Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

BEGEN NIJER (2nd Edition)


Dr. Aliyu U. Tilde

1. Ga Allah a kullum muke tambaya
Da daɗi hakan nan idan an wuya.
2. Idan hankali ya riga ya tsayar
Fa zucci da gangar jiki sai biya.
3. Tunani da begenta sun baibayen
Da farkon dare har zuwa safiya
4. A nan nai shiri babu mai tsai da ni
Da saurin gudu sai ka ce walƙiya.
5. Ina kai ga boda na ce sallama
Nijer na taho don biɗar zuciya.
6. Maraɗi na sauka ina tambaya
Gidansu su ce, “Ba ta nan. Ka jiya?”
7. Na bar su cikin hanzari, garzaye
Da fatar na iske ta gun rakkiya.
8. Ta ce kash Ali ka yi latti kaɗan
A Zinder ka same ta in ka iya.
9. Na ce ai da ikon Ta’ala Ƙadir
A can za ni kwan in akwai lafiya.
10. A can zan gano wagga tauraruwa
Ta zo min da tarba tana dariya.
11. Idan ta cene min “ca va?” sai na amsa
“Bien”, ka ji na ce ina lafiya.
12. Na ce na taho don buƙata huɗu
Idanu da kunne suna tambaya.
13. Fa kunne yana son ya zam ya jiya
Kalaminta daɗinsa har jijiya.
14. Ido kau yana son ganin Fatima
Da ba turɓunewa kaza ba riya.
15. Muruwwa, karimci da kumya duka
Da halin kwarai kana ga gaskiya.
16. Masauki ta kai ni da duk tanadi
Da safe ta gaisan, “Kana lafiya?”
17. Da “bonjour” suke gaisuwa a Faranshi
Da “morning” muke yi a Nijeriya.
18. Buƙata ta biu zan biɗa nan da nan
Abincin Faranshi nike tambaya.
19. A kawo “a la cart” na zaɓa na ci
Cikina da zurfi awa rijiya.
20. Ina ci da sauri ina zabga santi
Da zare idanu awa mujiya.
21. Idan na yi tam sai na ce mata: “Merci
Beaucoup”, ka ji na ce ina godiya.
22. Sa’an nan buƙata ta yawo ta zo
Gama na sani ba ta ce, “Na ƙiya”.
23. Ki kai ni wure na washe ido
A sassa na Nijer da duk rariya.
24. Ina so ki kai ni Yamai helkwata
Da Difa da Azbin wajen Gimbiya.
25. Mu dawo ta Dosso da Ƙwanni mu zo
Maraɗi ta Buzu wajen Hajiya.
26. Ta kawo ni boda tana sallama
Ido na hawaye kaza zuciya.
27. Buƙata ta ƙarshe ga mai martaba
Da nauyi da zan ba ki. Ko kya iya?
28. A tafinki zan sa shi kin gan shi nan
Ki damƙe shi kam kar ya zam ba shiya.
29. Da ƙauna da sona da duk rayuwa
Aje mini su har na bar duniya.
30. Ta ce ai ko ni ma buƙata garen
Da nauyin da zam ba ka. Ko ka iya?
31. A tafinka zan sa shi ka gan shi nan
Ka damƙe shi kam kar ya zam ba shiya.
32. Da sona da raina da duk zuciya
A je mani su har na bar duniya.
33. Ta amsa na amsa cikin tabbaci
Amana tsakaninmu ba tankiya.
34. Ta ce, “Bonne voyage”, sallama ‘yar Faranshi
Na amsa da “bye-bye” ta Birtaniya.
35. Salama ga Nijer da Nijeriya
Da dukkan masoya na Ifriƙiya.

6 February, 2017

No comments: