Dazu na ga wannan labarin a Whatsapp an turo min. Ban ji dadinsa ba don abin da ke ciki na zalunci na saba ganin sa a rayuwa a baya.
Ina jin Gwamnan Yobe bai san da wannan ba don da ya sani a matsayinsa na babba ba zai bari a yi zalunci ba, watakila aikin masu fushi da fushin wani ne.
Idan maganar Bulama ba gaskiya ba ce, to sai Gwamnati ta yi rubutu ta karyata don wayar wa mutane kai. Wannan kadai ya isa ya sa Bulama ya yi taka-tsantsan. Sai a yi masa nasiha a yafe masa. Haka ya fi kusa da adalci da halin dattaku.
Amma idan maganar da Bulama ya yi gaskiya ce, daci ta yi, to sai a daure a gyara, a neme shi gafara kan zaluntarsa da aka yi. In ba haka ba, abinda zai biyo bayan zalunci ba yi da kyau don mai yinsa sai ya dawo abin tausayi.
Gani ga wane ya isa wane tsoron Allah.
Dr. Aliyu U. Tilde
21 July, 2017
21 July, 2017
--------
Ga abinda aka rubuta:
Malam Bulama Lamba sannanen marubuci ne a yanar gizo a jihar Yobe wanda yanzu haka yana gidan yari dalilin alkalaminsa.
ASALIN ABINDA YA FARU.
Cikin shekarar nan ne aka ba wa gomann Yobe Ibrahim Gaidam lambar girma na cewa ya fi kowa ne gomna a fadin kasar nan kula da tsoffin ma'aikata ta hanyar ba su kudin sallamarsu akan lokaci da kuma fara biyan su kudin fansho ba tare da an dau lokaci ba, wanda mai magana da yawun gomna ya rubuta a shafinsa na fazebuk, inda a shi ma Malam Bulama Lamba ya yi na shi rubutun na musamman kan cewa wannan zance ba haka take ba domin akwai mutane da yawa da suke bin gomnatin jihar Yobe kudin sallamarsu, in da ya ba da misali da wani dan uwansa da ya rasu yau shekara Hudu da wata goma suna bibiyan kudin sallamarsa don a ba wa marayu amma shiru ka ke ji, ya kara da cewa tun da dai an ya ba wa gomna ta wannan fannin to duk wanda ya ke bin gomnati kudin sallama to ya garzaya sati mai zuwa ya karbi kudin sa.
Fitan wannan rubutu kenan Sai Hukumar sss ta gayyaci Malam Bulama Lamba don ya amsa tambayoyi kan rubutunsa bayan ya amsa Sai suka ce masa ya rubuta wa gomnati sakon ba da hakuri, bayan haka ne Sai kuma Hukumar ta tura shi kotun majistri da nufin gomnati ta sa shi karar yi mata kazafi, wanda hakan bayan ya amsa wa kotu cewa shi bai da laifi, bayan an tashi daga kotu Sai Hukumar sss suka tura shi gidan yari da ke garin Potiskum wai don su ajiye shi kafin a cigaba da sauraron kara, bayan haka ne bisa kokarin da Dansa Ibrahim Bulama Lamba Potiskum ya yi ta yi ganin cewa mahaifinsa bai da isasshen lafiya sannan kuma cikin azumi ne har Allah ya sa kotu ta ba da belinsa da nufin za a cigaba da sauraron kara.
Tun da aka ba da belinsa duk ran da za a je zaman kotu bangaren gomnati ba sa zuwa sauraron shari'ar bayan an ta fi hutun sallah an dawo satin da aka koma kotu Sai bangaren gomnati suka ce sun janye kara daga majistri ashe wata kullalliya aka shirya wa Malam Bulama Lamba domin ya fito da zimmar shiga mota sai kuma ga wata sammaci a babban kotun tarayya da ke garin Damaturu, da ya je aka karanta masa laifinsa by a musanta Sai kotu ta ce za ta, ta fi hutun shekara na wata uku saboda haka Sai ta dawo hutu za a cigaba da shari'a Sai lauyan Malam Bulama ya nemi kotu ta ba da belinsa sai kotu ta ce ya je ya rubuto, bayan ya fita don ya rubuto neman belin ya dawo ya samo Alkali ya tashi, shi kuma Malam Bulama sun turo shi gidan yarin Potiskum da nufin ya zauna har Sai Watan Satumba idan kotu ta dawo daga hutu.

Malam Bulama kamar kowane dan Adam ne ya na da iyalai, ga ba shi da isasshen lafiya domin yana fama da ciwon sugar
Do justice to Bulama Lamba
Sign concerned Yobe social media Youth.
No comments:
Post a Comment