Dr. Aliyu U. Tilde
Da yake mulki na cikin siffofin ubangiji da kuma ni'imar da yake ba wa bawansa da ya ga dama, kowa Allah ya ara wa rigar mulki, ba shakka sai ya yi taka-tsantsan. In ba haka ba hallaka ce miraran za ta same shi.
A bar batun gaggan shugabanni irin su Fir'auna, a'a, hatta namu kananan alhaki na karshen zamani da suke sude kwaryar mulkin, in mutum ya duba irin kasassabar da suke tafkawa na girman kai, da jiji-da-kai, da handamar dukiyar al'umma kamar za su dauwama a duniya, da fadin maganganu na fitan hankali idan kujerar mulki ta kai musu karo, musamman maganganu wadanda Allah ne kadai ya cancanci yin su, malam sai ka san cewa mulki hadari ne babba kuma abin guje mawa. Jahili ne kawai zai rika zumudin neman sa.
Na san wani gwamna da a lokacinsa har "kun fa yakun" wani malamin fada yake siffanta shi da shi wai don in ya ga dama yau dinnan sai ya mai da kai chiyaman na lokal gommen ko maloniya. Kuma a taron mutane ake wannan kirarin. Wasu malaman lamarinsu idan sun ga Naira fa sai a sulow.
Gwamna dai a kwana a tashi, mulki ya kare, duniya ta sau shi, ya zama bera abin farautar yara har ta kai yana tunanin kashe kansa saboda halin takurawa da ya samu kansa a ciki. Dukiyar da ya yi ta handamewa bata amfane shi da komi ba. Allahu Akbar. To shi wannan ma dama-dama ke nan. don satar da ya yi bata da yawa.
Eh bata da yawa don wanda ya karbe shi a mulkin tasa giyar ta hada har da ta'addanci, da lalata tsarin aiki, da kashe abokan hamayya da sata ta fitar hankali da ta ninka ta magabacinsa sau ashirin ko fiye. Shi ma ya gama nasa waadin , duniya ta yi mar halinta.
To, girman kai da fasadi - walau na satar dukiya ko na lalata dabi'ar mutane - sune nau'o'in zalunci biyu da masu mulki suke fama da su. Wadannnan biyun halayen wadanda suka tabe ne gobe kiyama. Tushensu kuma, akasari jahilci ne. Yana da wuya jahili shugaba ya barranta da su.
Wani sai ka ga ba mai fasadi ba ne amma sai ya kasance mai girman kai a mulki; wani sai ka ga fasadi ne damuwarsa, amma mai saukin kai; wani kuma a jarrabe shi da duka biyu. Amma wanda yake da rabo a lahira ba za ka same shi da ko daya ba.
تلك الدار الآخرة نجعلها للذين لا يريدون علوا في الارض ولا فسادا والعاقبة للمتقين.
To ba masu mulki ba kadai, mu ma talakawa Allah ya rabya mu da wadannan munanan halayen. Sai mu yi ta addu'a, muna istigfari don ya yafe mana kurakuranmu da zunubbai gaba daya. Su kuma wadanda aka jarraba da mulki, su iyanma bakunansu, da hannayensu da zukatansu.
Amma wasu maganganun da ke fita daga bakin wasu shugabannin ba su da dadin ji ko kadan. Mulki da jahilci, tabbas hadari ne babba.
18 Satumba, 2017
No comments:
Post a Comment