Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

'Wakokin Aruli' Ya Shiga Kasuwa

Littafina, Wakokin Aruli, ya shiga kasuwa tun wata guda da ya wuce. Ina sa ran littafin zai yi amfani wa dalibai da malaman rubutattun wakokin Hausa. Hakaza, sha'irai za su amfana da samfuran wakokin da na rubuta a ciki a kan kowane Bahari.
Zuwan da n yi Kano ya ba ni damar kai littafin zuwa manyan malaman rubutattun wakokin Hausa a Jami'ar Bayero wadanda suka yi murna da shi. Hakaza na turawa wasu malaman a Jami'ar Sokoto da ta Maiduguri.
Kudin littafin N650.00 kacal.
Ana iya samun littafin a wadannan wurare:
Jos - Darul Thaqafa, Bauchi Rd, Jos
Bauchi - Gidan-Man MRS Supermarket, Gidan Mai
Gombe - Samaha Supermarket, Kusa da General Hospital
Yola - San-Hussein Supermarket, kusa da Kasuwar Jimeta
Maiduguri - M-Deen Supermarket, UNIMAID
Azare - Ibrahim Dahiru, COE Azare
Kano - Jifatu Stores, Zaria Rd da BUK Bookshop
Zaria - Hamisu Bookshop, Tudun Wada Market
Kaduna - Arewa House
Sokoto - Prof. Haruna Abdullahi Biriniwa
Ina matukar godiya ga duk manyan mamalam aruli da suka taimaka wajen duba wakokin. Hakaza, ina godiya ga abokaina na kafofin sada zumunci na Facebook da Whatsapp wadanda suka rika bibiyar wakokin lokacin da nake rubuta su har ma wasu suka ba da shawar rubuta 4 daga cikin 24 da aka buga.
A karshe, ina fatar za a yafe kura-kuran da ke cikin littafin. Kar a mance cewa dalibi ne a cikin Sha'irai ya rubuta shi, ba malami ba. Kamar kowanne littafi, kura-kuran ciki za a yi kokarin gyara su a bugu na gaba.
A sha karatu lafiya.
Dr. Aliyu U. Tilde
14/1/17

No comments: