Nijeriya ta dau dumi. Nan da nan Shugaba Buhari ya aika da ta’aziyya ga mutan Benue da gwamnatinsu, yana jimami da jajantawa.
A karshe, Shugaba Buhari ya kira manyan jihar Benue yau, da gwamnansu suka tattauna. Aka fito waje aka dau hoto na tarihi. Rahotanni daga baya sun nuna cewa ya yi ta jajanta musu kan abin da ya faru kuma yana rokonsu don Allah su yi hakuri su zauna da sauran mutane a jaharsu. Sannan ya musu alkawarin kama duk masu kashe-kashen a jahar.
Fatata a nan ita ce, da zai yi kyau, kamar yadda ayar Qur’ani da dokar bature ta nuna, ya saurari shugabannin Fulani a kan harkar Benue kamar yadda mataimakinsa ya sauraresu bayan rikicin Numan. Mutanensu ake hana wa sana’a, ake zalunta da karfin hukumar jaha, ake kashe su da dabbobinsu, kuma gwamnatin tarayya ta kasa ba su kariya, amma ana kiransu yan ta’adda.
Bukatar Fulani a wajen Buhari yau bai wuce na sauraro ba kamar yadda yake sauraron sauran a’umma, watakila zai taimaka masa sauke nauyin hakkin al’umma da ke kansa, ko ya samu saukin hisabi gobe kiyama.
Bana tsammanin Fulani suna da niyyar rokonsa wata alfarma ko kwato musu hakki ba, ko neman kariya daga gunsa, don ko taaziyya bai taba musu ba. Bai taba tir da kashe su ba. Bai taba kiran makasansu yan ta’adda ba, haka za bai taba sa an tsare kowa cikinsu ba. An wuce inda za su roke shi.
In za su yi roko, akwai wanda suke roko. Shi ke ba su nasara a fafutukar da suke yi da zalunci a jahohi dabam dabam. Allah, mai mulkin gaskiya. Shi ne gaskiya, mai aiki da gaskiya. Fulani za su cigaba da mika al’amarinsu ga Allah. Shi ya kare su tsawon aru-arun shekaru a tsakanin al’ummu dabam dabam.
In Allah ya yarda, Buhari zai gama mulki da sauran Fulani makiyaya suna kiwo a Benue kamar yadda Jang ya bar mulki suna kiwo a Pilato. In kuma Allah ya ga dama, watarana zai kawo shugaba da zai dauke su da kima, ya ba su hakkin sauraro, kamar yadda ake daukar masu zalumtar su da kima a yau.
In kuma Allah ya ga dama, ana iya korarsu daga duk jihohin da ba su da gata. Wannan ma ba zai sa su k’are ba. In haka ya faru, a sani, wallahi, abinda ya ci Doma, ba zai bar Awe ba.
Dr. Aliyu U. Tilde
15 Janairu 2018
15 Janairu 2018
No comments:
Post a Comment