Kusan dai ya tabbata cewa Shugaban Kasa, Yaya Buhari, ya kufula da ministocinsa a bukatarsu ta karin kudin haya daga miliyan hudu da doka ta kayyade zuwa miliyan ashirin. Kafafe da yawa har sun ce ma ficewa ya yi daga mitin a inda suka mika masa wannan bukatar.
Lallai ran Yaya ya baci matuka saboda na san shi a matsayin mutum mai tsananin kunya da kawaici. Cewa har ta kai ya fice ya bar ministocinsa a zaune gaskiya bacin rai ya kai matuka.
Abinda zai dami Yaya Buhari a nan shi ne yawan kudin - miliyan ashirin a kowane minista. Zai ce da ma abinda ya guda tun da fari ke nan har ya takaita yawansu zuwa 36. Ba kudi, ba kudi, ba kudi.
Na biyu kuma shi ne ta yaya zai ba su miliyan ashirin bayan doka ta kayyade miliyan hudu? So suke a kama shi da sabawa doka ko yaya?
A bangaren ministoci kuwa suna ganin - kamar yadda sauran jama'a masu sharhi suka nuna - gidan miliyan hudu a tsakiyar Abuja bai kamace su ba don dawainiyar ofishinsu da zai bukaci samun gida mai kima da za su rika karbar manyan baki a cikinsa a madadin gwamnati. Ga bukatar iyali da bakin yan siyasa daga mazabunsu. Dan gida mai daki uku da wuya ya ishesu. A nan, suna da gaskiya suma.
Wani zai ce ai ministocin suna da manyan gidaje nasu a cikin Abuja. Ayya! Ya mance cewa akwai miskinai irina a cikinsu, kamar abokina Solomon Dalong, wadanda ko puloti ba su da shi a Abuja balle gida. Suna nan sai gararamba suke yi tsakanin gidajen abokan arziki - don ko 'yanuwa babu a Abuja, suna can kauye.
To yaya za a yi? A ganina a daina duk wani soki-burutsu a dau shawara guda. Kowa ya mai da wukarsa cikin kube: Yaya ya bukaci Ministan Kudi da ya rubuta takarda ta gaggawa zuwa hukumar da ke kayyade albashi da alawus alawaus yana bukatar ta sake nazarin alawusan din ministocin don kayyade abinda zai yiwu a yau. In miliyan hudu ya isa a 2002, yau, bayan shekara 14, ya kamata a kara.
Cikin sati daya, idan zai yiwu, sai hukumar ta maido amsa ta ce ga abinda ya za a biya. Shi ke nan. A karshe, in miliyan dari hukumar ta ce, Yaya ya ba su. Ba kudin aljihunsa ba ne kuma bai karya doka ba. Bin doka shi ne a'ala.
Ra'ayina ke nan.
Dr. Aliyu U. Tilde
No comments:
Post a Comment