Waƙar Bara’a
Ta Dr. Aliyu U. Tilde
1. Muna fara waƙa da sunansa Allah
Da ba shi da ɗa Jalla balle uba.
Da ba shi da ɗa Jalla balle uba.
2. A tun fil azal shi kaɗai ba kamarsa
Hakan zai zame ba iyaka gaba.
Hakan zai zame ba iyaka gaba.
3. Da mata da farka, bazaura, budurwa
Ka ce bai da Laila, Amina, Luba.
Ka ce bai da Laila, Amina, Luba.
4. A mulki dawaman isasshe kwarai
Da ɗai bai fatauci, haram ko riba.
Da ɗai bai fatauci, haram ko riba.
5. Wadace da baiwa ga mai tambaya
Ni’immu ga bayinsa ya rarraba.
Ni’immu ga bayinsa ya rarraba.
6. Fa duk ayyuka, zantuka ya sani
Da dabba, mutum ko ruwa mai zuba.
Da dabba, mutum ko ruwa mai zuba.
7. Mutane a kullum muna zullumi
Talauci da juyi muna fargaba.
Talauci da juyi muna fargaba.
8. To shi Jalla sam ba ya tsoron gushewa
Lamurransa kullum suna cigaba.
Lamurransa kullum suna cigaba.
9. Ta ya zan biɗar wanda ba ya iyawa
Da zai mutu sannan ya zam ya ruba?
Da zai mutu sannan ya zam ya ruba?
10. Na bar wanga Sarki da zan so ya ce
A ranar tsayawa: Ali marhaba.
A ranar tsayawa: Ali marhaba.
11. Fa ya Jalla Allahu tsarshe ni bauta
Na gunki mutum ajizi mai uba.
Na gunki mutum ajizi mai uba.
12. A kullum salatinka har sallama
Ka sanya su kan Mustapha shugaba.
Ka sanya su kan Mustapha shugaba.
Bauchi
7 Agusta 2016
7 Agusta 2016
No comments:
Post a Comment