Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

Bayani A kan Karuruwan Rubutacciyar Waka A Takaice

Tambaya:
"Doctor ina bukatar karin bayani a kan ire-iren sunayen wakoki. Na kan ji ana cewa, bahari kamil ko bahari mutaqarrab. Da sauransu. Nagode."
Amsata irin ta almajirai ita ce:
Akwai karuruwa 16 da wani malami mai suna Alfarahidi ya gano (dalibinsa Ibrahim? ne ya gano na sha shidan) a cikin wakokin Larabawa a karni na 9, ina ji. Wadannan karuruwa sai ya kira su Buhur ko Baharori (da Hausa). Kusan duk wata rubutacciyar waka a Larabci za a same ta a kan daya daga cikin baharorin nan 16.
Ma'anar kari ko bahari shi ne yadda fasalin sauti yake zuwa a kowanne baiti na rubutacciyar waka (poem). Watau, kowane kari da irin nasa sautin, ko kida, in ka so.
Ga sunayen karuruwan kamar yadda malamai ke jera su a al'adance:
1. Tawil
2. Madid
3. Basit
4. Wafir
5. Kamil
6. Hazaj
7. Rajaz
8. Ramal
9. Sari'
10. Munsarih
11. Khafif
12. Mudaari'
13. Muqtadab
14. Mujtath
15. Mutaqaarab
16. Mutadaarak
To, bincike na ya nuna min cewa malaman daular Borno, da su Shehu Danfodio da sauran malamai na bayansu sun rubuta wakokin Barbarci da Fillanci da Hausa ta hanyar aro wadancan karuruwa. In za su rubuta wakar su, sai su tsai da shawara kan wane bahari (kari) za su rubuta ta. To sai su tsara wakar daga farko har karshe a kan wannan karin.
Shi ya sa manazarta suke ganin banbanci tsakanin malamai da sauran jama'ar gari wajen rubutacciyar waka. In dai malami ya san aruli (ilmin sigar waka) sosai, to za ka ga wakarsa na kan wani bahari ne. Ta ya-ku-bayi - masu kwaikwayon su - kuwa sai ka samu kame kame ne kawai na kwaikwayo mai wahalar fedewa saboda rashin sanin ilmin aruli da karuruwansa. Sun aza haka kawai su Shehu suka zauna a gindin bishiya suka yi ta rabka waka ganin damansu. Hasali ma, sai su yi ta inkarin (opposing) amfanin bahari a rubutacciyar wakar Hausa, su ce wai haka kawai yakamata a yi ta ba tare da la'akari da karinta a larabce ba kamar yadda aka gano magabata suka yi, wai, a cewarsu za a dora wa Hausa nauyin da ba zai iya dauka ba.
To amma da yake ilmi yana fadada yanzu, na tabbata ilmin aruli zai fadada ta yadda masu son rubuta waka a Hausa ko wani cikin yarurrukanmu za su amfana da shi matuka. Don ba abinda ke bai wa waka muhimmanci da martaba wajen malamai na harsuna dabam daban da ke da alaka da larabci (kamar Farsi, Urdu, Hebrew, Swahili, dss) kamar karinta. Hatta yahudawa suna amfani da karuruwa 10 cikin 16 nan na larabawa tun daga andalus har zuwa yanzu. Don haka, Barebari, Hausawa ko Filani ba su kadai ba ne. Yana nuna kasancewarsu ne cikin wayayyun mutane tun kafin zuwan turawa wadanda ba wasu kamarsu a Nijeriya a wannan fanni na rubutacciyar waka (poetry). Wanda ya fara gano mana wannan shi ne marigayi Farfesa Kabir Galadanci a aikinsa na PhD da makalolin da ya rubuta.
Don in ba da tawa gudummawar ne ya sa na rubuta waka a kan kowane kari (bahari) cikin 16 nan don ya zame cikakken misali ga dalibin da zai so fara rubuta wakar ilmi a Hausa ko wani yaren. Sunan littafin Waka A Kan Baharinta. A ciki na ba da kafafun kowane kari yadda mai rubuta waka zai bi kowanne yake so cikin sauki.
A lura, karuruwan ba kirkiran wani ba ne, yanayin da sauti yake zuwa ne a al'adance (naturally). Shi Khalil Ibn Ahmad Alfarahidi gano su kawai ya yi bayani amma tun daruruwan shekaru ana amfani da su, kamar yadda Newton ya gano "gravity". Don haka kana da dama ka dau kowane kari kake so ka yi amfani da shi in za ka rubuta wakar ilmi.
Don haka za ka ga manyan wakoki ke da alaka da kari guda. Kamar yadda bakandamiyar Imru'ul Qais, da ta Almutanabbi, da ta Alfazazi (Ishriniya), da ta Shehu Usmanu (Ahmada) Tukur Danbinta (Bushra'u) da ta Sheikh Nyass duk karin Dawil suka yi amfani da shi. A kansa ni ma na rubuta wakar Ilmi da Nasiihaaji Fulbe. Idan kari ya zame daya, dole gabobin wakar su zame daya, hakaza sautinta. Ba wani ne ya saci wakar wani ba.
Wannan muhimmin banbanci ne tsakanin rubutacciyar waka da wakar baka (irin ta su Shata da Danmarya da Barmani Choge), wacce a cikinta kowane mawaki ke da nasa karin.
Allah ya fi kowa sani.
9 Agusta 2016.
(Bayani: akwai wasu manazarta da ke ganin karuruwan sun fi 16 amma dai kwanan nan ne nazarin ya kai haka.)

No comments: