Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

Shugaba Buhari: Ka Kafa Hukumar Gaggawa Ta Soja Don Yaƙi da Yunwa A Sansanun Ƴan Gudun Hijira

Duniya ta shaida ka taka rawar gani inda ka daidaita sahun sojojin Nijeriya har suka samu gagarumar nasara a kan ƴan Boko Haram. Mafi yawan garuruwa da yankuna an ƴanta su. Tashin bama-bamai ya ragu matuka, hatta a cikin Maiduguri. Kwanciyar hankali ya dawo zukatan mutane suna fatar komai zai koma yadda yake nan ba da jimawa in ƙoƙarin ya ɗore.
Ana cikin wannan yabo da fatan alheri, kwatsam sai ga shi wankin hula yana nema ya kai mu dare a batun ƴan gudan hijira da ke sansanoni dabam-dabam na Arewa-maso-gabas. Rahotanni da yawa sun nuna waɗannan bayin Allah da aka ceto rayuwarsu ta shiga cikin gayar ƙunci a saboda yunwa. Sun yi duk abinda za su iya yi don neman sauki, har da faɗawa cikin mummunan fasiƙanci a sansanun inda har mata da ƴanmata suke ba da kansu don su samu abinda za su ci, amma abin ya citura. A ƙarshe, hotuna da rahotanni irin na su Ƙungiyar Kare Haƙƙin BIl’adama Ta Duniya (Amnesty International) ta tabbatar da mutane suna mutuwa saboda yunwa a waɗannan sansanoni. Duniya ta riga ta ji, tunda kafofin watsa labarai na ƙasashen waje duk sun yayata labarin a farkon satin nan.
A ce yau yunwa tana kashe bayin Allah a sansanonin gudun hijira a Nijeriya kuma a zamaninka gaskiya abin kunya ne matuƙa (scandal) kuma alama ce ta cewa jami’an Gwamnatin Tarayya da na jihohin da abin ya shafa suna cin amanar da aka basu na ciyar da waɗannan bayin Allah kamar yadda suka saba. In akwai laifinka, shi ne rashin tsawatawa ko ɗaukan matakin daƙile wannan sama da faɗi da ake yi a sansanonin.
Wannan kuma bai tsaya ga matsalar ƴan gudun hijira kaɗai ba. In ka ɗebe abinda hukumar EFCC take yi na gurfanar da manyan jami’ai da suka ci kuɗi a gwamnatin da ta shude, kusan za a ce ba wani tsari tabbatacce wanda yake yaƙi da cin hanci a ma’aikatu ko tsakanin jami’an gwamnati a matsayin tarayya da jihohi. Kowa na cin karensa ba babbaka kamar yadda ake yi a gwamnatin da ta shude.
Kar ka raba ɗaya biyu, wannnan abin shi ke haddasa mace-mace a sansanonin ƴan gudun hijira ba wani abu ba. Dama jami’an gudanarwa na hukumar agajin (NEMA) duk na tsohuwar gwamnatin da ta shude ne waɗanda da yawansu sun yi ƙaurin suna wajen cin amana. Ba ka canza su ba. Duk da jama’ar da Allah ya maka wanda bai taɓa yi wa wani ɗan Nijeriya ba, gwamnatinka ta gagara naɗa waɗanda suka fi su inganci don su maye gurbinsu.
Ba tare da ɓata maka lokaci ba, ga shawara ɗaya rak a kan yadda za a warware wannan matsalar ta rashin wadatar abinci a waɗannan sansanoni.
1. Na farko dai, cikin gaggawa, Gwamnatin Tarayya ta karɓe haƙƙin gudanar da sansanonin gaba ɗayansu kuma ta kafa wata hukumar gaggawa (Taskforce) ta soja wacce za ta lura da su, daga yanzu har lokacin da za a rufe su. A samu wani tsayayyen jami’in soja wanda kuma aka shaide shi da matuƙar riƙon amana ya shugabanci wannan hukuma.
2. Don Allah wajen zaɓen shugaba da sauran ma’aikata, a gujewa son rai na zaɓen yan’uwa ko ƴan siyasar jam’iyya mai ci. Ba abinda yake kashe tsarin gwamnati irin ɗaukan ma’aikatan gudanar da aiki bisa son rai. In direba bai iya mota ba ko yana tafka shaye-shaye, dole a yi hatsari. Ka baiwa Kwamanda Burutai umarni da ikon haɗa mutanen, ka ga ni. Amma in jami’an fadarka ne za su yi, kayya! Mutane da yawa sun tsinke da lamarinsu.
3. Ana iya samun wani kwamiti na farar hula, suma masu gaskiya, waɗanɗa za su riƙa sa ido da baka rahoto a-kai-a-kai (monitoring). Kar a barwa wata ma’aikata wannan aikin. Wallahi ba za su taɓuka abin kirki ba banda neman cin kuɗi a alawus-alawus da tafiye-tafiye na ƙarya kamar yadda suka saba. (Ba don ana azumi ba ma, da na ɓace su a nan).
4. Kar wannan hukuma ta zame ƙarƙashin wata hukumar farar hula. A’a. Ta zame ƙarƙashin hukumar soja kuma a ɗauketa a matsayin ɓangare muhimmi na yaƙi da Boko Haram. Dole ka yaƙi yunwa a nan kamar yadda ka yaƙi Boko Haram don in bindigar Boko Haram na kashi, yunwa ma kashi take. Don haka, za mu yi murna mu ga sojojinka sun wa yunwa ɗiban karen mahaukaciya kamar yadda suka yi wa Boko Haram.
5. A cire hannun gwamnatocin jahohi wajen gudanar da sansanonin. Mun gode da gudummawar da suka bayar amma su bari haka. Da yawa daga jami’an jahohi marasa imani ne na inna-naha. In kai za ka kawo masu gaskiya, su jihohi ba masu gaskiya za su kawo a jami’ansu na SEMA ba don a haɗa kai a yi aiki. To tunda har matsalar ta kai ga rasa rayuka don yunwa, dole su jihohi su haƙura, su san cewa ba a damisa biyu ga fage.
6. Na sani akwai waɗanda za su yi ca su ce maka ina Gwamnatin Tarayya za ta samu kuɗi na ciyar da ƴangudun hijirar? Waɗannan sune ƴan aƙidar kasuwa-dole, masu gaya maka cewa zamanin taimakawa talaka ya wuce. Hakane, babu kuɗin ciyar da ƴan gudun hijira amma akwai N92billion wanda za a kashe wajen ciyar da yaran firamare abinci kyauta a makarantun boko duk da cewa abinci ba ya cikin dalilan lalacewaar ingancin ilmi ba a ƙasar nan. Ni ina ga, in an yi niyya, tsakanin gwamnatinka da na jihohin da abin ya shafa, ana iya tara kuɗaɗen da ake bukata. Banda kaso na NEMA a kasafin kuɗin bana, ko sabon buƙata ta gaggawa ana iya aikawa majalisa a kan haka. Balle ma ba na jin abin zai kai ga haka.
7. Tun da fari, a saki maƙudan kuɗaɗe da za a buƙata wajen sayen abinci da magunguna da faɗaɗa sansanun kamar yadda ake ware manyan kuɗaɗe wajen sayen makamai.
Shawarata ke nan taƙaitacciya. Ya zama dole in ba da ita don na fahimci matsalar za ta ci gaba da ta’azzara muddin ba a canza tsari ba. Shi maci haramiya kullum ƙara nitsewa yake yi cikin haramiyarsa don ba ta ƙosarwa.
A ƙarshe, ina so ka lura da cewa wannan abu ne na gaggawa matuƙa. Rahotanni sun nuna a kullum akan samu masu mutuwa a waɗannan sansanun saboda yunwa. Don haka gyara shi ba abu ba ne da za a yi sanɗa a kai. Da gaggawa ana ina neman shawarar jami’an da suka kamata, da gaggawa Burutai zai iya fito da ingantattun sojojin da za su gudanar da shirin, kuma da gaggawa suna iya fara aiki nan da nan.
Amma ko za a ɗau ƴan sati uku ko wata ɗaya kafin a kafa hukumar, ya kamata a yanzu haka gwamnatinka ta sai abinci mai yawa cikin gaggawa ta kai sansanun, ta kuma tabbata ana dafa shi, kuma mutanen ciki su ci su ƙoshi har su riƙa zubarwa a bola. In ba a ga abinci a bolan sansanun ba, to ka sani ba a gama yaƙi da yunwa ba. Ball e ma akwai abinci maƙare a rumbunan Ma’aikatar Noma a kowane sahi na ƙasar nan. Me zai hana a yi amfani da shi ne kam? Su waye ake ajiyewa in ba irin wannan buƙata ba?
Hakaza, ta washe kantin kwari kaf dinsa ta kai wa ƴan gudun hijiran nan kayan sallah. Su yi sallah suna murna, kai ma kana murna, mu talakawa ƴan’uwansu muma muna murna. Tsakanin Kano da Borno awa biyar ne, kamar tsakanin Kano da Yola.
Wallahi da Umar ɗan Khattabi (R) na da rai da abinda zai yi ke nan. Shi kam ma da cikinsu zai je ya yi sallah, ya gansu suna cikin ƙoshi da annashuwa. Ina ma da za ka yi koyi da shi ka rabu da ƴan kasuwa-dole, Muhammadu na?
Amma a ce a zamaninka, ƴan Nijeriya suna mutuwa da ƴunwa a sansanun gudun hijira, abin ya saɓa hankali. Wallahi ka wuce nan. Kamar yadda ka saba tashi tsaye, to yi maza ka tashi tsaye kan wanna bala’in.
Naka,
Dr. Aliyu U. Tilde
25 June 2016

No comments: