Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

Fadada Filin Jirgin Abuja da Gyara na Kaduna Ya Yi Kyau

Dazu da safe na ji rahoton BBC Hausa a kan shirin da gwamnatin tarayya take yi na fadada filin saukan jirage na Abuja da kuma karkata duk jiragen fasinja da za su sauka a Abuja zuwa Kaduna a yayin da ake gyaran filin Abuja din.
Mu Zagezagi musamman, wannan labari ya mana dadi saboda za a jefi tsuntsaye biyu da dutse daya kenan. Banda fadada na Abuja, na Kaduna shi ma zai samu kwaskwarima da ingantawa (upgrading) da ya dace da zamani. A bar ta zancen cewa garin Kaduna zai samu habakar tatttalin arziki a lokacin da jiragen Abuja suke sauka a Kaduna.
Ba wai, wannan zai kawo wahalhalu ga mutane masu-hannu-da-shuni da suke amfani da jirgin sama. Sai a yi hakuri. Wallahi muma talakawa haka muke fama da hanyoyin mota duk lokacin da za a gyara hanya. Mun wahala lokacin da Shekarau da Kwankwaso suke fadada hanyoyin kano, amma yanzu sai zuuuuuuuu kawai muke da mota in mun shiga birni.
Mu kam ma wahalar murna ce don da wuya ka ga ana kula hanyar mota. Ka duba azabar da muke sha a kan hanyar Jos zuwa Saminaka, da hanyar Rahama zuwa Saminaka, da hanyar Gombe zuwa Yola, ai abin ba a cewa komai. Balle su masu jirgin sama da mota ce jeep za ta dauke su suna shan raba har Abuja.
Akwai bata lokaci kam. Da sun saba daga Legas zuwa Abuja awa daya kawai za su yi. Yanzu kam sai sun kara wasu awa uku saboda kafin su fita daga Kaduna ma sai sun dau awa guda. Kuma ga rashin kyawun hanyar Abuja, dadin-dadawa, duk da gwamnati ta ce za ta gaggauta gyarawa. Amma tunda don gyara ne wahalar, sai ogo-ginmu su daure, oga. A lokacin mai tsawo, duk ministoci za su yi tafiya a mota na lokaci mai tsawo su ji yadda hanyoyin suke su ma. Mu gan su su gan mu.
Wannan ya sa in yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara fitar da wata bye-pass daga Airport zuwa mararrabar Abuja don sauwake bukatar matafiya ko da irin wannan ko wani abu zai tilasta karkata jirage daga Abuja zuwa Kaduna. Ana iya ba da kwangilar yanzu, alabashin a yi ta yi har a kare nan da shekara biyar ko shida. Kan da an yi irin wannan hanya tuntuni a yanzu ba wata wahalar da za a sha.
A karshe, ina kira da babbar murya cewa ya kamata a waiwayi gyara babbar hanyar Kaduna zuwa Kano da kuma Kaduna zuwa Jos tunda yanzu in zan je Legas a jirgi, dole Kaduna zan je, kuma an tilasta min bin hanyar Saminakan nan maras kyau; haka kuma Bakano shi ma, in zai je Kano daga Abuja ko Abuja daga Kano, ba ruwansa da jirgin sama, dole hanyar Kaduna zai bi har a gama fadada filin jirgin saman Abuja. Hanyar Kano din nan musamman daga Zaria kafin mutum ya kai Kwanan Dangorata baci sosai.
Ina ma da lokacin PTF ne? Jama'a su ga aiki da cikawa? Ga nama na jan kare.
Yanzu wani Bakano, Yasir Ramadan Gwale ya ce in jona Kanawa su ma cikin koken nawa don a karasa gyara musu filin jirgin saman Kano. To, Baba Buhari sai ka taimaka musu don su ma su dan more. Amma ai ni na fi son ka bar su su dinga zuwa Zazzau in sun matsu ko ma ci kudinsu kadan.
Aliyu
9/1/2017

No comments: