Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

Kashe 'Yan Shi'a Zalunci Ne. A Yi Hattara

Na Dr. Aliyu U. Tilde
Na sha fada a hira da kuma rubutuna cewa duk wanda ka kafirta shi, a cikin matakai dari da za ka bukata don kashe shi, ka gama da matakai 99, dama ce kawai ka ke jira ka cika na darin. Da razar damar ta samu ba za ka san lokacin da za ka kashe shi ba, kuma ka jawo Allah ka ce shi ya ce maka ka yi.
Ko Boko Haram a farkon da'awarsu, ba su yi tsammanin za su taba kashe musulmi yadda suke yi ba yanzu. Sun aza fadansu da jami'an tsaro ne kawai. Sannu a hankali, da tura ta kai bango, sai ga shi sun yi wa al'umma jama'u suna kashe kowa, kuma su kawo Allah su ce shi ne ya ce su yi.
A lokacin, mun yi ta tsawatawa don kungiyoyi masu irin wadannan akidu na Sunna da na Shia su daddara, amma ina? Wa zai saurare mu, ga Shedan yana buga gangar zubar da jini?
Hasbunallahu wa ni'mal wakeel.
In mutum ya kai wannan matsayi wajen bata, ayoyi da gargadi ba za su masa amfani ba. Ba don haka ba, tsawatawar da Allah ya yi a Suratul Nisa'i a kan jahannama, da fushinsa, da wautarsa ga wanda ya kashe musulmi da gangan ya isa duk mai danshin imani a zuciyarsa a tsorata, ya ki daukar ran musulmi ko da kuwa malaminsa ya ce masa ya yi. Amma in ba imani sai duniya, "ayoyi da gargadi ba za su amfanar ba."
Balle kuma hadisan Annabi (SAW), wadanda aka ce ya ce, kuma wasu suke fifitawa a kan Al-Qur'ani, ake musu canki d'ai-d'ai. Gargadin da ya yi a Arafa cewa bayansa kar mu zame kamar kafirai mu rika kashe junanmu, tsallake shi ake yi a nemo na "wanda ya yi kiyayya ga waliyyi na, to na yi shelar yaki da shi." Kuma a ce wannan hujja ce na mutum ya d'auki makami ya kashe wani. Wannan jahilci da son rai ya kai intaha. Allah ka yi mana tsari, yaaaa rabb!
To in da wanda yake zagin wasu sahabbai (R.A), hukuncinsa kisa ne, to ai da an saukar da wahayi a kai ko kuma a sami hadisi da ya nuna haka, ko a tarihi a aiwatar da shi. Duk da cewa girmama sahabbai dole ne a gunmu Ahlul Sunnati Wal Jama'a na asali, yana da wuya ka samu hujjar kafirta wanda ya yi haka balle kuma ka sami hujjar kashe shi. To wadanda suka kashe sahabban a cikinmu kuma mu ce musu me? Ina jin mutum ko kwakwalwar jaki ne da shi, ya san kisa ya fi zagi muni.
Wannan fitina da wasu yan'uwanmu malamai - masu ci da addini - suke kara dulmuya mu a cikinta dole mu tashi da rokon saukinta daga Ubangiji. Ba karama ba ce. Babba ce. Su suka ingiza kisan gilla da jami'ai suka yi wa yan Boko Haram a garin Bauchi da Maiduguri a farkon al'amarin a kan cewa su Khawarijawa ne. Malaman da suka ba da wannan fatawar, a kalla na garin Bauchi, sun san kansu, don wasunsu har barin kasar suka yi da Boko Haram suka fara dauki d'ai-d'ai, wasu kuma sunka boye; shugabanninau kuwa suka yi tsit, har sai da aka fara samun galaba kan Boko Haram kafin suka fara cika baki.
Da haka aka hallaka marigayi Yar'adua. Ina tuna farkon tashin fitinar a Maiduguri, kwana biyu kafin ya tafi Brazil ziyara. Da aka tambaye shi a filin jirgi a Abuja wannan safiyar, ya ce ya ba da umarni a kurmushe su kuma za a gama kafin karfe hudu na yammacin wannan ranar. Ba a jima ba matsalar rashin lafiyarsa ta ta'azzara, mulki ya gagara, ya bi su barzahu.
Dole ai! A tsangayar yan Boko Haram a bayan Airport din Bauchi, mahaddata nawa aka kashe, sannan aka kawo gireda ta share wurin wannan Litinin? Allah bai yarda da zalunci da azzalumai ba. Ba ya son su. Haka dai ya tabbata a cikin littafinsa kuma mun gani a aikace.
Haka nan Allah ya saukar mana da musiba wacce ba ta tsaya a kan azzaluman ba kadai. Shekara shida kuma har yanzu tana nan don ko jiya bam ya tashi a Maiduguri wasu sun rasa rayukansu. Kuma gobe in wasu daga wani sashi na al'ummar Nijeriya suka karbi mulki, haka za su mara musu baya su farfado da su, su ba su makamai kamar yadda su Jonathan suka yi a baya, su dawo da kashe mu, sakamakon zaluncin da muke aikata wa junanmu wanda mugayen malamai ke ingizawa a maimakon su sulhunta ta hanyar tilasta gwamnati ta martaba bin doka a duk lamarinta.
To ba mu daddara ba, musibar Boko Haram ba ta ishe mu ba. Malaman da suka yi kudi da ita ta hanyar tatsar gwamnatoci ga alama suna neman bude wani shagon. Suna zuga gwamnati kan cin hakkin yan'shia, wai don suna zagin sahabbai. Yanzu sun wuce nan, har sun kai ga tunzura mabiyansu su abka musu da kisa da kona gidajensu da kadarorinsu.
Abin kunyar da ya abku ke nan jiya a garuruwan Kaduna, Funtua, Kano da Jos. Yan koren wadannan malamai a yanar-gizo sun fara kiran mutanensu na garuruwa dabam dabam da cewa suma su bi layi, su dau irin wadannan matakai. Shugaban Izalar Kaduna, Sheikh Abdullahi Bala Lau kam ma har cewa ya yi a Rediyo wai Gwamnatin Jahar Kaduna ta hana addinin Shi'a, alhali kuwa ba haka maganar take ba, soke kungiyarsu aka yi ba hana addininsu ba, abinda ba wanda yake da wannan hurumin a Nijeriya.
Abin mamaki shi ne yadda gwamnatin Buhari take aikata kurakuran da ta Umaru Yar'adua ta aikata na yarda da a karya doka har a kai ga kisan gilla irin wanda ya faru a Zariya bariya, da kuma irin wanda jami'an tsaro da wasu mutanen gari suka aikata a garuruwan da muka ambata a baya.
Wannan babban kuskure ne don bala'in da zai jawo ba kadan ba ne. Bala'in Boko Haram dai mun gan shi: duk da tsananinsa, ya fi yawa ne a yankunan da suke karkashin tsohuwar Daular Borno. Masifar Shi'a kuwa za ta shafi kasar Hausa ne gaba dayanta ba Borno ba. Kuma za ta ba da dama ta biyu ga makiyan musulmi su lalata tattalin arzikinmu da rayukanmu da zaman lafiyarmu kamar yadda na Boko Haram ya ba su. Da Boko Haram suka kira kansu Nigerian Taliban a 2005, dariya muka rika musu. Daga baya sai kuka. Kan a jima, malamai sai buya, yan'sanda da soja sai gudu ana yar da bindiga ana canza uniform ana shigewa har karkashin gadon matan aure ana buya. Mu yi hattara.
Kuma kar a dauka Shia ba za su iya yin bore ba. In matsi ya kai matsi, tarihi ya nuna, dan'adam a kowane lokaci zai dau matakan kare kansa ko daukan fansa a kan wanda yake zaluntarsa. Balle kuma a wannan zamani da abu kalilan kawai ake bukata a haddasa barna mai yawa ko a hana wa mutane sakat. Masu wannan tunani ba su fahimci tarihi ko siyasar zamantakewar mutane ba.
Nasihata ga Shugaban Kasa da dukkan musulmi shi ne mu danne zuciyarmu mu bi doka. Wallahi ba zan iya jure sauraron zagin sahabi ba ko na minti daya saboda munin yin haka, kuma ba tarbiyyar mutanen Bilad al- Sudan ba ne wadanda aka sani da akidar Ahlul Sunna wal Jama'a wacce ta yi koyi da a girmama sahabbai matukar girmamawa kuma a kame daga sukar sabanin da ya wanzu tsakaninsu. Kuma take hakkin walwalar mutane da su yan Shia suke yi a unguwanni da garuruwa mummunan abu ne, zalunci ne; hakaza sabawa doka da raina hukuma. Ba a haka a Iran ko a Syria ko a Lebanon kamar yadda na fada a rubuce-rubucen da na yi a baya.
Amma duk da haka ina cikin masu cewa a yi hakuri a danne zuciya wajen tinkarar al'amarinsu. A bi doka don gudun afkawa cikin barna fiye da wacce suke yi kamar yi musu kisan gilla. Wannan ba abu ba ne da duk wani mutum mai ilmi, ko wayayye zai yarda da shi. Abadan.
Na yi mamakin yadda Shugaban Buhari ke nuna halin ko in kula a kan wannan matsala. An yi kisan gilla na Zariya amma ya nuna halin ko-in-kula. Ba taaziyya, ba tsawatawa. Ko-oho! Halan yana tsammani, kamar kullum, cewa Allah ba zai tambaye shi bisa zaluncin da na kasa da shi suke aikatawa ba, alhali yana da ikon hana su kuma da umarninsa suke aiki. Wannan hadari ne babba a gare shi da mu wadanda yake mulka gaba daya.
In da Shugaba Buhari zai koma baya kadan ya natsu ya yi tunani, zai fahimci cewa tunda aka yi kisan gillar Zariya a watan Disamba 2015, har yau al'amurransa kara sakwarkwacewa suke yi har zuwa inda ba a taba kaiwa ba a tarihin Nijeriya, lafiyarsa tana kara raunana, damuwarsa tana karuwa kulla yaumin, al'amarin siyasarsa yana sukurkucewa har ta kai iyalinsa ma za su koka a bayyane, magoya bayansa suna kara raguwa a kullum har ta kai ga su yan siyasa ba sa batun takararsa a 2019, fata ma ake yi wannan zangon ma ya karasa kar mu koma gidan jiya. In zai yi karatun ta-natsu, dole ya san akwai matsala.
Ina yi wa Shugaban Kasa nasiha da abinda yan koren malamansa ba za su taba fada masa ba. Wallahi. Wallahi. Wallahi. Rantsuwa nawa ke nan? Uku. To, Allah ya nanata a Al-Qur'ani cewa ba ya son azzalumai. Ya kuma ce ba za su taba yin nasara ba.
Muhammadu, ina jiye maka tsoron giyan mulki ta kwashe ka har ka kasance cikin azzalumai wandanda a karkashinsa ake kashe mata da yara da samari da magidanta don sun aikata laifukan da Allah ko tsarin mulki bai ce a kashe su a kai ba. Ka gyara in ka ga dama. In kuwa ka ki don jin karfin ofis dinka, to ka waiga baya kadan ka ga abinda ke tafe kamar yadda na fada a sama. Ka sami wakar Nasiha Ga Buhari da na rubuta ka karanta.
Mu yan Nijeriya, don Allah mu yi ta hakuri da junanmu, mu daure mu bi doka, da fadawa kowaye gaskiya, mu kasance masu yin Allah tsine da duk zaluncin da za a yi wa wani daga cikinmu. Kar mu bi masu son duniya da za su kai mu ga halaka ko da kuwa malamanmu ne, su halalta mana haram su jefa mu cikin hallaka. Mu kuma yi ta addu'a Allah ya yaye mana talauci, da jahilci da halin wauta irin wanda muke ciki.
Wannan ta'addanci da ake yi wa Shia ba daidai ba ne. A d'au matakin doka a kansu bisa laifukan da suke aikatawa, ba matakin karfi ba.
In kunne ya ji, jiki ya tsira.
13/10/2016

No comments: