Total Pageviews

Wednesday, January 17, 2018

Mayaudariya!

1. Sarkin da babu guda tamkarshi har abada
Waye ya shi a kama? Wallahi babu shiya.
2. Mulki ko duk mu sani, ƙarshensa zai ruguje
Sai nasa za ya rage; yau, gobe, tun a jiya.
3. Dunya muke ta biɗa, himma da fafutuka
Kullum gudunmu take, mu ko muna mabiya.
4. Sannan idan muka ƙi, don mun jiyo wa’azi
Zauwa take da ladab tamkar Babarbariya.
5. Balle idan muka ce: kaitonki! Sai ta taho
Ƙaunarta za ta raya, tamkar Basakkwaciya.
6. Mun kau da kai ta zaƙe, kaidinta ba shi da kyau
Murya, diri da ado, kaa ce Balarabiya.
7. Ga munduwai a hannu, gwallai su tim wuya
Ƙurɗi cike a jaka, yaro ka ce: Hajiya!
8. In ta ga ba mu kusa, nan za ta zo ta matsa
Ƙofar gida da kira: Malam nake cigiya.
9. In ta ji an yi shiru, can sai ta kama batu
Cewa takai: Mu zuba, zan bi shi ko Libiya.
10. In ya tsaya na tsaya, in ya gusa na cira
Sauri gare ni ƙwarai, har na wuce kibiya.
11. Burinsa in na sani, cabke shi ba wahala
Tarkon da za ni haɗa, kama shi babu wuya.
12. Shi saurayi ya sani, tarkonsa ne shagala
Ƙwallo da Instagiram, Fesbuk, sako haɗiya.
13. Ƙwaya da fim hakanan, miusik, yawan magana
Hoto na batsa haka, in babu togaciya.
14. In yai gida na haɗo tarkon zina na naɗa
In baibaye shi da shi, in sa a sarƙaƙiya
15. Ɗankasuwa kuwa ai, haajarsa gata a nan:
Mudunsa za ya rage, kullum yana ta saya.
16. In malami ya zame, burinsa ne a cene:
Sam ba ya shi a sani, ga da hassada da riya.
17. Mulki na masu ƙasa, ƙatti da son haɗama
Haƙƙi da zali su ci, ba wanda za su biya.
18. Mata ko yan bidi’a, kishi ya kai halaka
Tsafi da makru sunai, kullum suna aniya.
19. Dunya tana ta kiɗa, mu ko muna ta rawa
In ta ɗaga duniya, ƙarshenta tai ajiya.
20. Sarkinmu ba mu fita, in ba kana kusa ba
Tsarshemu bin ta a yau, dunya mayaudariya!
21. Allahu mun gajiya, tserad da mu da wuri
In mun taho da biɗa, sanya ta kan shiriya.
22. Aikinmu bai da yawa, himmarmu ta yi kaɗan
Ga shekaru da yawa, mun zo cikin karaya.
23. Ƙarfinmu ya yi kaɗan, mun sunkuya, gajiye
Nauyin da za ka aza, sa wanda za mu iya.
24. Duk gaskiya mu tsare, yardarka mui ta biɗa
Ɗora mu kan shiriya, hanya matabbaciya.
25. Kalma ta ratsa jiki, kullum cikin zikiri
Sallah, siyamu, zakat, hajjinmu ba gajiya.
26. Tara mu gun Namadi, haadinmu ran tsayuwa
Dukkan uwa da uba, mu naka, sa da diya.
27. Ƙarshenmu sa shi da kyau, aikinmu gam-da-katar
Kalma ta zo da wuri, zancenmu gun tafiya.
28. Tsira kaza salama, sanya su kan Nayabo
Alih, sahaba, daɗo manya irin safiya.
29. Gaffaru nai roƙo, bawanka ya halaka
Laifi dubu miliyan, yafe wa Dan-Rakiya.
30. Sanya cikin ƙabari, sunanka za ya kira
Man rabbukum? Amsa: Allahu rabbu daya!
Dr. Aliyu U. Tilde
3 September, 2017

No comments: